Chapter 17
Chapter 17
abincin kici ko." Da sauri ta sauka daga jikin Mommy ta sauko ƙasa, ganin abin da ke gabanta ta ɓata fuska kamar za ta yi kuka ta ce" Wannan dan yakushen abincin kamar wata almajira ni dai gaskiya ki kawo mini goman wannan indai har ba rowa za ki mini ba yau" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki gaba tare da aikawa Sudas harara da ya shigo yana fito tafiyar ma yana yi yana rawa har ya iso gurinsu.." Shuru Kande ta yi ita kanta wannan cin abincin na Auta yana bata mamaki, ji ta yi tasa kuka tana faɗin aje ayo mata wani, juyowa Kande ta yi za ta mata magana taga ba komai a kwanon ta cinye tass ta miƙe ƙafa tana kukan a ƙaro mata, da sauri Kande ta ɗauke kwanon ta wuce kitchen.. "Allahuna ajurni fi musibati wa'akalifili khairan minha! Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyun azim! Ubangiji ka bawa yarinyar nan lafiya wannan wacce irin masifa ce haka muke cikinta? Cewar Mommy tana kallon Auta da take kuka bil hakƙi.. Sudas ya dubi Mommy ya ce" Mommy ki dena damuwa za ta dena yanzu dai kuje Asibitin a lafiyart a gani, kinga daga nan sai asan abin yi." "Ba dole na damu ba Sudas yarinya gaba ɗaya ta canja komai nata ya canja Kamar ba Afra ta ba da na sani a baya.. Kande ta soye mata kwai guda 12 ta ɗauko wani bred ɗin da shayin ta kawo mata, da sauri ta amsa ta shiga ci tana jinjina kai , kafin minti ɗaya tuni ta cinye ta miƙe tana gyatsa ta nufi banɗakin palon ta wanke hannunta kana ta fito, kallon Mommy ta yi ta ce" Mommy muje asibitin kinga har yanzu cikin nawa bai dena ciwo ba muje a dubani" Ta ƙarashe maganar tana kamo hannun Mommy dake zau ne ta saki ba ki tana kallon ikon Allah." Ba shiri Mommy ta miƙe suka bar gidan. Daret wajan Malam ta nufa da ita, tun a hanya ta yi bacci hakan ya yiwa Mommy daɗi ta yi saurin ƙarasawa gidan Malam. Sai da isa kana ta tasheta , da ƙyar ta tashi tana miƙa suka nufi ciki, sake da baki Auta ke kallon gidan har suka isa inda Malam yake zau ne a wata ruwa. Barka da zuwa ya musu kana suka shiga ita dai Auta na bin Mommy da kallo, za ma suka yi suka gaisa kana Mommy ta ce" Malam gata nan na kawo ta." Kallon Auta Malam ya yi yana nazartata da kyau, addu'a ya yi a ciki ruwa ya miƙawa Auta ya ce tasha, kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta amsa tana yatsina fuska ta sha kaɗan ta aje gefe tana hura hanci.. Karatu Malam ya soma yi yana yi yana mata tofi, yafi minti 20 yana karatu amma shuru ko gizo Auta bata yi ba sai ma wasa zoben hannunta take yi, abin ya bawa Malam mamaki ya tsayar da karatun ya dubi Mommy ya ce" Gaskiya Azima babu komai a jikin yarinyar nan, in ma tana da su to ƙila sai an ɓata mata rai ne suke zuwa, yanzu dai ba komai a jikinta inda akwai da tuni sun yi magana a Karatun da na yi yanzu, abin yi kawai zan ke mata rubutun addu'o'in kariya daga shedanun aljannu da duk wani abin cutarwa sai take sha tana shafe jikinta da shi.." Jinjina Mommy ta yi ranta jiki a sanyaye ta masa sallama suka dawo gida. Mommy na zuwa ta shirya ta fito dan tana da meeting