Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

za ka yi? To ina ku ka haɗu da yarinyar?" "Ƙawar Auta ce sunanta Amra duk da ƴar talakawa ce amma fa yarinyar in ta ƙara girma za ayi babbar mace.. "Tsuww Wallahi ka bani kunya yanzu Ƙawar Autar ce za ka wani ce kana so?. "Kaga Malam ni naga abin da na gani na ce ina so dan haka ka zuba ido ka gani zan aureta, so nake Mommy ta dawo na faɗa mata dama ta ce ta gaji da za ma damu a haka.. Shi kam Sauban bai ɗauki maganar Sudas da muhimmancin ba ya ci abincin shi ya wuce ɗakinsa... Da dare kasancewar Daddy bai dawo ba ba wanda ya zau na yin hira suna gama cin abinci kowa ya shiga ɗakinsa.. Sudas na kwance iyapis na manne a kunnen shi yana kallon wani vidéo da budurwar shi ta turo masa, itace ta turo kanta ta yiwa kanta vidéo ba kaya a jikinta tana masa kalamai tana ce masa duk abin da yake so indai tana da shi za ta mallaka masa shi.. Da sauri ya miƙe ya gyara kwanciya ya danna mata kira vidéo call ya haska wutar ɗakin, tana ɗaga kiran ya zau na. "Hey Sweetheart da gaske kike maganar da ki ka faɗa mini a video nan?" Ya faɗa yana ƙura mata idanu... "Sosai ma mai kake so daga gareni ni kuma zan baka shi" Cewar budurwar ta shi.. Wani shu'umin murmushi ya saki sannan a ranshi yana cewa lalle za aje dake kema, a fili ko ya ce" Yawwa yanzu ki mini kamar yadda ki ka mini vidéo nan, in ki ka mini haka to zan tabbatar kina mugun sona kuma za ki iya komai a kaina." Jikinta na rawa ba muso ba tunanin komai ta kwabe kayan jikinta ta dawo tsirara ta zau na tana hasko masa duk wani albarkatun jikinta yana gani, shi kuma sai cewa yake" Yes Baby ashe kina sona love you so nake ki hasko mini kanki gaba ɗaya na ganki, zan iya komai domin ke.." Ta ɗaga baki za ta yi magana dif wayar ta ɗauke.. Oh my god shiii! Ya faɗa yana wullar da wayar gefe ya janyo ɗayar wayar ya shiga ƙoƙarin kunnata, kin kawowa ta yi ya aje ta a gefe.. Wutar ɗakin ce ta ɗauke, tsaki yaja yana cewa" Ai kaji matsala kana cikin jin daɗinka amma sai a ɗauke wuta.. Wutar aka maido sai yaga gilmawar wani ɓakin abu ya wuce da sauri, a zabure ya kalli gurin yaga wayam, shafa bayan shi yaji anyi ya juyo nan ma yaga ba kowa. Tuni tsoro ya mamaye Sudas jikin shi ya ɗauki rawa ya yi saurin rufa da fargo zai kwanta aka yi sama dashi shuu. Kwalalo idanu ya yi cikin firgici da tashin hankali ya soma zunduma ihu ganin yadda ake royal da shi a saman ɗaki.. Waiyo Allah! Ya faɗa da ƙarfi aka sakoshi ƙasa tim, kanshi ya buga a jikin gado ya kuma zunduma wani ihun yana ƙoƙarin tashi, yana buɗe idanun shi ya yi arba da wata ƙatuwar Teddy mai kai biyu idanunta baƙaƙe manya-manya ta nufo shi gadan-gadan.. Waiyo! F..... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [27/11, 22:36] Maman Nusaiba: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *Ga masu son Littafin Abba ne complete N500 ne su tuntubeni ta WhatsApp number ta gata nan a ƙasa👇🏻* _Masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi su nemeni ta WhatsApp number na_ _WhatsApp number +966599791573_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 0️⃣4️⃣ "Waiyo! Fatalwa mai na miki ki yi mini rai Mama fatalwa