Chapter 24
Chapter 24
ɓangaren." Da sauri Mufy ta kalli Auta sai kuma ta janye idanunta ta mayar kan TV tana jinjina irin dukan da za ta yiwa Auta in ta samu dama. Daddy ya yi shuru yana nazarin kalaman Auta kana ya ce" OK no problem my dear zan ƙara mata dan farincikin ki." Fadila ta shiga hura hanci ta zabure kamar ƙiftawa da bismillah sai gata a gaban Daddy ta shagwaɓe tare da cewa" Daddy a canza mini mota gaskiya tawa ta samu matsala jiya ma a tsakiyar titi ta lalace, ni a matsayina na ɗiyarka bai kamata ace ina hawa keke napep ba, abin kunya ne ma aga wanda ya fito daga cikin gidan nan ya hau napep." "Karki damu zan saya miki ku je ku huta brothers ɗin ku kusa shigowa. Tsalle ta yi tare da sumbatar Daddy ta koma ta zau na bata ce da friend ɗin nata ba su tafi part ɗinta ba .. Wani horro film aka kawo a tashar da suke kallo abin da Auta take matuƙar so kenan dan haka ta mayar da hankalinta kacokam akan TV tana murna, Mommy ta koma gefe ta zau na tana harara su Mufy su kuma suna mata kallon uku saura kwata... Hon suka ji Daddy ya ce" Yawwa ga ma su nan sun iso." Da ihun kiran Mommy da Daddy Sudas da Sauban suka kutso kai cikin palon ba sallama, fito Sudas ya dinga yi ya nufo Mommy, shi kuwa Sauban kamar yadda ya saba eapis ɗinsa a kunne yana bibiyar wakar da yake sauraro,Mommy ta rafka tagumi tana addu'a a zuciyarta har Sudas ya iso gabanta ya kama hannayenta ya mata kiss tare da cewa" Mommy missing you so much. " Harara ta watsa masa sai kuma ta yi murmishi kana ta ce" Welcome back my Son's ya aikin?" Am fine Mommy how are you today? Lafiya ta amsa masa a takaice dan ita ta tsani wannan kwarmaton na dole su sai dai su ma turanci ba za su maka Hausa ba a matsayinsu na 'ya'yan Hausawa, sai dai kawai turanci kamar daga England aka yo ruwan tsirar su... Bayan an gama murna Kande ta zo ta gyara gurin suka koma kan kujera, tana gamawa ta kawo abinci suka ci ta kwashe komai.. Kowa harkar gabansa yake Daddy na can gefe yana duba wasu takardu, Auta na a gefen shi tana wasa da yar Teddynta tana mata surutu, Mommy na can ɗayan gefen tana kallon wani hira da ake da Malamin addini a BBC a cikin wayarta, Fadila da ƙawayenta tare da yayunta Sudas da Sauban na kallo... Ɗagowa Daddy ya yi cikin farinciki ya kalli Mommy ya ce" Darling na kara samun riba a company na har ta miliyan goma cikin wata biyar, Auta maza tashi ki ɗauko mini barrow zan rubutawa Kande cak ɗin da kuma naku lis ɗin." Da murna Auta ta miƙe ta nufi ta gaban su Fadila tana cewa" Daddy zan rakaka Dubai sai kawai taji ta yi baya ta faɗi tim.. Bata yi kuka ba ta ɗago kai ta kalli Fadila da take aiko mata da harara, hmm kawai ta faɗa ta wuce ranta a matuƙar ɓace... Tana tunkaro ɗakin taga kamar an wuce ta gabanta, dariya ta yi kawai ta nufo cikin ɗakin Daddy. Mamaki ne ya kama ta ganin duhu ba alamar haske, bata kawo komai a ranta ba ta miƙa hannu da niyar haska wutar ɗakin. Tun kafin ta kai hannu ɗakin ya gauraye da haske, murmishi ta saki ta nufi inda Daddy yake aje barrow ta ɗauko ɗaya ta juyo idanunta suka kai kan ɗayar ƴar Teddyn ta a kan gadon Daddy.. Ɗaukan Teddy