Chapter 28
Chapter 28
yi sanyi ta nemi izinin shiga ya juyo yana harararta tare da ce mata ta shigo ciki, a ɗarare ta shiga kanta a ƙasa tana karanto kalmar "Lailaha'illa antas subhanaka inni kuntu minan zalimin. Haka ta dinga faɗa har ta ƙaraso kusa da malamin nasu, wani kallo ya watsa mata ya ce" Ƙarfe nawa yanzu?" Jikinta ne ya ɗauki rawa a sanyaye ta ce" Malam Ƙarfe 8:30 ne." "Ok shi ne dan kin raina mutane har kika ƙara 30 minute ko?" Da sauri ta ce" A a Malam ba haka bane ka yi haƙuri Mommyna ce bata tashi da wuri ba bana makara sai yau shima akasi aka samu Malam." "Yiwa mutane shuru kin tsaya dai wani abun a hanya maza fita kafin na zaneki a gurin nan" Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita." Sum-sum Auta ta juya da nufi fita sai ta yi kicibus da principal ɗin su a bakin ƙofar sai ta tsaya ta gaishe da shi kana ta raba gefensa za ta fita ya dakatar da ita hakan yasa ta tsaya tana addu'ar Allah ya sa kar a daketa. Principal ya dubi malamin su Auta ya ce" Me ya sa ka ce ta fita daga aji?" Kai tsaye ya ce" Ta yi latti ne ranka ya daɗe." Ɗaure fuska Principal ya yi ya ce" Ka barta ta shiga kasan dai yarinyar bata yin latti dan yau ta yi kuma ta bada uzirinta ai sai ka karɓa ba ka koreta daga aji ba, kasan ma ɗiyar waye ita ɗin da kake daka mata tsawa haka? To karka bari labarin nan yaje kan kunnensa dan za ka yi ta aikinka har abada." Jin kalmar da Principal ya faɗa jiki na rawa ya ce ta dawo ta zau na, godiya Auta ta yiwa Principal cike da jin daɗi ta wuce ta zau na a mazauninta.. _________________________ Amra ce ta bayyana a inda Auta ta aje mata saƙo tana sanye da hijabi har ƙasa fuskarta a sanye da niƙaf, hannu ta miƙa ta dauki ledar haɗi da takardar tana sakin murmishi ta buɗe takardar dan taga saƙon mai ta ƙunsa rubutu ta gani kamar haka: "Assalam alaikum my Amraty ina fatan kina lafiya ya su Aliyu da Inna? To kice ina gaishesu da kyau ga abinci nan na kawo miki ku buɗe yau na makara shi ya sa ban tsaya mun gaisa ba, sannan in sha Allah na faɗawa Mommy ta biya muku kuɗin makaranta har Islamiya na bata labarinku to ta ce in sha Allah gobe za mu zo ni da ita sai mu ɗaukeku muje a sakaku ke da Aliyu, ina fatan za ki yi farin ciki da hukuncin dana yanke ba tare dana nemi izininki ba naji ta bakinki daga Ƙawarki Auta.. wasu hawaye ne suka zubo daga idanun Amra, a sanyaye ta ce" Saliha baiwar Allah in sha Allah ke ƴar aljanna ce." Juyawa ta yi sai suka haɗa idanu da kama hannun shi suka ɓace daga gurin... A ɗakinsu suka bayyana Amra ta zau na tare da aje ledar ta dubi Aliyu ta ce" Yanzu za mu samu damar shiga ko'ina na lamuran Auta ta yadda za mu gane waye wannan wanda yake tare da ita." Zama ya yi ya ce" Haka ne Yaya Amra sannan lokaci ya yi da za mu yi maganin duk wanda ya shiga gonarmu kawai ki kira Yaya Amina." Jinjina kai ta yi tare da miƙewa tana zagaya ɗakin wani kalar murmishi ta saki ta juyo ta ce" Zaki ka kwantar da hankalinka ni yanzu burina na gani waye wannan wanda yake ƙoƙarin cutar da ita? Sannan mai meye dalilinsa na bibiyar