Chapter 8
Chapter 8
baki, a kan kujera aka dire shi idanunsa a rintse. "Kai dalla can banza ka damu mutane da ihu kana kan kujera a zau ne, ashe ma ba komai kawai dan ka tashi hankalin mu ne, yanzu da Mommy tana nan sai ta wanka maka mari" Fadila ta faɗa tana ƙarasowa bakin gadon tana za ma.. A hankali ya buɗe idanun shi, yana gama buɗewa yaga komai tsam-tsam, tsananin al'ajabi da tsoro ya sa Sudas sakin baki yana kallon su Fadila. Auta ta iso ta hau kan gadon ta ɗauki Teddynta ta rungume tana cewa" Yaya Sudas me ya sa baka kai mini Teddy na ba da ka zo? Ihun ka naji sai na tuna Teddyna a gurinka na ce bari na zo na amsa, ina nufo ƙofar na haɗu da su Daddy lafiya kake ihu a cikin daren nan?" Dariya Sauban ya yi ya ce" Amma kai dai Sudas mugun ɗan iska ne duk ka ishi mutane, yanzu saboda Allah me aka maka kake wannan ihun?" Shi dai Sudas kasa magana ya yi ɗago kai ya yi yana kallon Auta da ta rungume Teddynta tana shafa kanta, gani ya yi Teddy ta juyo kanta tana aiko masa da harara idanunta sun kara za ma manya-manya. "Waiyo! Daddy Wallahi wannan Teddyn ta Auta fatalwa ce ita ce take tsoratani tun ɗazu" Ya faɗa yana faɗowa daga kan kujera.. Dariya suka sa har Daddy , Auta kuwa kuka tasa tana ƙara rungume Teddynta ta ce" Wallahi ni dai babyna ba fatalwa ba ce, haka kawai kaje ka kalli horror film ɗin ka ko kasha giyarka ka ce wai Teddyna faltawa ce akan me?" Ta faɗa tana murguda baki.." Kowa ya tashi zai bar ɗakin Sudas ya yi saurin binsu ya ce ba fa zai kwana a ɗakin shi ba , haka dai suka tafi ɗakin Sauban yana manne da shi kamar wani baby.. Yau ta kasance Saturday babu makaranta hakan ya sa Auta ta shirya ta shiga ɗakin Daddy ta same shi yana waya, za ma ta yi tana jiran ya gama ,sai da ya gama kana ya dawo gareta fuskar shi dauke da murmushi ya ce" Auta ya dai?" Murmishi ta masa kana ta ce" Daddy ina so zanje gidan su Ƙawata Amra, to bani da kuɗin da zan saya ɗan wani abun na kai mata so nake ka bani dubu goma dan bana so wata ta fini a cikin ƙawayena, inaso nafi kowacce yarinyar a cikin ƙawayenmu" Ta faɗa tana wani cin magani ba alamar wasa." Wani ƙayataccen murmishi Daddy ya yi najin daɗin kalaman Auta, hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce" Da kyau Auta haka nakeso naga kin kere duk wata yarinya a cikin ƙawayenki, yanzu dubun goma ta isa ki saya mata abin da za ki kai mata?" Dariyar jin daɗi ta yi a ranta tana cewa" Yes Daddy plain ɗina ya tafi yadda nakeso." Miƙewa ta yi tsaye ta ce" E ka bani ya isa inaso zan je direba ya kaini ba zan daɗe sosai ba, yawwa Daddy Mommy ta ce gobe za ta zo ko?" "Kwarai ma kuwa yanzu ma muke waya da ita gobe za ta iso.. "Kuma Daddy gobe birthday Anty Fadila ni dai ba zan je ko ina ba in ba a hol za ta yi, haba ina dalili mutum sai son kaɗe kaɗe kamar shedani" Ta faɗa tana cuno baki gaba.." Murmishi kawai Daddy ya yi ya ciro kuɗin ya bata, godiya ta masa kana ta wuce zuwa palo. A hanya suka ci karo da Fadila tasha adon riga da wando jins sun matseta sosai, rigar hannunta ɗaya bakin kafaɗa ne