Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sanar da ita yadda suka yi sosai hankalin Mommy ya tashi suka nufi ɗakin su duka, duk wanda yaga Khamis a wannan lokacin saiya zubar masa da hawaye ko ina na jikinsa an nade da bandeji hancinta an saka masa abin ƙarin numfashi, sai Yamma likis kana Mommy taja Auta shi ma da ƙyar ta yarda tabi Mommy gani take inta tafi za a kirata ace mata ya rasu haka dai suka tafi tana sharar hawayen tausayin masoyin nata.. _____ Ko da suka je gida ɗakinta ta nufa ta faɗa kan gado ta ci gaba da kuka zuciya na mata zafi da raɗaɗin ganinsa a wannan yanayin, bata taɓa jin ƙaunar Khamis ba irin ta yau ji take kamar ta koma Asibitin ta ƙara ganinsa ajiyar zuciya ta sauke ta tashi zau ne tare da zama a tsakiyar gado, can ta miƙe ta lalibo wayarta ta shiga duba number da Amra ta bata ta danna kira har ta yi ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira nan ma haka, sake kira ta yi a karo na uku tana ringing har ta cire rai za a ɗauka sai ance hello. Baki na rawa ta ce" Amra kina jina?" "E ina jinki lafiya dai naji muryarki a haka?" Kuka ta sa mata ta shiga bata labarin abin da ya faru, salati Amra ke yi daga cikin wayar itama na tayata kukan ta ce mata gobe su haɗu za ta zo taga jikin nasa haka dai ta yi ta kwantar mata da hankali sai da ta tabbatar ta daina kukan kana suka yi sallama. Idanunta ne suka soma rufewa hakan ya sa ta jefar da wayar ta koma ta faɗa kan gadon tare da lumshe idanunta. "Afra! Taji an kira sunanta a saitin kunnenta hakan yasa ta ɗan buɗe cikinta ne ya soma murda mata ta sa hannu ta riƙe cikin, wasa wasa ciwon cikin ta dinga karuwa tun tana kan gado har bata san lokacin data faɗo daga gadon ba tana murkususu tare da yin salati, tun daga ɓakin gado take birgima har takai jikin ƙofar ɗakin tana juyi tana wash cikinta haka ta dinga birgima a tsakar ɗakin har wani wahalallan bacci ta yi gaba ita.. Zau ne yake a jikin wata bishiya cikin shiga ta alfarma gefensa tana zau ne ta kauda kanta gefe, juyo da fuskarta ya yi cikin kulawa ya ce" Afra na wai duk fushin ne haka?" Bata yarda ta haɗa idanu da shi ba hakan ya tabbatar masa bata huce ba, shu'umin murmushi ya yi tare ta hura mata iska a gefen wuyanta . Da sauri ta juyo tana saɓa baki kamar mai shirin yin kuka ta ce" Bobby! Ɗan murmishi ya saki kana ya ce" Afra na kwana biyu ban ganki ba ke ko kewata ma ba ki yi ba ma." "Na yi mana Bobby" Ta bashi amsa tana shafa cikinta tare da ɗauko hannunsa ta ɗaura akan cikin nata tana murmishi. "Tashi muje mu kaɗai ake jira kowa ya hallara" Ya ƙarashe maganar yana miƙar da ita. Cike da farin ciki take binsa har suka isa ɓakin ƙofar wani ɗaki ƙarami ƙofar ɗakin bata fi yaro dan shekara biyar ya wuce ba, hakan yasa ta kallesa za ta yi magana ya ɗaura mata hannu a bakinta ta yi shuru ya kama hannunta suka kutsa kai ta ƙofar, kamar kiftawa da bismillah ta taga sun wuce ta ƙofar sai gasu a wani tamfatsetsan ɗaki. Baki da hanci t saki tana kallon gurin taga dai ba kowa hakan yasa ta ce" Bobby ka ce mu ake jira kuma naga bà kowa ina suke masu jiran namu? Hannu ya kai ya