Chapter 20
Chapter 20
mayar da numfashi, kallonsu ta yi sai kuma ta cuno baki ta ce" To ina ruwan yake?" Miƙa mata ya yi ta amsa ta sha, bayan ta gama ta yi hamdala kana ta juyo ga Amra da take kallon ɗakin da matar da take.. Suna nan gefe sai aka buɗe ƙofar, Doctor ta fito riƙe da jaririya ta nufosu Amra ta yi saurin tashi ta amshi yarinyar tana murna, itama Auta murna ta shiga suna hamdala. Amra ta ce" Likita ya jikin nata?" "Lafiya lau take babu komai sai dai rashin kwarin jiki za ma ku iya ganinta ai." Godiya suka mata kana suka shiga ɗakin suka sameta kwance tana kallon gefe, zama Amra ta yi riƙe da jaririyar ta ce" Anty kinga ƴarki mai kyau." Murmishi ta yi tana taɓa jaririyar, "Yawwa Anty mijinki dai ya ki ɗaukan kira na kira yafi sau 20 bai ɗauka ba, yanzu ki mana kwatancen inda gidanki yake sai mu tafi mu kaiki gidan naki ko gidanku." Goge hawaye matar ta yi ta ce" Dama ba lalle ba ne ya ɗauki kiran tun da kin kira da farko ya dauka yana masifa, kawai gidanmu zan tafi na gaji da cin mutuncin da yake mini a zamana dashi." Ajiyar zuciya Amra ta sauke ta ce" Ba komai Anty ya sunanki to?" "Sunana Hafsat. "To Anty ina ne Unguwar taku? "A ƙofar Soro ne gidanmu. Jinjina kai Amra ta yi sai kuma ta ce" Wannan shi ne ya biya kuɗin da aka sa miki jini"Ta faɗa tana nuna shi ya yi tsaye bakin ƙofa." Godiya ta shiga masa har da hawayenta ya ce ba komai in an sallame su shi zai kaisu gida, Amra ta masa godiya sai ga Doctor ya shigo ya miƙawa wannan mutumin takarda ya ce" Idan kum fita ku bi hanyar hagu sai zai kaiku wani ɗaki anan za a baku magani Allah ya raya baby" Ya faɗa yana barin ɗakin tare ta jadadda musu da ruwan ya kare a kira shi ya cire sai su tafi.. Sai kusan ƙarfe 11 kana aka sallame su suka tafo zuwa gidan su Hafsat.. Suna zuwa gidan suka shiga Maman Hafsat ta tarbesu da Ƙanwarta, sai da suka zau na kana Amra ta musu bayanin komai, godiya Maman Hafsat ta yiwa su Amra ta sanya hijabi ta fito waje ta yiwa mutumin nan godiya tana saka masa albarka, shi kuma yana amsawa da amin kana ta juyo sai ga su Amra sun fito suka mata sallama.. "Haba yaran nan ya za ku tafi yanzu kuma ku zauna mana a jima. "A a Mama za mu wuce za mu dawo ko gobe ne mu ga Babyn" Cewar Amra tana shigar da Auta cikin motar, shiga itama ta yi suka bar ƙofar gidan Maman Hafsat na ɗaga musu hannu.. Daidai inda suka ɗauki matar nan ya aje su, godiya sosai suka masa ya buƙaci Auta ta basa number ta, ai kuwa ta kafe ta ce ita fa bata kula maza shekararta 14 fa ,da ƙyar Amra ta lallaɓa ta ta bashi number kana suka ya tafi.. Dariya Amra ta yi ganin yadda Auta ta yi kicinkicin da fuska, kamo hannunta ta yi ta ce" Ƙawata wai fushin nan dan kin bada number ki ne? To meye ƙila ma ba sonki yake ba sai kawai musha biki ba nan da wasu shekarun." "Nidai bana soyayya Mommy ta ce inyi karatuna kar na kula maza wasu yaudara garesu.. To naji yanzu dai kin yi latti zuwa makaranta kira Direba ya mayar dake gida.. To ta ce tana kumbura baki ta kira shi, suna zau ne a gindin wata bishiya sai gashi ya iso, sallama