Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mata hannun ya tsaya cak, kiciniyar sauke hannun take amma ta kasa, bulalar ce ta yi sama aka shiga zuba mata ita tako ina sai ihu take tana kiran ƴar mairo... Wani duka aka kawo mata bakinta saiga hakoranta na gaba sun zubo ƙasa, ihu ta kurma ta zabura hannunta a sama ya kasa yin ƙasa ta nufi hanyar fita waje, kafin ta isa aka sauke mata ƙyawawan mari, gashin bayanta ne ya yi wani irin ƙara ƙaƙaratttt! Ihu suka sa duka falon ai kuwa bulalar nan ta ta shiga zanesu tako ina, Ƴar Maigado ta ci sa'a aka barta ta buɗe ƙofar palon, zaninta a hannu daga ita sai sket na ciki kanta ba ɗan kwali ta fito a 360 tayi wata irin suka sai gata a samar katanga.. Baba Maigadi ya kalleta da sauri ya ce" Ke karfa kiji ciwo ki sauko na buɗe miki ƙofa, wani abin ne yake faruwa a ciki?" Ƴar Maigado ta watso ƙafafuwanta bayan katangar ta juyo ta kalli Maigadi ta ce" Uwarka ce take faruwa ashe haka gidan nan yake da aljannu." Maigadi zai sake magana Ƴar Maigado ta kurma ihu ganin wata ƙatuwar mage ta yo suna za ta hayo katangar, a firgice ta wuntsila ta faɗo waje timmm! A guje ta bi haya kamar sabuwar kamu yi take tana waiwaye magen nan data biyo. "Takalmanta a hannu tana tana falfala gudu kamar za ta tashi sama, rigar jikinta granbubu ce tana gudu iska ta cikata, ganin fa da gaske magen nan bata dena binta ba ta zubar da takalman ta dinga ihu tana faɗin" Ihu jama'a taimako! Taimako! Aljana ta biyoni ku tareta kar ta iskoni.. Duk inda ta nufa a guje wanda suke zau ne da sun hangota tana ihun nan za su kwasa a guje su yi gaba.... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [02/12, 23:18] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *WhatsApp number. +966599791573* *بسم الله الرحمن الرحيم* 0️⃣7️⃣ Auta ta kwanta a ƙasa tana birgima dan ba ƙaramin zafin dukan taji ba, miƙewa ta yi daga kwanciyar da ta yi ta kalli su Fadila da suka yi shuru suna kallonta, tsaki taja ta nufi kan darning table ta buɗe babbar kular da Fadila tasa aka haɗawa saurayinta.. "Ke! Dan uwarki karki taɓa mini wannan abincin, duk abincin dake kan darning ɗin sai na wannan kular za kici? Bata kulata ba ta gyara za ma tana huci mai ƙarfi kamar mai ciwon fuka, hannu ta tattare ta saka a ciki ta ciko hannu da dambun kuskus da yaji kayan haɗi yana zuba ƙamshi ta kai bakinta ta kuma danna hannun ta ciwo ta ƙara cusawa a bakinta, da ƙyar take juya abincin dake cikin bakinta sai zare idanu take. Kafin Fadila ta yi taku biyar zuwa gurin Auta tuni ta dinga hannu baka hannu ƙwarya kan kace mai tini babu dambun ta cinye tass. "Kuturun uban can! Auta ke kuwa ki ka cinye abun nan ko kuwa aljannun naki ne suka tayaki? To Alkur'an sai kin rama mini dambu na ko in miki dukan mutuwa dan kakan uwarki. "Karki ƙara zagina malama, dambu kuma na ci sai dai ki farka cikina ki fito dashi in kika takura mini zan sa masoyina ya miki dukan tsiya, banza ke da ko ruwan zafi ba ki taɓa ɗaurawa ba ma" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki gaba tare da daura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙarewa Fadila kallo.. Tab dijam! Ke yanzu duka nawa kike da har wani sakarai zai kulaki da sunan soyayya? 