ɗaya kuma dogon hannu ne har gwiwar hannunta.. Riƙe baki Auta ta yi ta ce" Wai wannan ɗiyar Musulmai ce kuma Musulma? An ji kunya dai Wallahi Allah ya sa wani ya miki dukan tsiya a samarin naki, kuma gobe Mommy za ta zo na huta da zalincin ki muguwa." Mutumelesy! Ni kike zagi? " Fadila ta faɗa a fusace ta miƙa hannu za ta ɗamko Auta. Ke! Da sauri ta juyo suka yi ido hudu da Sauban da yake ƙasa yana kallonsu, Auta na ganin haka ta soma ƙoƙarin sauka Fadila ta biyota suka sauko ƙasa tare.. Da gudu ta iso gurin Sauban ta ɓoye a bayan shi tana cewa" Yaya gata nan karka bari ta dakeni babu abin da da na mata fa." Fadila na huci ta nemi kamo hannun Auta, da sauri Sauban ya daka mata tsawa taja da baya tana zagin Auta, ita kuwa Auta na mata gwalo tana mata dariya, hakan ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba fuuu ta wuce sama da gudu tana cewa za su haɗu an jima... "Na gode Yaya" Cewar Auta tana barin shi ta nufo ledar dake kan kujera ta ɗauka ta wuce zuwa waje, shi ko da idanu ya rakata har ta fita ya saka eapis ɗinsa yaci gaba da jin waƙar shi yana gyaɗa kai ya zau na akan kujera... Auta na fita Direba ya buɗe mota ta shiga suka bar gidan.. A inda suka saba haɗuwa Direba ya sauketa, kallon shi ta yi ta ce" Direba ka tafi idan Yamma ta yi ka dawo nan ka ɗaukeni." Cike da girmamawa ya ce" To Madam amma yanzu ita Ƙawar taki ina gidansu yake?" Ɗan murmishi ta yi sannan ta ce" Gidansu na can bayan dutsen can sai an jima ka tafi." To ya ce sannan ya shiga motar yabar wajan.. "Ƙawata sannu da zuwa. Juyowa Auta ta yi da sauri suka yi ido hudu da Amra dake tsaye a baya, sanye take da wata doguwar riga ta yage daga gefe, kanta ta wani ɗan kwalli irin mai sulɓin nan shi ma duk ya yi dauɗa. Turo baki Auta ta yi ta saki kayan hannunta tare da buɗe hannayenta tana kallon Amra dake mata murmushi, ganin haka ya sa Amra ta iso gareta suka rungume juna cikin farin ciki. "Amra na yi kewarki sosai ya jikin Inna? Ɗagowa ta yi daga jikinta ta ce" Lafiya lau ni ma na yi kewarki Inna tana nan lafiya zo muje." Binta ta yi suka jera suna ta hira cikin nishaɗi, suna zuwa saitin wata bishiya Auta ta tsaya ta ce" Inuwar nan akwai daɗi." Murmishi Amra ta yi ɗago kan da za ta yi,ta yi arba da wani ƙaton Zaki a samar bishiyar, waro idanu Amra ta yi cikin ƙaraji ta ce" Auta maza ki dawo bayana! Ta faɗa da ƙarfi hakan ya sa Auta sakin kayan hannunta ta kwasa a guje ta dawo bayan Amra jikinta na rawa, sai da ta ɗaga kanta sama taga abin da Amra ta gani ai ko ta ɗauke salati tare da sakin kuka ta ce" Amra mu gudu don Allah kar Zakin nan ya sauko ƙasa, waiyo Allah! Yanzu ya za mu yi Amra? Ta faɗa a firgice.. Amra dake tsaye bata ko motsa ba ta rufe idanunta.. Dirowa zakin ya yi a gabansu yana wage baki, tuni Auta ta yi baya luuu ta zube a ƙasa sumammiya.. Cikin tsananin ɓacin rai Amra ta ce" Ka tafi na ce! Mai ya kawo ka nan? Za ka tafi ko saina canja maka halitta yanzun nan? Ta ƙarashe maganar tana buɗe idanunta wanda ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31