Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Daddy ya ɗauke cak ya sata a cikin mota yana ta masifa. Da sauri Auta ta buɗe schoolbag ɗinta ta fito da biskota gida uku da kuɗi ta dubi Daddy ta ce" To ka bari na bata wannan tun da ba za ka taimaketa ba." Dafe kai Daddy ya yi bai kuma ce mata komai, ganin haka ya sa Auta ta balle murfin motar ta fito da gudu-gudu ta iso inda ta bar Amra zuwa lokacin ta tashi tana kusa da Mamanta tana rusar kuka. "Amra! Ta kira sunanta da ɗan ƙarfi ganin hankalinta baya inda take. Juyowa ta yi tana kallon Auta bata amsa ba sai binta da kallo da take.. Murmishi Auta ta yi ta miƙa mata kayan hannunta ta ce" Ki yi haƙuri da abin da suka miki Amra Allah zai saka miki ga wannan kici wannan kuɗin kuma ki kai Maman naki Asibiti kinji" Ta faɗa da muryar tausayi." Itama Amra murmishin ta yi ta miƙa hannu ta amsa sannan ta ce" Na gode Auta kina da kirki ba zan manta dake ba a rayuwata." Jinjina kai Auta ta yi ta ciro zoben dake hannunta mai kyau ta kalli Amra ta ce" Bani hannunki nasa miki zobe ina so ki za ma Ƙawata." Ba muso ta miƙa mata hannunta wanda ƙuraje ƙanana suka fito a yatsotsin nata wasu har sun yi ruwa kuɗa nata bin hannun. Cikin tausayawa Auta ta kalli hannun ta ce" To ki riƙe karki saka tun da naga ƙuraje sun fito miki ki sayi magani kisha sai su mutum zan ke sawa direba ya biyo nan dani dan nake ganinki." Jinjina kai Amra ta yi tana zubar da hawaye da ƙyar ta ce" Na gode Ƙawata." Ba komai Auta ta ce kana ta miƙe ta mata bye bye sannan ta koma cikin motar direba yaja suka bar gurin.... Sai da taga tafiyar su sannan ta miƙe da ƙyar tana dafe kwankwasonta da yake mata zafi. "Wash Inna ƙila ƙashin kwankwasona ya karye" Ta faɗa tana buɗe kwalin buskotar.. Ɗago da kan Inna ta yi tana jera mata sannu ta tashe ta, kafaɗarta ta shiga ta taimaka mata ta miƙe. Napep ta tsayar ta ce masa ya kaisu kyamis mafi kusa, kallon Amra mai Napep ɗin ya yi yana done hanci, tsaki yaja yana ce mata taya zai dauketa tana tsami salon ta kashe masa kasuwar shi ga mota da mutane biyu.. Kuka Amra tasa ta durƙusa ta ce" Ka taimaka ka kaimu kaga Innata bata da lafiya magani zan sayo mana ko nawa kake so zan baka ina da kuɗi." Wani kallo ya kwatsa mata ya yi gaba abin shi.. Kuka sosai take tana riƙe da Inna sai neman faɗuwa suke, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta samu wani ya daukesu ya kaisu kyamis.... Tun da suka bar gurin Auta ta murtuke fuska tana kumbura baki, shi ko Daddy ko a jikin shi sai ma faɗa da yake mata akan biskotanta da ta bai wa Amra.... Suna zuwa gida Auta ta fito a guje ta nufi ciki tana kuka.. Kicibus ta yi da Fadila da ƙawayenta biyu sunsha kwalliya suna wani ɗage kai.. "Ke dalla can jaka daga gidan uban wa kike yanzu? Auta ta tsayar da kukan da take ta ɗago kai tana saba baki ta ce" Anty Daddy ne." "Kuma dan Daddy ne ya sakaki kuka sai ki shigo mana afujajan kamar wadda ta gudo daga Dawanau? Nifa kin sani bana son iskanci za ki wuce ko saina bangajeki daga hanyar? Ta faɗa tana nuna mata hanya.. Wani kukan Auta ta kuma sakawa tana sakin schoolbag ɗinta a ƙasa ta kuma ƙarawa kukanta