rayuwarta da wannan mummunar alaƙar?" "To Yaya Amra ki ka sani ko shima abin da aka mana shi aka yi masa shi ya sa ya biyo ta wannan hanyar dan ɗaukar fansa? Girgiza kai ta yi tana binsa da kullo ta ce" Bana tunanin hakan Zaki kawai dai akwai wata a ƙasa kuma koma meye za mu gano shi in sha Allah." Haka suka dinga tattaunawa a tsakanin dan neman mafita game da lamarin.. Washe gari kamar yadda Auta ta yiwa Amra alƙawarin za tazo da Mommy suka zo tare, a daidai inda ta saba tsayuwa Ɗanladi ya yi packing Auta ta fito da sauri tana kiran sunan Amra data juya baya ita da Aliyu Mommy na biye da ita a baya har suka iso gurinsu. Da murna suka rungume juna basu tsaya yin komai ba Auta ta kama hannun Amra suka iso gurin motar ta ce Amra ta shiga kana Aliyu sai Mommy ita kuma a gidan gaba yau harda su glass ta saka kamar wani ƙatuwar mace, tun da suka shigo Amra ta rufe idanunta ta yi shuru shi kuma Aliyu ya harde hannayen shi yana mayar da kallon gefen titi ta ɓangaren Amra.. Suna zuwa makarantar su Auta Mommy ta cike duk wani abin da ake buƙata ta buƙaci a saka su aji ɗaya da Auta aka musu tamabayoyi akan karatun su na baya suka faɗi suna aji 3 ne aka korosu daga makaranta, sosai Auta ta yi farin ciki sai godiya take yiwa Mommynta ta cire kuɗin ta biya kana ta fito Ɗanladi zai mayar da ita taji muryar Amra ta kira sunanta ta juyo ta sauri, a sanyaye Amra ta ƙaraso Mommy ta durƙusa ta ce" Allah ya saka miki da alkhairi Mommy kina da kirki ke da Auta baku da wulaƙanta na ƙasa daku Allah ba zai taɓa bari ku wulaƙanta a idanun duniya ba Mommy, bani da bakin gode miki sai dai na yi ta miki addu'a" Ta ƙarashe maganar tana goge kuntun hawaye." Murmishi Mommy ta yi ta ce" Karki damu ki daukeni tamkar ni na haifeki duk abin da kukeso ki tambayeni zan yi muku shi matuƙar ina da shi." Jinjina kai Amra ta yi Auta ta iso ta jata suka shige aji.. Tun daga ranar alaƙar Amra da Auta ta ƙara ƙarfi dan har gidansu take zuwa tana wuni itama Auta taje nasu gidan, karatu kuwa ko basu duba ba in aka tamabayesu za su amsa daidai abin har ya bai wa yan ajin mamaki sosai duk abin da aka tamahayesu ko tangarda basa yi suke faɗa a daidai, wannan bawan Allah kuma kullum sai ya kira Auta amma bata dauka hakan ya sashi a damuwa har sai da aka yi katari ya gansu tare da Amra ya nemi ta shayo masa kan Auta ko za ta amince da soyayyar shi, amma data sameta da maganar cewa ta yi ita fa sai ta yi shekara 19 ko 20 za ta fara soyayya yanzu a 17 take ta yi ƙarama ta tsaya da namiji, sai da lallami da dubara Amra ta shayo kanta ta amshi soyayyar wannan bawan Allah mai suna Khamis... Tsaye suke a kusa da gurin shakatawa ita da Khamis tana kumbura baki shi kuma sai lallaminta yake, kallon shi ta yi ta ce" Ruwa nakeso kuma ka mayar dani gida nifa bana son yawo" Ta faɗa tana murguda masa baki." Murmishi ya yi cikin sauri ya miƙe ya ce mata yana zuwa yanzu zai kawo mata ice cream sai su koma gida, Ko ci kanka bata ce ba ta juya baya tana jan tsakin an takura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31