Chapter 19
Chapter 19
ta ce suka shiga mai motar yaja suka bar gurin... "Tun suka kama hanya Amra ke jan tsaki tana jinjina kai, lumshe idanu ta yi ta ce" Zaki kana ina ne?" Shuru ta yi da wani lokacin ta saki murmushi kana ta buɗe idanunta a lokacin sun iso Asibitin. A hanzarce aka shiga da matar suka tsaya a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da ita, Amra nata zarya tana hura hanci idanunta sun yi jajur saboda ɓacin rai sosai kalaman mijin matar nan yake mata yawo a rai... Bala mai shayi yau da ƙyar ya iso gurin sana'arsa, sai da ya buɗe komai ya ya zau na ana ciniki ana ta tambayarsa mene ne ya samu bakin shi haka? "Ai jiya nake baku labari Garbati aljannu na gani a gindin b... Bai ƙarasa maganar ba ya yi arba da wani ƙatoton maciji ya tashi koshi a gefen shi, zabura Bala ya yi yayi sama sai gashi akan cinyar Garbati. "Waiyo gasu nan sun sake dawowa ku taimaka Garbati" Ya faɗa yana ƙara maƙalewa a jikin Garbati.. "Kai dalla Malam ka ɗagani" Cewar Garbati yana rintse idanu.. Bala juyo dan ya gani macijin nan yana nan ko kuwa ai kuwa ya yi arba da macijin yanzu sun zama biyu ma, suna haɗa idanu suka yo kanshi, ihu yasa ya yi wata irin sufa ya watsa da gudu a 380 ya hau hanya a guje.... Amra tsaye taga Auta ta yi bacci, zama ta yi a gefenta tana tarota dan kar ta faɗi ji ta yi saitin zuciyarta na bugawa sai murmushi take saki kuma baccin take. Idanu ta rufe ta dafa saitin zuciyar Auta, zuwa can ta yi saurin buɗe a zabura ta miƙe ta ce" Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Auta k..... _*Yau dai na yi muku dayawa ina bukatar comment da sharhi, in ku ka yi haka zan ke muku 2 fage a rana inhar kun bani haɗin kai ta hanyar comment da sharhi*_ _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [05/12, 14:39] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *Much love ƙauna masoya ina alfahari daku🫶🏻🫶🏻😘* *بسم الله الرحمن الرحيم* 0️⃣9️⃣ Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Auta k. Bata ƙarasa maganar ba sakamakon jin sautin muryar Doctor da ya fito yana mata magana ta yi saurin juyowa hankalinta a tashe ta ce" M.. Me ka ce Likita?" Murmishi ya sakar mata tare da gyara tsayuwar shi ya ce" Yarinya Antyn naku fa bata da jini sai kun saya ko kuma ku samo wanda za a ɗauka a jikinsa." Ya rabbi! Amra ta faɗa tana miƙewa tsaye, hannu biyu ta haɗe sai ga hawaye sharr³ ta ce" Likita ka taimakemu asa mata jinin nan na maka alƙawari in sha Allah zan kawo maka kuɗinka, mijin nata ne baya kusa ban san a ina zan samu kuɗin nan ba a yanzu ni ba ƴar garin nan ba ce ka taimaka kar ta rasa ranta ka dubi girman Allah ku saka mata jinin nan" Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye." Ke yarinya karki raina mini hankali mana, taya ina miki maganar ki bada kuɗi kina maganar ba ki da kuɗi in ba za ki nemo ba ki bari Antyn naki ta rasu ku kuka yi asara bani ba kin gane? Numfashi ta fesar ranta ta kai matakin ƙarshe a ɓaci, idanunta suka yi jajur tana zubar da hawaye lumshe idanu ta yi ta soma magana a cikin zuciyarta. "Ya rabbi! Ubangiji ka sassautawa wannan baiwar taka ta haihu lafiya, Allah ya sayayya mini