Chapter 21
Chapter 21
a duba mini abinci yunwa nakeji banci komai ba yau ko ɗaya" Ta faɗa tana cuno baki." A fusace Fadila ta juyo ta dungure mata kai ta ce" To fitinanniya kin iso gidan ai kuma shi kenan ba dama mutum ya huta sai kin dameshi da yunwa kike ji, anya ma kuwa ke a cikinki kike zuba abincin? To ba zan iya wannan masifar taki ba ki wuce ki bani guri ko in lallasaki yanzu." "Mufy ta harari Auta ta ce" Ki fice mana a nan mai ɓakar zuciya anyo gadon Mommy banza, in kinga dama kije ki zuba abincin gashi can akan darning, idan kuma ba ki ga dama ba ki yi ta zama da yunwa karki kuskure mu yi baƙi ki iso inda muke ko ki faɗa mana maganar banza." Saɓa baki Auta ta yi tana shirin yin kuka Fadila ta yi saurin hankadata gaba ta faɗi tim ta shiga zaginta har da jan mata kunne sai da taji ta kwalla ihun azaba kana ta sake mata kunne, hannunta ta kama tana janta kiiii ta kawota kan darning ɗin ta damƙi wuyan rigarta ta ce" Tashi dan uwarki ga abincin nan, idan na sake ganin walkiyarki a palon nan sai na kakkarya miki ƙafafu ya" Tana gama faɗa ta saketa ta dawo inda Mufy ke tsaye tana yiwa Auta dariya har tana cewa Fadila ta zane Auta.. Haushi da ɓakin ciki suka rufe Auta ta fashe da kuka ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta, tana zuwa ta faɗa kan gado ta dinga kuka tana kiran sunan Mommy... ________________________ Yana zau ne kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye ya nufi gindin wata doguwar bishiya, kamar biri nan da nan ya haye samar bishiyar ya samu guri ya zau na yana sakin murmishi, a hankali ya ce" Afra na na yi kewarki a ina kike? "Ya ƙarashe maganar yana shafa hannun shi sai gata ta bayyana a kan gado tana bacci, tsayawa ya yi da kyar yana kallon fuskar tata yaga hawaye kwance akan kuncinta har sun bushe, hankalin shi ne ya yi matuƙar tashi ya yi saurin rufe idanun shi yana faɗin" Abar ƙauna wani mai tsautsayi ne ya sa tsadaddan hawayenki ya zubo daga cikin idanunki? Ko ma waye zai karɓi hukuncin daga masoyiki Bobby. Buɗe idanun shi ya yi ya wura iska a jikin rishen bishiyar, abubuwa da ya faru a gidan tun daga shigowarta har kukanta duk ya gani, Jinjina kai kawai ya yi ranshi na ƙara tafasa ya ɓace a kan bishiyar. A cikin wani ɗaki mai kama da faɗa ya bayyana a bakin gado ya zau na yana huce ya ce" Namir ko mai kake ka aje ka iso ina neman ka." Yana rufe baki wani haske ya haska ɗakin, zuwa can sai ga wani haɗaddan saurayi matashi mai fasalin larabawa ya yi tsaye a gaban shi, cike da girmamawa ya ce" Yaya gani da fatan dai ba wani abu bane yake faruwa ko?" "Mene ne ma bai faru ba Namir so nake duk wanda ya taɓa mini matata a masa yadda ba za moru ba, wai yau aka samu wanda ya dakar mini ita ya kuma sakata kuka da hawaye, na yi ƙoƙarin mu haɗu a baccinta amma naga bata cikin shauƙin da za mu iya haɗuwa, ni kuma yau ina buƙatarta a tare dani ina so mu kwanta a gadon nan nida matata bana so ko kuɗa ya taɓa mini ita bare mutum irinta, inaso ka yi duk abin da ya dace akan su ni zan lallaɓa Afra na shayo kanta bana son ganin ɓacin ranta ko da