ta yi tana cewa" Baby ashe a nan na barki?" Hasken ɗakin ne ya ragu tare da sautin kuka da muryar yara, dariya Auta ta yi ta ce" Ni ce na aje ki?" Ji ta yi kawai an ce" E". Auta ta miƙe da sauti tana dariya ta ce" Yawwa to yi haƙuri yau zan goyaki a bayana" Ta faɗa tana ɗaukan Teddyn ta wuce zuwa palo. Shuu ta ji wucewar wani abu ta bayanta ta yi saurin juyawa sai taga ba kowa, wucewarta ta yi tana shilla ƴar Teddy har ta sauko ƙasa ta miƙawa Daddy barrow ta zau na.. "Auta ke daga aikin ki sai ki shantake" Cewar Daddy yana ci gaba da rubutunsa." "Daddy ƴar Teddyna na ɗauko har ma ta yi fushi dani tun ɗazu take kuka" Ta faɗa tana rungume Teddy.. Murmishi Mommy ta yi haka ma Daddy... Sudas ne ya juyo zai yiwa Daddy magana, idanunsa ne ya sauka akan Teddy Auta. Gani ya yi tana zaro masa idanu fuskarta ɗauke da ɓacin rai. Waiyo Daddy tana hararata" Ya faɗa yana maƙalewa a jikin Sauban. . Dariya suka kwasa sai wutar palon ta dauke dif, kowa ya shiga zare idanu. Palon ne ya ɗauki wata irin girgiza tuni kowa ya rungume na kusa tashi duk suka cika palon da ihu, Mommy ta soma addu'a aka yi sama da ita shuu sai gata a ɗakinta aka kullo mata ƙofar.. Auta ta miƙe tana laliban Mommy tana tafiya a duhu sai ta isa gurin su Sudas ta shafa bayan shi cikin wata irin murya ta kwashe da dariya wadda palon gaba ɗaya ya dauki sautin ta.. Futsari Sudas ya saki yana karkarwa take ya maƙale Sauban, ita kuwa Auta dena dariyar ta yi ta dinga tafiya da lalibe har ta iso kusan su Fadila ta soma shafata. "Waiyo! Fatalwa Daddy kana ina Mo. Bata ƙarasa ba aka yi sama ta isa aka buga a kan kujera ta Ƙwalla ihu, tare da sakin zawo saboda tsananin tsoro. Wani irin kuka-kuka aka dauka kamar na Doki kamar na Jaki hakan ya sa suka karade palon da ihu suna ƙara mannewa da kujera kamar za su shige cikinta.. Wani haske ne ya bayyana a sama duk suka ɗago kai a tunanin su wutar ce ta dawo sai suka yi arba da wani narkaken halitta mai suffar mutane ƙafafuwan shi na Doki hannayen shi irin na biri, fuskar shi ba kyaun gani haƙoransa na gaba manya guda biyu, idanunsa jajaye manya-manya har wani tartsatsin wuta yake.. Sudas ya buga ihu yana cewa" Ihu jama'a ku kawo ɗauki fatalwa a g. Bai ƙarasa ba aka wanka masa mari ya sume a jikin Sauban, shi kansa Sauban ɗin futsari ya saki ya yi sharkaf da futsari haɗi da zufa... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [09/12, 00:13] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣1️⃣ "Waiyo Daddy ka taimakeni bayana ciwo yake" Cewar Fadila tana ƙara maƙalewa kujera jikinta na rawa karr³ . Kiyat! Suka ji ƙaran yanka wani abu kamar an yanka zani da ƙarfi, ihun Mufy suka jiyo tana faɗin ta mutu ta lalace a taimaka mata.. Fadila dake gefenta ta soma ja da baya jin wani abu na bin mata hannu, zabura ta yi cikin tsananin firgici da nufin ta sauka akan kujerar. Tinjum! Suka kuma jiyowa kamar an saka wani abu a cikin rijiya mai ruwa sosai.. "Daddy! Daddy ka taimakeni Waiyo ana jana Daddy za su tafi dani ku taimakeni"Fadila ta faɗa a tsorace jinta a cikin ruwa tsundum sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31