Chapter 10
Chapter 10
Za ma ta yi tare da kai hannu ta soma shafa fuskar Auta tana kiran sunanta, a hankali ta fara buɗe idanunta har ta gama buɗe su akan Amra dake mata murmushi. Da sauri ta zabura ta tashi ta kama hannun Amra cikin nuna tsoro ta ce" Amra ba dai abin da ya sameki dai ko? Ina Zakin nan yake da na gansa a sama?" Ta ƙarashe maganar da tambaya tana shafa jikin Amra." "Ai na kore shi ki dena jin tsoro Ƙawata yanzu dai gamu a gidanmu na kawo ki. Da sauri ta ɗago tana kallon ɗakin wanda ba shi da komai sai gadon ƙarfe wanda take kai, gefe ta kalla inda taga langogi an jerasu ƙasar ɗakin rairayi ne ja a shara tass babu wani datti, ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Ashe nan ne gidanku to ina Innar take?" "Inna ai bata nan taje Unguwa daga ni sai Aliyu ƙanena gashi nan a bakin ƙofa zai shigo" Ta faɗa tana mata nuni da ƙofar ɗakin.. Kallon ƙofar ta yi inda ta yi arba da Aliyu tsaye yana mata murmushi, itama murmishin ta mayar masa ta ce" Ya sunanka?" "Aliyu sanana" Ya bata amsa yana ƙarasowa hannun shi dauke da langa babba da ƙarama, yana isowa ya aje a gefe ya zau na.. Buɗewa Amra ta yi ta miƙawa Auta ba muso ta amsa tana kallon abin da yake ciki, koko ne a ciki ɗayar langar kuma ƙosai ne yana turiri, cikin zumuɗi ta sauko ƙasa ta zau na tare da yin bismillah ta soma cin ƙosan tana korawa da kokon. Sai da ta ci ta ƙoshi kana ta janye tana hamdala, murmishi ta yi mu su ta ce" Ban taɓa cin ƙosai mai daɗi irin wannan ba wa ya yi shi?" Aliyu ne ya yi saurin cewa" Yaya Amra ce ta yi ai." "Au kuwa kin iya Ƙawata. "Na gode. Hira suka soma cikin nishaɗi, suna a haka sai ga Amina ta shigo bakinta dauke da sallama. Kallonta Amra ta yi da mamakin ganinta, itama Amina kallon nata take tana sakin murmishi, a nutse ta ce" Yaya Amra wai mamakin ganina kike?" "E sosai ma ina fatan dai lafiya dai ko? "Gaskiya akwai magana Yaya Amra zp muje kiji. Da sauri Amra ta suka fita ta cewa Auta tana dawowa suka fita, can bayan ɗakin suka nufa su ukun, Amina ta ruƙo hannun Amra ta ce" Yaya Amra akwai matsala yanzu nan naje yankin su Amsar ya ce yana nan zuwa gurinki ki tayashi yaƙin ɗaukan fansa akan wani mutum, ke kuma nasan bakwa shiri dake sun tsara yadda za su tsaraki ki yarda da su yanzu haka nan da sati ɗaya za su iso can inda muke.. Jinjina kai Amra ta yi sai kuma ta yi murmishi ta ce" Amina karki damu zan ji da duk wani daɗin bakinsu, ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alkhairi.." Aliyu ya ce" Nifa ina tunanin Amsar akwai abin da yake nufi damu." "Karka damu Aliyu babu abin da zai faru mu koma Yamma ta yi inaso na kai Auta gida.. Juyawa suka yi duk suka nufi ɗakin inda suka samu Auta tana gyanyadi , tadata Amra ta yi, kallonta Auta ta yi cikin muryar bacci ta ce" zan tafi gida Amra bari na kira Direba ya zo ta ɗaukeni." "A a ni zan kaiki da kaina tashi maza muje na rakaki har gida" Cewar Aliyu yana murmishi." Ƴar dariya ta yi ta ce" Kai Aliyu a ina kasan gidanmu? Kaga ko Amra bata taɓa zuwa gidanmu ba." "Da gaske fa kedai ki tashi mu kaiki gida kuma kar ki mana kwatance daret gida