Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jika da ita amma har take ce masa tsohon najadu kamar ta gansa yana abin da bai dace ba, anya kuwa Alhaji ya san abin da yake yi kuwa? Yara duk babu kamun kai ba nutsuwa musamman ma ita Fadilar da kowa ma a hanci take kallonsa kuma Daddy na gani ba zai ce komai ba akai.. "Maigadi lafiya dai ko? Maigadi ya juyo sautin muryar Daddy ya daki dodon kunnen shi hakan ya katse masa tunanin da yake yi.. "Alhaji dama wata mata ce da yaranta biyu a bakin ƙofa ta ce wai wajanka ta zo, ni kuma na ce mata baka sauraron irinsu in kuma saƙo ne ta kawo, amma firr matar nan ta ce ita sai ta ganka da idanunta, na koreta amma taƙi tafiya ta zau na yanzu haka tana nan bakin ƙofa.. Wani dogon tsaki Fadila taja tana shiga mota, shi kuma Daddy bai ce komai ba har ya shiga mota yabar harabar gidan... Yana fitowa ya ga matar zau ne da yaranta biyu kamar yadda Maigadi ya faɗa masa, dogon tsaki yaja yana tsayar da motar dan yaji dame ta zo masa... Da sauri matar ta miƙe ta kama hannun yaranta wanda basu fi shekarar 8 ba ta nufi bakin motar, durƙusawa ta yi cikin ladabi ta ce" Alhaji barka da fitowa da fatan na sameku lafiya." Sai da ya watsa mata wani banzan kallo kana ya ce" Barka dai wace ce ke dan ban ganeki ba?" "Ayya dama ba lalle ka ganeni da wuri ba, nice matar Malam Usman mai aiki a gidan nan.. Jinjina kai Alhaji ya yi tabbas ya tuna Malam Usman mai bawa fulawa ruwa da wankin kayansa, kallonta ya yi yana wani batsarwa ya ce" Yanzu ina shi Malam Usman ɗin dan tun da ya ce zaije gida ya gano iyalinsa ban sake jin labarinsa ba?" Goge hawaye ta yi sannan ta ce" Ai Alhaji Malam ya rasu tun wata shida da suka wuce, bayan ya tafi daga nan basir ya tasan masa bai kwana ba a daren ya rasu, to kafin ya mutum ya bar mini wasiya ya ce idan rai ya yi halinsa na zo gidan da yake aiki, a bani albashinsa na rabin shekara da ba a basa ba sai na sa yaran nan a makaranta suma su yi ilimi, shi ya sa na zo Maigadin gidan ya hanani shiga sai na zau na anan.. Nan da nan Daddy ya haɗe, kauda kanshi ya yi cikin basarwa ya ce" Kinga malama babu kuɗin da yake bina da wata ya yi nake bashi albashinsa, shi ne dan a wulaƙantani a duniya har da barin wata wasiya? To bazan bayar ba matsa ki bani guri kar in take ki na taka banza Wallahi" Ya ƙarashe maganar yana tashin motar.." "Don girman Allah Alhaji ka bani hakkin mijina, na tabbatar ba zai mini ƙarya ba yana binka kuɗin nan me ya sa za ka ce baya binka? Kaji tsoron Allah Alhaji kar son zuciya ya kaika ya baro, yanzu ko tausayin marayun nan ba zai sa ka ɗauki hakkin ubansu ka bani ba? K.. Bata ƙarasa ba taji sauka mari tas tas, a gigice ta ɗago fuskarta ta sauke idanunta akan Fadila dake tsaye a gefenta... "Karki kuskura ki faɗawa Daddyna maganar banza, matsiyanta banza kin zo nan ki goga mana tsiya ko me? To ku wuce ki bar mana ƙofar gida idan na sake ganin ƙafarki a wannan Unguwar sai na sa an miki ɓalɓalle.. Jinjina kai matar take sai kuma ta kama ɗiyanta da suke kuka ganin hawaye a idanun mahaifiyarsu, matsawa ta yi ta kalli Fadila ta ce" Yarinya kibi duniya