sauti.. Tass tass ƙaran marin ya daki dodon kunnen Direba da yake ƙoƙarin shugowa da ƴar Teddyn Auta. Waro idanu ya yi yana ja da baya jikin shi na rawa.. "Kai kuma munafiki uban me ka shigo yi cikin palonmu? Cewar Fadila tana jefa masa gorar ruwan da tasha rabi ta bar rabi.. Kuka Auta ta Ƙwalla tana riƙe kuncinta cikin jin zafin marin ta sunkuya ta ɗauki schoolbag ɗinta tare da nufar hanyar cikin palon, har ta kusa kaiwa palo ta dawo ta isa gurin direba ta amshi ƴar Teddynta, kallon Fadila ta yi ta ce" Muguwa azzaluma Allah ya isa ban yafe miki sai na faɗawa Daddy" Tana faɗin haka ta kwasa a guje ta shiga ciki." Kanbu! Ni ki ka cewa muguwa? Zan dawo na haɗu dake yau zan ga mai rabamu dake a gidan nan, ba dai Mommy bata nan ba zan yi maganinki" Cewar Fadila tana girgiza jiki ta yi gaba suka bi bayanta.. Tana zuwa saitin mai gadi ta ce" Kai kuma Ɗanladi sai na sa Daddy ya koreka daga aiki tun da in na ce ka wanke mini mota ba za ka yi ba ko? Haƙuri ya shiga bata amma taki ko kallon shi ta shige mota ita da ƙawayenta, kiɗa suka konna kana taja suka bar gidan a guje kamar za su tashi sama... Misalin ƙarfe 11pm na dare Daddy na zau ne yana duba wata jarida, Fadila dake gefe ta kunna kallo ta kawo MBC2 tana kallon wani American film ana ta nuno wasu masoya suna rungume da juna, Auta dake kan stamp ta rafka tagumi tana kallonsu... Da fito ya sanyo kai cikin palon, shi kuma na bayan shi ya shigo yana waka da turanci kiɗa na tashi a cikin wayarsa.. "Oh my god! Daddy yaushe ka shigo gari ne ba ka faɗa mana ba?" Cewar Sudas yana miƙawa Daddy hannu. Dariya Daddy ya yi ya ce" My Son's ai dama surprise na muku daga ina haka?" Wani juyi Sauban ya yi tare da yin rawa ya iso gaban Daddy ya bashi hannu suka tafa, kallon su Auta ta yi sai kuma ta yi saurin saukowa tana murna ta nufo su. Tana zuwa saitin Fadila tasa ƙafa ta taɗeta ta faɗi tim a ƙasa. Sudas ya yi saurin juyowa ya ce" Kai Auta bi a hankali mana har kina faɗuwa." Kallon Fadila Auta ta yi bata ce komai ba ta miƙe ta isa gurin Sudas ya ɗaurata akan cinyar shi ya yi yana shafa guiwar hannunta da take mata zafi... " Sannu Auta Mommy bata dawo ba?" Cewar Sauban yana danna wayar shi... Bata cewa kowa komai ba har suka gama surutun su suka rabu da ita... Miƙewa Fadila ta yi ta wuce ɗakinta, Auta ma ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tana hawa kan stap taga ƴar Teddynta tasa hannu ta ɗauketa ta wuce ɗakinta... Tana shiga ta faɗa kan gado sharar hawaye... Ƴar Teddynta ta rungume tana ci gaba da kuka har bacci ya kwashe ta.. Bata fi minti goma da soam bacci ta farka, saukowa ta yi daga kan gadon riƙe da ƴar Teddynta ta buɗe ƙofa ta fita.. Ɗakin Fadila ta nufa tana mutsitsika idanu, tana isa ta shiga buga ƙofar da ƙarfi tana faɗin" Anty Fadila ki buɗe mini ƙofa." Cikin bacci Fadila taji ƙaran buga ƙofar ta miƙe, a fusace ta nufi ƙofar ranta na tafasa, tana buɗewa ta faɗo ɗakin ta takure a guri ɗaya.. Galala ta saki baki tana kallonta, wani ɓakin ciki ne ya rufe Fadila ta janyo cazar wayarta ta soma tsula mata tana faɗin" Dan

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});