Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [24/11, 21:24] Maman Nusaiba: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum(Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ Daga marubuciyar: Amir da Amira. Aljanar Jarumai. Hafsat. Ƙaddara ce. Tani da Manu. Rayuwar ma'aurata. Sumayya baiwar Allah. Abba ne. And new book. Aljanar gidanmu. Ya Ubangiji yadda ka bani damar ɗaura Alƙalamina ka kuma bani dama da ikon sarrafa tunanina da baiwar da ka mini, ina addu'a ka bani ikon ɗauke shi lafiya, ya rabbi ka bani ikon rubuta abin da zai amfani Al'ummar Annabi Muhammad (S.a.w) Habibi ɗan gatan Allah shugaban duniya da ƙiyama. Allah ka ƙara mana lafiya da wadatar zuci ka hanemu ga aikata saɓo.... *WhatsApp number +966599791573* *بسم الله الرحمن الرحيم* 0️⃣1️⃣ Tsaye take a gefen babban titi tana rusar kuka, gefenta wata tsohuwa ce kwance tana rawar sanyi bakinta na haɗewa da labbanta saboda yadda jikin nata yake rawa sosai. Juyowa yarinyar ta yi za ta yi magana sai ta fasa ta mayar da hankalinta ga wata mota da take mata oda, tsayuwa ta yi tana Ƙifƙifta idanu tana jiran taga wanda zai fito daga motar... Babbar motar ce fara sol ta yi parking a gaf da ita, direban dake a set ɗinta ya buɗe murfin motar ya fito fuskar shi na nuna fushi, yana zuwa bai tsaya yin komai ba ya kife yarinyar da mari ya kuma ƙara mata wani a ɗayan kuncin.. "Ke uban wa ya ce ki zo kan hanya ki tsaya? Dan uwarki ana magana kin wani tsare da manyan idanunki kamar wata maiya, to ki shiga hankalinki so kike ki ɓata mini suna a gari na ƙare rayuwata a gidan yari ko me?" Shuru yarinyar ta yi ta zuba masa idanunta wanda ya ciko tam da kwalla, sosai taji zafin marin da ya mata hakan ya sa hawayen idanunta suka shiga zubowa jikinta nawa, da sauri ta sunkuyar da kanta tana goge kwallar data zubo mata tare da lumshe idanun nata, sai da ta jima kafin ta ɗago kai za ta yi magana taga ana ƙoƙarin buɗe motar daga set ɗin baya ta yi shuru tana kallon ƙofar.. Wani babban mutum ne ya fito tare da wata ƴar yarinya mai kimanin shekaru 13 tana riƙe da ƴar Teddynta, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da taga an mara ta yi saurin sakin hannun mahafinta ta isa gurin yarinyar ta tsaya, a sanyaye takai hannu ta shafa gefen fuskarta da shatin yatsun direbansu yake kwanta tar.. "Ki yi haƙuri zan rama miki marin da ya miki kinji." Yarinyar ta faɗa ta ƙara da cewa" Ya sunanki?" Ajiyar zuciya yarinyar ta sauke ta buɗe idanunta akanta sannan ta ce" Na gode sunana Amra." Murmushi Yarinyar ta yi ta kamo hannun Amra da yake ɓace da taɓo ga dauɗa data kwanta amma bata ji kyamarta ba ta riƙe hannun nata tana shafawa ta ce" Sunanki mai daɗi ni kuma sunana Afra amma ana ce mini Auta dan ni ce Auta a gidanmu, kuma z.. Bata ƙarasa maganar da take son yi ba mahaifin nata ya iso gurin tare da fisge hannun Auta daga na Amra ya ce" Auta me ya sa bakya ji ne? Yanzu wannan ƙazamar yarinyar kike taɓawa ko ba ki ga yadda take da datti ba? Kalle ta fa sai wari take." Amra ta kawar da kanta gefe ta durƙusa a gaban shi ta ce" Ranka ya daɗe ka taimaka mana kaga Mamata can a kwance bata da lafiya bamu da gurin kwana ko abinci da ƙyar muke samu muci, ka taimaka mana na kaita Asibiti" Ta faɗa tana riƙe ƙafafunsa." Cikin azama ya buge ta ta yi baya ta faɗi. "Ƴar matsiyata ni za ki taɓawa jiki ɗan uwarki kinga na miki kama da matsiyatan mutane irin ki? To ba zan taimaka ba ɗin ko an faɗa miki kuɗin a banza nake samun su da zan ke yiwa kowa hidima kamar ban san ciwon kaina ba? Ke kuma ki fice mu tafi gida" Ya faɗa yana damƙar hannun Auta da ta yi tsaye baki buɗe tana kallon Mahaifin nata.." "Waiyo Allah! Daddy don girman Allah ka taimaka mata kalli fa yadda Mamanta ke rawar sanyi, haba Daddy me ya sa ba za ka taimaka mata ba kuma har kake dukanta? Ni dai ka barni na tashe ta sai mu tafi" Auta ta faɗa tana mintsinin hannun Daddy da yake ƙoƙarin janyeta daga gurin.. "Ke ba ki da hankali za ki taɓa jikinta? Wannan fa tsami take ki rabu da ita mu tafi gida" Cewar Daddy yana ƙoƙarin janta.. Fir Auta ta kafe ta ce ba fa inda za taje sai ta tashi Amra dake ƙasa a yashe, haushi ne ya kama

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});