za mu kaiki. To shi kenan kace dai ku 'yan baiwa ne da alama ko? Miƙewa ta yi tsaye Amra ta kama hannunta tana dariya ta ce" Auta rufe idanunki." Cike da mamaki ta rufe idanun nata tana cewa" Kai yau dai zanga baiwar Aliyu inaso yanzu na ganni a gida indai da gaske kasan gidanmu" Ta ƙarashe maganar tana ƙara riƙe hannun Amra.. "Buɗe idanunki Auta mun kawoki har bakin ƙofar gidanku.. A hankali ta buɗe idanunta, tana gama buɗe su ta ganta a bakin get ɗin gidansu, cike da mamaki take kallon su da kuma al'ajabi ta ce" Amra taya ku ka san gidanmu?" "Hmm ba dai kin ce bamu sani ba to gashi mun kawoki, yanzu sai an jima mu za mu koma gida" Cewar Amra tana rungumar Auta... "Na gode Ƙawata sai mun haɗu zuwa jibi gobe Islamiya ba tabbas ba ne muga juna, amma jibin zamu haɗu.. Sai da suka ga tafiyarta kana suka ɓace daga ƙofar gidan.. Tana shigowa gaishe da Maigadi ta yi kana ta wuce ciki, tin kafin ta shiga sautin kiɗa ya fara ziyartar kunnenta, tsaki taja tana haɗe tasa Kai ta shiga cikin palon... Ko kula kowa bata yi ba ta kawar da kanta gefe zata wuce, har ta hau kan stap taji muryar Mufy kawar Fadila na cewa" Ke Auta dawo nan na ce miki ko ba ki gansu ba ne" Ta ƙarashe maganar tana aiko mata harara.. Ba juyo ta kallesu ba ta yi saurin wucewa sama.. "Kan uban can! Wai Fadila yaushe wannan Ƙanwar taki ta raina mutane ne? Nifa da ni Ƙanwata ta yiwa Ƙawata Wallahi sai na kusa karya ƴar iska" Ta ƙarashe maganar hura hanci.. "Hmmm ki rabu da ita ɓakin ciki ne yake damunta dan taga Daddy ya sakar mini kuɗi ba iyaka ina shagalina, ki rabu da ita dama da safe ta zageni ta tafi, so nake na gama komai zan waiwaye ta ai... "To gara dai dan naga alama Yarinyar nan gaba sai ta soma dukanki.. *Washe gari* Tun da sassafe ƙawayen Fadila suka sauka gidan su, duk wanda ya zo sai an cika palon da ihun murna har duk suka gama zuwa saura saurayinta ya rage bai zo ba, a ɓangaren Auta kuma murna take Mommy za ta zo gida itama ta huta da hantaran da Fadila take mata, ko ba komai Mommy ba za ta bari ta daketa ba.. Cikin sauri ta yi wanka ta saka riga da sket ta sauko ƙasa fuskarta ɗauke da murmishi mai ƙayatarwa, dukkansu 'yan palon zubawa Auta idanu suka yi suna binta da kallo musamman ma mazan, wani friend Fadila ya kasa daurewa ya ce" Wow cute girl Fadila wannan Ƙanwar mu ce ko?" Cikin iyayi Fadila ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana shan ƙamshi kana ta ce" Yes this is my sister, ko ta birgeka ne?" "Kai sosai sai dai kamar yarinyar yanzu ta soma girma ma, idan ta kai shekarunki fa sai ta fiki komai. Ran Fadila ne ya ɓaci jin an ce Auta za ta fita inta girma, amma ganin suna ciki farin ciki sai ta yi shuru tana murmishi amma ƙasan zuciyarta na ƙara tsanar Auta fiye da da.. Tana isowa ta tsaya a gaban Fadila tana cuno baki ganin yadda suka zuba mata idanu, ta ce" Ku kuma lafiya kun zuba mini idanu rakatau ba wanda ya ce ma sha Allah inma kunga na yi kyau ne?" Da sauri friend ɗin Fadila dake kusa da Auta ya ce" Haba Ƙanwarmu ai ke kuwa ki ka yi kyau matuƙa ma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31