14 years fa gareki ita ma sai nan da wata biyar za ki cike 14 years ɗin, anya ba aljannun jikinki bane suke da samarin? Hmm aikin banza an yi sadaka da karuwa.. "Amma dai an ta raya sunnar ma'aiki ko? " Cewar Auta tana murmishi mai ɗauke da ma'anoni.. Sake da baki Mufy take kallon Auta sai kuma taja tsaki ta ce" Aminiya ki rabu da wannan ƴar shilar ina mutumci haka zuwa maka da kare, wannan yarinyar in kika biyata ai sai mutumciki ya zube a banza ta take. "Dama na gama take shi ai" Ya bawa Mufy amsa tana shafa gefen fuskarta.. Riƙe baki Bash ya yi jin yarinya ƙarama na zaro magana kamar wata ƴar shekara 20, Jinjina kai ya yi ya miƙe yana cewa" Fadila ni zan tafi gida a gyara mini hannuna, ina tunanin ki bar birthday ɗin nan sai gobe kawai, kinga shi Al'amin ɗin ya ce sai dare zai shigo Katsina kawai mu bari sai gobe tun da ba a kawo komai ba na birthday." Auta ta mishi kallon uku saura kwata ta miƙe ta wuce sama tana cilla ƴar Teddynta kamar ba ita ba ce yanzu take kuka tana birgima. " Tab Wallahi Fadila aljannun jikin Auta mayunwata ne, diba fa ki ga yadda ta tashi da ƙatotuwar kular abincin, gaskiya bari na wuce gida" Yana gama faɗin haka ya miƙe ya ɗauki key ɗin motar shi ya wuce daga palon.. Suma sauran duk barin gidan suka yi Fadila ta jadadda mu su gobe su fa zo kana suka wuce,cika yi ta yi fam tana nufar sama.. Amra ce ta tafi daga gidansu sanye take da doguwar riga amma tsanyin nata mai rufe ta ba har ƙasa iya kwafrinta ne kawai, shagon wani mai shayi ta nufar tana ɗan wake-wakenta cikin nishaɗi har ya iso gurin. "Yarinya mai za a ba ki ? Cewar mai shayin yana kallon Amra.. "Dama zuwa na yi ka taimaka mana, ba mu da komai ga yunwa da nake ji ka taimaka ka bamu an jima kaɗan zan kawo maka kuɗin ka" Cewar Amra tana matso hawaye.. "Kut! Waye zai baku bashin? Wai anya kuwa kin san Bala mai shayi kuwa? To duk Umguwar nan babu wanda bai sanni ba bana bayar da bashi , ki fice mini a nan ko na mika dukan mutuwa.. "Don Allah kada ka kureni ka bani koda na hamsin ne Innata bata ci komai ba kar ta mutu. "A fusace Bala mai shayi ya yo kan Amra ta sauke mata mari mai zafi, cikin masifa ya ce" Ni za ki kalla ki ce ba baki bashi dan kin rainani? To ki shiga hankalinki kar in kakkarya miki ƙafa kiji daɗin yin bara akan titi." Da ƙyar wani mutum ya zo wucewa ya kwaci Amra daga gurin Bala mai shayi, nunata ya yi da hannu ya ce" In na sake ganin ƙafarki a nan wajan gobe saina miki dukan da yafi wannan, banza yar matalauta masu ƙashin tsiya kalleta ko takalmin kirki bata da shi, za ki tafi ne ko saina miki abin da yafi wannan?" Kuka sosai Amra take ta koma gefe tana kallon Bala shayi tana jero masa da saƙon Allah ya isa shi kuma yana aiko mata saƙon zagi, sai da taga mutane sun yi yawa a gurin kana ta miƙe ta tsallaka titi ta nufi inda ta fito... Kwance take tana sakin murmishi tana juyi ita kaɗai akan gadon, da sauri ta buɗe idanunta sai kuma fashe da kuka ta ce" Haba wallahi ba zan yadda ba ka tafi ka barni, ka dawo mana please" Ta ƙarashe maganar tana komawa buduf ta kwanta tana

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});