Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana lumshe idanu. Ɗaukan ya yi cak ya miƙe tsaye, taku uku ys yi sai gashi a cikin ɗakinsa wanda ya tsaru gadon ma abin kallo ne , ɗaurata ya yi ya lulluɓeta da bargo shi ma ya haye gadon ya kwanta tare da janyota gareta ya lumshe, shafata yake yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta ta buɗe idanunta, so take ta dakatar dashi amma taji kamar an daure mata duk wata jijiyar jikinta, hannu yakai zai sauke akan ƙirjinta ta waro idanu ta ce" Bobby! Ta faɗa a zabure ya yi saurin rufesu da bargo, ihu ta kurma. Zabura ta yi ta tashi tana salati jikinta ya yi sharkaf da zufa, Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Me yake faruwa dani? Ta faɗa a bayyane dan ba ƙaramin tsoro ya kama ta ba da zarar ta tuna abin da ta gani a cikin mafarkin nata... Tashi ta yi taji bayanta na mata mugun ciwo haɗin da jikinta gama ɗaya, mamaki sosai ya rufe Auta tana dingisawa da haka ta shiga banɗaki ta soma yin wanka jin zafi ya hanata sukoni... Banko ƙofar aka yi lokacin ta fito daga wanka sanye da towel tana goge jikinta, da sauri ta kalli ƙofar taga suak haɗa idanu da Sudas dake mayar da numfashi yana riƙe da hannun shi hawaye shaɓe-shaɓe kwance a fuskar shi, da mamaki ta kalle shi sai kuma ta kwashe da dariya ta zau ne a gaban madubi ta shafa mai, bayan ta gama ta ce" Yaya Sudas wai lafiya na ganka da daren nan kamar an koro ka?" "Babu lafiya Auta taimaka ki mini ruwan zafi ina jin na ƙarfe" Ya ƙarashe maganar yana yin zaman 'yan bori . Dariya Auta ta kuma yi ta shiga banɗaki ta kawo ruwa a cikin wani bokati, zama ta yi ta ɗauki towel ɗin ta ƙaramin ta dubesa ta ce" Yaya ina Yaya Sauban da su Anty Fadila? Ko kuma bacci suek yi ne? Jam majina ya yi yana gunjin kuka kamar wani yaro ya ce" Waiyo Allah Auta! Ki dena mini maganar su ki gasa mini dan naji saukin azabar da nake ji." Murmishi ta kuma yi ta ɗauko ta danna masa da karfi, ihu ta kurma yana kwace ƙafar saboda tsananin azaba a gigice ta nufi bakin ƙofa ya rarrafa da sauri zai fita sai kuma ya yi maza ya dawo yana kuka wiwi ya zauna a bakin ƙofar ɗakin yana rufewa. Mamaki sosai ya kama Auta ta isa gareshi tana ce masa lafiya amma ya kasa bata amma, dawowa ta yi ta ɗauki ruwan ta zo gurinsa ta ce" Yaya ka tsaya don Allah a gasa ma targadan naka." "Wash Anty Afra don Allah ki dena mini da ciwo da hankali za kike yi kar ki ƙarasa ni kin.. Kwashewa ta yi da dariya ta ce" To Yaya yau kuma nice na sawo Anty Afra ba Auta ba?" "E kece ko Mama zan ce miki tun da mun samu an dena mana duka"Ya faɗa yana wani narkewa kamar yaro ɗan shekara 3.. Dariya Auta ta kuma yi ta gyara ta soma gasa masa a hankali, idan taji ya yi shuru sai ta danna masa da karfi ga ruwa akwai zafi sosai, ai kuwa sai ya kurma ihu yana kiranta da Yaya Afra a haka har ruwan ya wuce... Su Fadila da Abokanta a palo sai da aka gama lallasa su aka gaji kana aka dawo da wutar palon, da ƙyar kowa yake motsawa daga kwanciyar da ya yi, abin da ya ba su mamaki komai na palon tsaf yake duk futsari da zawon da suka yi babu a ƙasa ko akan kujera sai a jikinsu kawai suke jin tsami... Ana gama