Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sha Allah sai ina haka ki ka sha ado? Ko kuma kema shagalin birthday za ki yi tare da mu?" Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya tare da riƙe hannunta yana bin hannun da kallo... Dariya Auta ta yi ta ce" Tab waye zai zau na shagalin birthday wai? Ba dai ni ba gaskiya ni na yi kwalliya ne dan Mommyna za ta dawo daga inda ta tafi, yanzu ma yunwa ce nake ji shi ya sa nazo Anty Fadila ta zuba mini abinci naci." Da sauri ya miƙe ya ce" Ki rabu da Fadila dama can dukanki take bare yau da taga tana yin birthday, muje da kaina zan zuba miki abincin kici" Ya faɗa yana janta suka nufi kan darning table. " Sake da baki duk suka bisu da kallo, Mufy ta yi tsaki ta ce" Wallahi Bash ya dai ji kunya wannan zai ke wani likewa, ni har ya sa naji kunya Wallahi." "To ki ka sani ko yana mata haka dan ya hutar da Fadilar" Cewar wata dake gefen Fadila... "E kuma fa haka be to shi kenan ai gara hakan.. Kujera yaja mata ta zau na ita dai sai kallon ikon Allah take, abincin ya zuba mata ya aje a gabanta ya saka cokali ya ɗiba ya nufi bakinta yana murmishi ya ce" Ha Ƙanwata kici abincin ni zan rakaki duk inda za ki tafi." Ɓata rai Auta ta yi ta ce" Ka aje naci da kaina Malam, nifa ba yarinya ba ce ba girma yanzu da a bani abinci a baki inba Mommy ko Daddy ba' Ta ƙarashe maganar tana amshe cokalin ta yi bismillah ta shiga ci hankali kwance... Tun ta fara cin abinci ya zuba idanu yana murmishi har ya gama ta miƙe tsaye, ji ta yi ya yi carab da hannunta ta yi saurin juyowa a fusace ta ce" Kai cikani ko in zabga maka mari Wallahi ko an faɗa ma nima ƴar iska ce irinku? To ka fita safgata ka gane" Ta ƙarashe maganar tana wani ƙofa... Fadila ta daddage ta kawo wata irin ashariya ta kundumawa Auta tana cewa" Ke dalla can banza shashasha dan ma kin samu ya miki magana, duk matan gurin nan ba su dameshi ba ke dan kin samu ya miki magana ma." Tsaki Auta ta yi ta ce" Can ke ki ka sani mahaukaciya kawai shedaniya marar kamun kai, sai kin haɗu da daidai ke." A fusace Fadila ta miƙe ta iso gurin Auta bata tsaya yin komai ba ta zafga mata wani irin mari mai shiga jiki, gani ta yi Auta ko gizo bata yi ba kuma ba ta yi kukan data saba yi ba, hakan ya sa ta kuma marinta shima bata matsa daga inda take ba.. "Ni ki ka mara? To yau saina rama. Dariya Fadila ta yi ta sunkuya ta ce" Ga fuska in kin ki r.. Bata ƙarasa ma taji sauka mari wanda ya sa taga taurari, kafin ta dawo an kuma ɗauketa da mari wanda yafi na farko zafi. A razane ta ɗago ta kalli da take wasa da zoben hannunta, ihu ta kurma ta yi kukan kura ta damƙi Auta ta ce" Ni za ki mara yau sain.. Wutar palon ce ta ɗauke dif, Friend ɗin Fadila ya matso kusa da Auta ya lalibota yana bata haƙuri ya rungume ta da wayo ya soma taɓa ƙirjinta yana cewa ta yi shuru ta rabu da Fadila, wani irin ihu ya kurma ji kake tim.... *Kwana biyu kunjini shuru naje Unguwa ne kuma can ɗin ba network mai kyau, ina godiya a gareku da wanda suka miki magana ta pc da masu kira duk ina muku fatan Alkhairi Ubangiji ya bar ƙauna much love masoya😘🤗🤗* _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [01/12, 22:59] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ _Ina kuke masu jiran a gama littafin *ABBA NE* to ku garzayo jira ya ƙare an gama sa complete za ku same shi a farashi mai sauƙi akan N500, ga masu buƙatar ku tuntubeni ta WhatsApp number na.