karki kasheni, Wallahi ban gaji da rayuwa ba ina da sauran burukan da ban cika ba ki taimaka" Ya faɗa yana sakin futsari haɗe da tusa. Tuni jikin shi ya jiƙe sharkaf da zufa haɗe da futsarin da ya yi.. Wani irin dariya aka kwasa wadda ta karaɗe ɗakin ba ki ɗaya, ɗakin aka shiga girgizawa kamar zai kife cikin ƙasa. Sake yin sama aka yi dashi zuwa saman silin ɗakin ana yin juyi dashi a samar, ƴar Teddyn nan ta ƙara nufo kan Sudas da ya ƙame a sama tamkar gunki yana zaro idanu, tana isowa ta miƙa hannayenta wanda suke ɗauke da zaƙo-zaƙon faracuna masu karfi, ƙafar shi ta kama tana dariya mai firgitarwa ta yo ƙasa da shi ji kake tim ta sakoshi kan gado.. Ihu Sudas ya kuma zundumawa yana ƙudundunewa cikin bargo, ji ya yi an kai masa rungume ana shafa kan shi haɗe da bayan shi, idanunsa ya buɗe ai ko ya yi arba da ƴar Teddy ta rungume shi a jikinta.. "Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, Mama fatalwa ki mini rai z.. Bai ƙarasa fa aka zafga masa mari, magana ƴar Teddyn ta fara magana cikin wani irin amo marar daɗin saurari.. "Dama kai kasan Allah ne kake kiransa? Mugu azzalume mai son ɓata rayuwar bayin Allah, to saina aikaka lahira inyaso sai kaje can ka yi tijarar da kake yi anan duniya.. Tun da aka mari Sudas ya sume.. Wata sanda ce ta bayyana daga saman ɗakin, kallon sandar ƴar Teddyn ta yi idanunta sun yi jajur suna zubar da hawayen jini ta ce" Ku lallasa mini ɗan iska." Dukkan Sudas aka shiga yi tako ina ita kuma Teddy ta ɓace daga kan gadon ta dawo samar ɗakin tana kyakyata dariya marar ɗakin ji.. Dukan Sudas ake ba kakkautawa, tun yana cikin suma dukan ya farfaɗo dashi ya shiga kwara ihu yana kiran Daddy da Fadila da Sauban.. Sai da aka masa lilis kana yaji an dena dukansa, a daddafe ya miƙe ya sauko daga kan gadon yana nufar ƙofar fita daga ɗakin, har ya kai hannu zai buɗe ya yi wani tsalle ya dawo baya yana mayar da numfashi tare da ja da baya.. Ƙatuwar macijiya ya gani a jikin ƙofar ta kwanta ta yi luf, idanunta fari ƙal babu ko ɗugon baƙi da cikinsa, kanta guda biyu ne jikinta ma haka fari sol, ƙurawa Sudas idanu Macijiyar ta yi tana fito da harshe tare da fasa kanta tana huci. . "Shi kenan na mutu na lalace don girman Allah ki yi mini rai fatalwa duk abin da kike so zan miki z... Maganar shi ce ta katse jin ana buga ƙofar da ƙarfi, yana son isa ya buɗe amma ba hali macijiya na jikin ƙofar. "Yaya Sudas! Yaya Sudas! Ka buɗe mini ƙofa zan ɗauke Teddyna na kasa bacci da ban ganta ba. Waro idanu ya yi jin muryar Auta sai kuma yaji ta Daddy da Sauban, ihu ya kurma yana faɗin" Daddy ku taimakeni fatalwa a ɗakina za ta kasheni" Ya faɗa yana jan majina." Da ƙarfi Sauban ya buga ƙofar ta ɓalle, duhu ne ya mamaye ɗakin Sauban ya ce" Kai ɗan rainin hankali ka kunna wutar ɗakin mana tun ɗazu nake jin ihunka." Sudas dake manne a jikin bango yana zare idanu ya ce" Don Allah ku kunna ƙafafuwana sun karye." Dariyar Fadila yaji tana ce masa matsoraci wai ya damesu da ihu a gida, bai ce mata komai ba burin shi bai wuce ya buɗe idanu ya gansa a kusa da su ba. Sama aka yi dashi zai yo ihu yaji an rufe mata

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});