a office ɗin su, a palo ta samu Daddy Fadila na gefe tana bashi labarin abin da ya faru jiya har suka kasa gabatar da shagalin birthday ta, shi kuwa Daddy yana gefe yana mamaki har Mommy ta zau na tare da gaishe sa. Ɗago kai ya yi ya dubi Mommy ya ce" Ina Auta take ne? Yanzu Fadila ke faɗa mini abin da ya faru jiya." "Hmm meye bai faru ba Daddyn su yanzu haka wajan Malam na kaita ya mata addu'a ya kuma ce zaike mata tana sha tana shafawa a jiki mu gani ko za a dace ta dena abubuwan nan.. Daddy ya ce" Ni ma zan sa a haɗa mata magani sai mu gani, yanzu ke Fadila an jima birthday ne ko an fasa wannan shekarar?" "Tab! Haba Daddy ai ba abin da zai hanani yin birthday na, ka dena faɗin haka kar ma Mommy ta samu damar hanani yin abin da nake so gashi na tattaro ƙawayena da friend na makaranta wanda muka yi Jami'a da su kuma kowa ya ce zai zo, kaga kenan ai ba zan fasa dan kar ajina ya zube a gurin su, in kuma kana so a rainani to sai ka yi ta faɗa Mommy tasa mini ido" Ta ƙarashe maganar tana haɗe rai. Murmishi kawai Mommy ta yi ita yanzu lamarin Fadila ya dena damunta saboda ubanta ke ɗaure mata gindi ta yi duk abin da takeso ba mai hanata, Daddy ya kamo hannunta ya ce" Ai dole ma ki yi na tura miki 500k ki samu ki yi komai na kece reni zanje gidan Yaya daga can zan wuce wani taro da ya taso kuma nine babban baƙo a gurin." Murmishi ta yi tare ta yi masa kiss a goshi ta ce" Love you so much my darling Daddyna ,ina ƙaunarka fiye da kowa a rayuwata a gidan nan kai kaɗai kake sona Wallahi dan haka duk abin da kakeso nima zan yi maka Daddyna bari naje zan yi waya da Mufy ta iso" Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ɗakinta dukkan wani illahirin jikinta ana ganin komai hatta da pant din jikinta da bra duk ana ganinsu a bayyane, girgiza kai Mommy ta yi ta miƙe da sauri ta ce" Bye sweetheart idan Kande ta iso ka ce mata ta kula mini da Auta yanzu za ta tafi school da ta dawo ta kirani zan mata bayanin abin da za ta dafa mata." Tsaki Daddy yaja ya ce" Ke dai Wallahi Azima har yau kin kasa wayewa, kalleki za ki je babban meeting na manyan mutane ki ɗauki wani zunbulelan hijab ki zunbula kamar wata matar Liman ko Ustaz, kullum ke kanki a dubu yake ki yi ta yawo da hijabi ke wai bakya jin zafi ne? Ko ba ki ga yadda abokan aikin ki suke yi ba wayayyu masu aji da class ba irin ke ba mai kai a duhu, duniya ta canja zamani ya zo amma ke har yanzu kina nan da kanki irin na kifaye kin kasa wayewa ki ci lokacinki ki fita kina ƙamshi yadda duk wanda ya kalle ki zai yi sha'awar ƙara kallonki ya san ke ɗin matar Alhaji Shatima ce, tsuwww wani lokacin kamar mai hankali ashe amma minti ɗaya sai ki dawo riƙakkiyar mahaukaciyar kidahuma, Wallahi aure ma zan yi na auro ƴar bana bakwai mai wayewa ba irin ki ba aikin banza, kalleki gaki fara sol mai jiki da ƙyan diri ga gashi gaki doguwar mace kamar ke ki ka yi kanki ,amma duk sai kike kunshe jiki a cikin hijabi.. "Ko irin ɗaurin ɗan kwalin nan da ake a fito da gashi ya zuba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31