rufe mata idanu ta yi murmishi kawai bata ce komai ba, wani haske ne ya fito daga idanunsa ya zagaye suka wajan sai wasu dabbobi sun bayyana cike da gurin, duk dabbar da ya kalla sai ta rikide ta dawo suffar mutum. Buɗe mata idanun ya yi ta kalli gurin taga ya cika taf kowa ita yake kallo, baƙi ɗaga za ta yi magana taji an yi sama da ita da ƙarfi ta ce" A a Bobbyyyy! A firgice ta farka tana salati jikinta sai rawa yake, al'ajabi da tsoro sun hanata motsawa zuciyarta na bugawa da ƙarfi sai zufa ke karyo mata ta ko'ina ta sauke ajiyar zuciya kana ta yi ta maza ta miƙe da ƙyar tana riƙe bayanta dake mata ciwo, cike da mamakin mafarkin nata ta ce" To shi wannan kuma waye shi? Kuma a ina zan ganshi a zahiri da nake mafarkin tsayin shekaru huɗu, da sauri ta miƙe ta kalli agogon ɗakinta taga ƙarfe 7:30pm salati take tana ambaton kalmar Astagafurullah ganin lokaci ya tafi bata yi sallar Magariba, jikin bango ta dinga bi har ta shiga banɗakin.... _________________________ Amra na zau ne tun da ta gama magana da Auta take nazarin maganarta Aliyu dake kusa da ita ya ce" Yaya Amra nifa na gaji da dakatar damu da kike yi akan ahalin yarinyar nan gaskiya, Yaya Amina za ta iso na jiyo ƙamshinta yau ɗin nan za mu yi duk abin da ya kamata sannan maganar mai bibiyar rayuwarta ina iya bakin ƙoƙarina amma har yau na kasa gano shi, tabbas wannan ko a ina yake mugun shu'umi ne na gasken gaske ace duk ƙarfinki ki ka kasa gano shi to taya ma ni zan gano shi yanzu d... "Ya isa Haidar! Ta faɗa da ƙarfi cikin irin wata murya dake nuna ranta yakai mataki na ƙarshe a ɓaci, tuni idanunta suka canja kala cikin wata irin murya ta ce" Zaki ka daina tunanin na hanaka yi wannan abun ina son ne na gano wanda yake tare da ita daga baya sai mu cika alƙawarin da muka ɗaukarwa iyayenmu." "Haba Yaya Amra taya za ki ce wai sai kin gano kana za mu cika alƙawarin da muka daukarwa iyayenmu shekaru da dama? Nidai in za kibi magana kawai mu fara cika da alƙawarin da muka ɗauka inyaso daga baya komai ba sai ayi, ko kin manta yadda girman alƙawari yake ne? " A a Zaki ban manta ba amma ku mini uziri ina so mu taimaki wadda ta nuna tausayawarta a garemu duk da bata san mu ko su waye ba, mu taimaki rayuwarta mu rabata da wannan ɓakin azzalumin da yake tare da ita." Aliyu ya koma suffar Zaki ya yi kururuwa ya yi wata irin sufa ya nufi kan Amra,ita kuwa ta tsaya tana kallonsa har yazo kusa da ita sai kuma ya yi baya ya kuma yin kukan Zakuna kana ya koma gefe yana huci, Amra ta matso kusa dashi ta sunkuya cikin tausasa murya ta ce" Zaki kada ka yi fushi da Amrar ka ka mini uziri ni ban halaka yin abin da kake so ba, idan za ku iya aiwatar da komai ba tare dani ba to ku yi har lokacin da zan gama bincikena na dawo cikinku ka yi haƙuri ɗan'uwana" Ta faɗa tana shafa kan shi." Sunkuya da kai Zaki ya yi hakan ya sa Amra ta fahimci ya ji maganarta ta miƙe ta fice a ɗakin.. _________________________ Hon yake ba kakkautawa kamar wanda ake neman rayuwar shi, a guje Maigadi ya fito daga banɗaki ya iso ya buɗe masa ƙofar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});