ta yiwa Amra ta shiga mota sai gida... Amra na ganin sun wuce ta ɓace a wajan, bata bayyana a ko'ina ba sai a cikin wani daji mai bishiyoyi dayawa baka jin komai sai kukan tsintsaye da kukan kuraye da Zakuna, za ma ta yi akan bishiyar can sama ta ce" Aliyu kana ina wai?" Wata guguwa ce ta karaɗe gindin bishiyar, Amra ta yi murmishi kawai har sai da guguwar ta lafa kana ya bayyana sanye da kayan yaƙi a jikinsa, gyara zama ya yi ya ce" Yaya Amra wai lafiya kike ta kwada mini kira? Kin san fa naje farauta ne haka na bari ganin kiran ya yi yawa me yake faruwa ne?" Ajiyar zuciya Amra ta sauke kana ta dubi Aliyu ta ce" Zaki akwai matsala babba." "Subhanallah! To me yake shirin faruwa ne? Ki faɗa mini ko akwai ta yadda zamu samu mafita." "Zaki akwai wani a jikin Auta kuma ya daura soyayya da ita har ma yana mata maganar aure, na duba na kasa ganin fuskarsa sai dai kawai naga fuskar ta yi baƙi, bana so ya cutar da ita dan da alama bashi fa imani ya san tsakanin mutum da aljani babu soyayyar aure amma me ya sa ya canja ta? Zaki ya za mu shayo kan matsalar nan don Allah? Na yi iyakar dubana na kasa ganeshi bana ganin komai Aliyu ka yi wani mu gani mana" Ta ƙarashe maganar idanunta na canjawa." Hannayenta Aliyu ya riƙe cikin kwantar da hankali ya ce" Yaya Amra ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru da Ƙawarki in sha Allahu, bari na duba na gani ko ni zan ganshi, amma kuma Yaya Amra kema da kika fini ƙarfi ta ko wani ɓangare ba ki gani ba bare ni da ko rabin ƙarfinki ban kai, amma dai bari na duba sai muga abin da zamu iya akai." "Ka taimaka ai ba sai lalle sai ka kaini ƙarfi ba za yi abin da ni na ƙasa abin daga Allah ne ka taimaka nidai.. Jinjina kai Aliyu ya yi kana ya rufe idanun shi, can ya ce" Yaya Amra na ga ƙafarshi ki duba ƙila kema ki gani." Da sauri ta rufe idanunta Aliyu ya ce" Kama hannuna za ki iya gani ta hakan." To kawai ta ce ta riƙe hannun shi, ƙafar tasa ta gani a nade irin ta harde su ya zau na ƙafar tana sanye da takalmi, ran Amra ya kuma ɓaci ta ce" Aliyu tabbas ko ma waye wannan ya shamceni kuma ko a ina yake saina binciko shi in sha Allah" Ta ƙarashe maganar tana buɗe idanunta." "Yaya Amra karki damu za mu gano shi amma tabbas yana matuƙar sonta sosai kin gani kalli nan" Ya faɗa yana shafa hannun shi ya ɗan miƙa mata. Amra ta gani tana cikin nishaɗi tana jikin wata fulawa sai shinshinawa take tana sakin murmishi , Jinjina kai ta yi ta ce" Mu koma gida so nake Amina ta iso mu ko ita za ta samo mana shi tun da ta fimu shiga duniya." To kawai ya ce suka ɓaci daga kan bishiya , basu bayyana a ko'ina ba sai a jikin wani dutse mai girman gaske suka shige ciki.... _________________________ Auta na zuwa gida ta samu Fadila tare da ƙawayenta suna ta gyare-gyare a falo, isowa ta yi gurinsu tana kallon yadda aka shirya kayan da za ayi shagali ga balon-balon nan kala kala an saka su a jikin bango abin sai ya birge Auta ta saki murmushi tana lumshe idanu , kallon Fadila ta yi ta ce" Anty
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31