a sannu in zalinci kike ji Fir'auna ma ya yi nasa zamanin an shude tarihinsa bare ke, tsakanina da ku Allah ya isa bazan yafe muku ba in sha Allah sai kunga sakayyar Allah akai zalincin da ku ka yiwa mijina har ya rasa ransa" Tana gama faɗin haka ta juya ta wuce a gurin.." "Sai dai kiga sakayya a kanki la'ananniya mun fi karfin kazafinki" Cewar Fadila tana komawa cikin mota... Auta bayan sun taso daga karanta a inda take haɗuwa da Amra tasa direba ya tsaya ta nufi gurin tana ta dubawa amma bata ganta ba, ta jima tana jira amma shuru hakan ya sa ta haƙura da nufin gobe in Allah ya yarda za ta zo mata da kayan sakawa... Suna isa gida bayan ta cire kayanta ta yi wanka sannan ta sauko ƙasa, Kande ta samu tana jera kayan abinci akan darning table, murmishi Kande ta sakar mata ta ce" A a Auta yaushe ki ka dawo?" Itama murmishin ta mayar mata sannan ta zau na akan kujera kana ta ce" Yanzu na dawo wanka kawai na yi yunwa ta fito dani." Abincin ta zuba mata ta koma ciki ita kuma ta zuba tagumi ta lula duniyar tunani. "Kai Auta wai har ki ka cinye abincin kenan?" Kande ta faɗa tana waro idanu ganin kwanon gaban Auta ba komai.. Da sauri Auta ta kalli kwanon gabanta, miƙewa ta yi tsaye tana kallon Kande cike da al'ajabi ta nuna kwanon da hannu ta ce" Wallahi banci komai ba a tafiyarki ni tunanin Ƙawata Amra nake ma, waye ya cinye mini abincin kenan?" Itama Kande da al'ajabi take kallon Auta ,a ranta tana cewa in ba Autar ta cinye ba to wa zaici abincin bayan ita kaɗai ce palon? "To nima dai ban sani ba kawai ki zuba wani kici tun da yunwa kike ji.. A sanyaye ta zau na tare da janye kwanon ta janyo wani ta zuba shinkafa da wake da miya, bismillah ta yi kana ta soma cin abincin cikin sauri saboda abin da ya faru na ya girgiza mata zuciya.. Tana gamawa ta miƙe har ta nufi ɗakinta sai ta tuna Teddynta fa a motar Sudas da ya kaita school, saba baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce" Allah sarki Baby bari Yaya Sudas ya dawo zan ɗauko ki a motarsa." Wucewa ta yi ta shige ɗakinta... Sudas na dawowa ya tafo da ƴar Teddyn Auta cikin palo, ko da yazo bai aje ta ba ya wuce ɗakin shi da ita ya jefa ta kan gado ya shiga wanka.. Yana buɗe ƙofar toilet zai fito yaja baya turus ya tsaya, sake da baki yake kallon kayan sakawar shi yashe a tsakar ɗakin an yi ɗaiɗai da su, ƙarasa fitowa ya yi ya sunkuya ya tattara kayan ya cusa a drower ɗin, ƙananan kaya ya saka singleti da gajeran wando iya gwiwa ya fito zuwa palo.. Bai samu kowa ba ya zuba abinci ya ci yana ci yana sauraron wata sabuwar wakar turanci data fito.. Sauban ne ya shigo gidan kamar yadda ya saba yana fito tare da takun rawa yana wani lallankwasa jiki, sai waka yake rerawa da bakin shi yana rawar har ya iso gurin Sudas da shima tashi wakar yake ji.. "Mazajeeee" Cewar Sudas ya bashi hannu suka tafa kana ya zau na... Kasan yau kuwa na haɗu da wata baby mai shegen kyau, nifa ina jin aurenta zan yi dan taƙi bani haɗin kai" Sudas ya faɗa yana shafa ƙirjin shi.. Dariya Sauban ya yi sannan ya ce" Kai wai da gaske aure

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});