salla a Masallaci Mufy dake kwance tana jin ƙafarta da hannunta kamar ba'a jikinta suke ba ta lalibo jakarta ta dannawa Mommynta kira, tana ɗauka ta dinga mata kuka tana bata labarin abin da ya faru da su, abin ya bawa Mommynta mamaki ta turo mata mota aka zo daukanta, da jan jiki ta fito daga palon tana kuka wiwi hannunta har ya kumbura ya yi sintum ya mata nauyi, shi kanshi Direban gidansu da ya ganta sai da ya tsorata, taimako ta nema ya sata a motar na fa ya gara jinjina abin da ya samu Mufy wai yau shi ne take cewa ya taɓa jikinta ya taimaketa ta shiga mota? Sai da ta kuma maganar da muryar kuka kana ya ɗagata cak kamar yarinya ya sakata a mota yaja suka bar gidan.. Haka sauran kowa kira ya yi aka zo aka ɗauke su , labari suke badawa gidan su Big girl Fadila aljannu ne kamar kan tsamiya, wasu sun ce sun yanke ƙawance da Fadila wasu kuma sun ce za su ƙawance amma ba za su zo gidan su ba... Mommy da kanta ta taimakawa Fadila suka shiga toilet din palo ta gasa mata jiki, ita kanta abin ya firgitata na jiya gadda aka wullata ɗaki aka rufo ƙofar gam... Daddy sai da ƙarfe 6 na safe ya fito daga wani part dake can jikin ɗakinsa, shi kansa hankalinsa a tashe yake matuƙa, amma sai ya nuna ban ga komai ba a jiya aka ɗauki Fadila da Sudas da Sauban zuwa Asibiti.... "Doctor!Doctor ka taimakeni ga Ƴata na kawo ka duba ta karka tafi gida" Cewar wani tsoho yana binsa kamar zai yi kuka... A fusace ya juyo ya gagga masa magana ya wuce har da zagi ya shiga mota ya bar Asibitin, dafiya yake ya zo kusa da Masallaci yaji ana kiran Sallar Isha'i ya tsaya ya nufi ciki.. Bayan ya yo tsarki ya zauna zaman alwala, da farko ya fara wanke fuska kana ya shafa ruwa a kai, ya wanke hannu sannan ya wanke ƙafafuwa cikin sauri ya shige masallacin, wani dake kusa dashi ya ce" Kai jama'a yanzu duk yawancin samarin zamanin nan ko alwala ba su iya ba." Bayan an gama ya fita da sauri ya wuce zuwa gidansa... A hanya yana kan tafiya ya hango wata Saniya babba a tsakiyar hanya ya kai mata karo ji kake kiiiii! _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [12/12, 22:59] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣2️⃣ "Subhanallah! Yake faɗa jin an yi sama dashi sosai ya runtse idanu jikinsa na rawa tsoro da firgici sun dabaibaye shi, jin komai ya lafa ya sa shi buɗe idanunsa a hankali har ya gama buɗewa cike da mamaki yake kallon inda yake yana shafa inda aka zaunar dashi, "To waye ya kawoni gida kuma? Ya furta maganar tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki.. Kafin ya yi wani ƙwaƙƙwaran motsi yaji palon ya ɗauki amsakowar wata murya mai amo marar daɗin ji , tuni ya maƙale a jikin bango yana zare idanu tamkar ɓarawon da aka kama a bainannasi jikinsa na ɓari ya soma faɗin" Waiyo Allah na shiga uku! Shuuu yaji an wuce ta gaban shi tamkar wucewar mikiya, ihu ya kurma yana ƙara mannewa a jikin bango tare da rufe fuskar shi. "Buɗe idanunka na ce! Yaji an faɗa a karfi kamar za a fasa masa dodon kunne ya buɗe fuskar ya rufe kunnewan shi kana ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan dan yaga

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});