👇🏻_ *WhatsApp number +966599791573* 0️⃣6️⃣ Itama Fadilar ihu tasa tana ƙanƙame jikinta, wata irin iska ce ta shiga kaɗawa a palon, tuni kowa ya dunga gwaran kai da na kusa dashi, maimakon su yi addu'a sai suka shiga ihu da kiran juna.. Ɗaya bayan ɗaya ake binsu da gyararren mari a ko wani kunci ai kuwa suka kuma cika palon da ihu, Auta ta miƙe ta nufi inda ta ci abinci, tana isa ta sunkuya ta ɗauko ƴar Teddynta ta rungume tare cewa" Anty Fadila ku kunna mana haske bana ganinku." "Wani ɗan iskan ne zai kunna miki dan uwarki? Wallahi ki ka sameni da kiran in wuta ta dawo dukan mutuwa zan miki, kina ga.. Bata ƙarasa ba taji saukar wani abu mai shegen nauyi akan bayanta. "Waiyo Daddy na mutu na lalace shi kenan ƙila suminti ya faɗo mini a gadon baya" Ta shiga faɗa tana huci da ƙyar saboda nauyin da aka ɗaura mata yafi ma na buhun sumintin... Friend Fadila na ƙasa yana ƙoƙarin tashi aka ja shi baya, zane shi aka shiga da bulalar doki. "Waiyo! Fadila tana kuna da Aljannu a gidan nan naku? Shi kenan hannuna ya karye waiyo na shiga uku Mami sun karya mini hannuna" Ya ƙarashe maganar tare da kurma wani zababben ƙara na azaba kana ya baya ya sume... Fadila ta shiga laliben Friend ɗinta tana kiran shi da" Jon! Jon! Jon! Wai kana ina?" Saukar ruwa mai zafin gaske taji a bayanta hakan ya sa ta saki ƙara tana faɗuwa ƙasa ta shiga birgima, saboda azabar da take ji bata san ta kai gaf da kujerar palo ba ai kuwa ta buga goshinta a jikin ƙafar kujerar, ihun ta kuma sakawa tana jan jiki ta yi baya tare da riƙe goshi tana jin wani lakar zafi wanda bar kan babban ɗan yatsarta ta jishi zafin ba shi da misali.. Girgiza palo ake ana ta yin wata irin dariya mai firgitarwa, tuni wasu suka dinga sakin futsari a jikinsu wasu kuma saboda tsananin firgita har zayo suka saki a jikinsu ba su sani ba, can dai suka ji ɗif shuru babu komai, sai da suka ɗauki kusan minti uku a haka kana suka fara jiyo gudu ana ta zagaye palon, tuni kowa ya soma neman cetan ranshi, wasu a jikin kujera suka maƙale wasu kuma a ƙarƙashin darning table suka liƙe suna zunduma ihu, kowa kiran kowa yake yayinda wannan ƙaran gudu ke funfair gadan-gadan kamar zai hau kansu.. Suna a haka suka ji komai ya dena rawa na palon shuru, harhada kan komai aka shiga su kuma nata ihu har aka gama, wutar palon ce ta dawo haske rau.. Sake da baki kowa yake kallon shi a inda ya zau na, shi ko Jon yana can gefe yashe a sume, Fadila na kusa dashi ta riƙe goshinta da yake mata mugun raɗaɗin azaba, kanta suka yo suna ta kiran sunanta ita da Jon.. Kande ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe maggi, ganin Fadila a ƙasa ta nufesu da sauri tana faɗin" Subhanallah Fadila me ya faru dake haka?" Cike da mamaki Fadila ta tsayar da kukan da take ta saki

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});