na minti ɗaya ne, kasan dai yadda nake ƙaunarta ba zan bar wani ya ɓat mata rai ba na barshi shi yana walwala a duniyar nan, kaje ka gargade su kara musu kunne ni in naje mai gaba ɗaya zan musu shi ya sa bana zuwa sai dai na tura ka" Ya ƙarashe maganar yana fesar da iska daga bakinsa.." "An gama Yaya ka kwantar da hankalinka zan yi komai yadda ya dace, dama kasan dai makiyanmu ne wannan ahalin gidan ai , ina fa tunanin lokacin bayyanarmu ya yi wa ahalin gidan nan.. "Haka ne amma ba ko da wasa kar a taɓa mini matata, zan ɗauketa na kaita kullacaccen gidana inda za ta samu farinciki.. Jinjina kai kawai ya yi ya ɓace a ɗakin.... _________________________ Mijin Hafsat yaga shuru-shuru har la'asar ta yi amma bata dawo ba sai mamaki ya kama shi , kiran wayarta ya yi ringing biyu uku ta ɗauki kiran, a masifance ya ce" Ke dan tsabar kin raina mini hankali ki tafi gantalinki har Yamma ba ki dawo ba, yo ko gidanku ki ka wuce ai kin mini text ki faɗa mini, amma da yake ba a miki tarbiya a gudanku ba kin kwashi ƙafa kina gararanba a gari, dan kina kawai dao ki wulaƙantani ace bana baki abinci ko bana kula dake to ba zai yiyuba ba ki maza ki dawo ko ma ina ki ka tafi, kayana gasu nan ba ki wanke su ba ki ka tafi wani dan iskan ne zai wanke mini da ki ka bar mini su a zube kamar ba ki darajar tufafiba? Ki fita idona na rufe Hafsat, ko da yake dama ku 'yan zaɓin iyayen nan haka kuke da raina miji ya yi magana ku kai ƙaran shi wajan iyayensa ƙara." Haka ya dinga masifa ta inda ya shiga ba ta dan yake fita ba.. Hafsat ta kalli Jaririyarta dake gabanta tana nono, wani ɓakin ciki ne ya rufe ta ta cire jaririyar daga shayarwar da take mata, gyara wayar ta yi ta ce" Maigida yanzu ni kake faɗawa wannan maganar? Ko da yake ai dama ka saba kai ko tausayina baka yi ga tsohon ciki ga aikin gidan har ma da wankin ka to ba zan yi ba, ji nake kiranka aka dinga yi kaƙi ɗauka daga karshe ma ka yiwa wadda ta kiraka rashin mutumci a lokacin da nake tsakanin rayuwa da mutuwa, idan kaga dama ka zo gidanmu na haihu ga ƴarka nan akan cinyata." Zaro idanu ya yi sai kuma ta miƙe tsaye ya ce" Kuturu! To Alkur'an sai dai Baba ya yankawa ƴarki ragon suna ba dai ni ba, ni nace ki yi cikin ko nj nace ki haihu a wannan lokacin da bani da kuɗi sosai a hannuna, mata turo mini photo Yarinya na gani in bata yi kama dani ba kema kin san sauran bayanin, in ban da ke raguwa ce tashin farko ma ki haifo mini mace dan ki cika mini gida da haihuwar ɗiya mata, ba ba zai yiyuba daga wannan karki sake haifo mini mace duka maza nake so ƴar rainin hankali, na dai kusa yin aure na aure yar charas." Murmushi mai ciwo Hafsat ta yi tana jinjina rashin mutumci irin na mijin nata, ta ce" Maigida kenan ai bani na bawa kaina haihuwar ba in kuma kasan kasuwar da ake sayo ɗa namiji kaje ka sayo namijin sai na bayar da wannan ɗin kyauta, kana musulmi amma ya shigo Muslimci yau ya fika sanin komai daga Allah ne, yanzu kai ko kunya kaba ji ba? Allah ya maka kyauta amma ka raina saboda mutulci irin na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31