zuciyata kar na nunawa yaron nan fushina, Aliyu kana ina ne? Ka zo yanzu ina son ganinka. Buɗe idanunta ta yi ta durƙusa a gabansa ta ce" Don Allah ka taimaki Antyna kar ta rasa ranta kaji." "Tsuwww aikin banza kuma ai sai ki yi kinga ma tafiya ta ta mutu ma babu ruwana, ni za ki rainawa hankali har da wani kuka na iskanci? To ba zan taimaka ɗin ba" Ya ƙarashe maganar yana juyawa zai koma ɗakin.. "Nawa ne kuɗin? Kamar daga sama Amra taji murya mutumin. Dawowa Doctor ya yi yana dage hanci sai da ya sha ƙamshi kana ya ce" Dubu hamsin za ku biya har kuɗin maganinta bana ma tunanin za ta iya haihuwa da kanta, kawai abu mafi sauƙi ku biya 100k sai a mata aikin." Murmishi ya yi ya zaro 'yan rafa ɗaurin dubu dari ya miƙawa Doctor ya ce" Gashi a hanzarta a mata aikin, inma yafi haka zan biya ma matsala ba ne." Da sauri Doctor ya warci kuɗin a hannun shi yana washe baki ya ce" To ranka ya daɗe yanzu kuwa bari na wuce" Ya faɗa yana ficewa.. Jinjina kai Amra ta yi ta juyo ta kalli mutumci tana goge hawaye ta ce" Yaya na gode Allah ya saka da alkhairi ashe za mu sake haɗuwa?" Murmishin dai ya mata ya dawo ɗaya daga cikin kujerun ya zau na ya ce" Ai dama na ce miki za mu sake haɗuwa dake ya jikin Inna?" Itama murmishin ta yi ta zau na a kusa da Auta tare da ɗaura kanta akan cinyarta ta ce" Inna ta samu lafiya sosai gaskiya naji daɗi matuƙa ka zo a lokacin da nake buƙatar taimakonka, Allah ya saka da alkhairi bani da bakin maka gidoya kai ɗin mutumcin kirki ne." Jinjina kai kawai ya yi sai yakai kallon shi kan Auta dake ƙoƙarin tashi, zuba mata idanu ya yi har ta buɗe idanunta tana kallon Auta sai kuma ta miƙe zaune. "Amra ta haihu ne wai?" Kallonta kawai Amra ta yi ranta na tafasa ta rasa dawa za ta yi magana akan abin da ta gani a jikin Auta, "Amra lafiya dai kike kallona haka?" "Ihum ba komai Auta naji kamar zazzaɓi ne a jikin naki ko? Cuno baki ta yi tana murza idanu ta ce" Amra yunwa nake ji ki bani abinci naci." Idanun Amra ne ya ciko da ruwan hawaye ta yi saurin mayarwa ta kama hannayenta ta ce" To Auta a ina zan samu abinci a Asibitin nan? Ki daure a jima Aliyu zai zo mana da abinci." Auta ta faɗa jikin Amra ta fashe da kuka tana a bata abinci ta ci, dan yadda take jin yunwar nan in har aka jima sai dai a ɗauki gawarta. Murmishi ya yi ya ce" Sorry sister bari nasa a kawo miki abincin dena kukan kinji." Ɗagowa ta yi tana kaon shi baki ta murguda masa ta kalli Amra ta ce" Wannan fa?" "Shi ya biya kudin da za a saka mata jini, dama na taɓa ganin shi kuma ya taimakeni.. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" To mun gode ka kawo mini abincin naci yunwa nake ji sosai." Waya ya yi ya ce a kawo abinci inda yake kana ya kashe kiran.. Suna nan zaune sai ga wani ma'aikacin restaurant ya kawo abincin, godiya ya masa tare da bashi kuɗin ya tafi, yana miƙa mata ta yi saurin karɓa ta gyara zama ta soma cin abincin da sauri-sauri. Yadda take cin abincin sai ya birge shi ya yi tagumi yana kallonta har lumshe idanu take. Amra ma kallonta ta yi tana jinjina kai har ta ci ta ƙoshi ta bar sauran ɗan kaɗan tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31