Chapter 18
Chapter 18
baya yana channing duk ke ba ki iya ba gashi dai kinà da komai wanda mata masu class suke nema, ko ba ki ga har gashin doki suke sakawa ba? Tun da ya soma magana Mommy ke tsaye tana kallon ikon Allah, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba murmishi kawai ta yi ta dube shi sama da kasa ta ce" Ka gama ko da saura?" Tsaki yaja ya ɗauki jaridar dake gaban shi ya ce" Malama rufe mana baki a gurin marar wayewa kawai." "Hmm indai wannan ne wayewa ba zan yi ba, kai yanzu dan rashin sanin darajar matar sai na saka kaya masu matsewa na saka mayafi a kafaɗa, sannan na fito da gashina na fita haka dan baka da kishin matarka? To ba da ni ba aure kuma inka tashi ka auro 3 mu za ma 4 a gidan ni ba damuwata ba ce , Allah ya sa ka gane gaskiya Wallahi kaji kunya" Tana gama faɗin haka ta fice fuuu ranta a matuƙar ɓace." Dariya Daddy ta yi ya ce" Mahaukaciya na san kishi ne kike dan na ambaci zan ƙaro aure, ni bani da lokacin ki mai hakin mutanen farko." Da sauri take saukowa tare da faɗin" Daddy! Daddy! Please zan bika ka saukeni." Kallonta ya yi ganin yadda tasha riga da sket kayan sun amsheta fatar jikinta ta haska, murmishi ya yi ya ce" Ba hanya ɗaya za mu bi ba gaskiya Auta ki tafi Direba ya kaiki kawai ni sai na yi wanka zan tafi." Kumbura baki ta yi ta nufi ƙofar fita tana cewa" To ba ruwana dakai yau zan haɗu da Ƙawata ba zan dawo da wuri ba tun da Anty Fadila birthday za ta mana a cikin palo, wani lokacin sai na bar muku gidan nan dan na huta daku mutane kamar jikokin shedanu haba, kowa sai jin kiɗa kun mayar mana da gida kamar club to kun kaini bango saina bar muku gidan na huta da ganin kayan takaici" Haka ta dinga faɗa har ta iso bakin mota ta buɗe ta shiga. Direba dake kallonta ya ce" Auta kin tashi lafiya?" Murmishin yake ta yi ta ce" Alhamdulillah ya gida ya su Anty?" "Duk suna lafiya. Jan motar ya yi Maigadi ya buɗe musu ƙofa suka fita.. Suna zuwa saitin inda suke haduwa da Amra ta ce ya sauketa ya koma tun da gata ga makarantar za ta isa, ba yadda ya iya a sauketa ya dawo.. Shuru ta yi a gurin tana jiran Amra , can daga bayanta taji taku ta yi saurin juyawa suka haɗa idanu da Amra, da gudu ta isa gareta suka rungume juna cikin farinciki ta ce" Ƙawata na yi kewarki sosai kwana biyu ji na yi kamar mun shekara bamu haɗu ba." Amra ta ɗagota daga jikinta tana murmishi ta ce" Nima haka Ƙawata ya gida ina dai fatan Mommyn namu ta dawo ko? Ina kuma Yayanki Sudas?" Cikin zallar ƙaunarta Auta ta ce" Mommy ta dawo jiya Yaya Sudas kuma ai ranar da muka zo nan da dare ya dinga ihu ya ce wai fatalwa ce ta shigo masa ɗaki, kuma da mu ka shiga bamu ga kowa ba na ce ya rakoni ya ce indai school ba zai rakoni ba amma indai wajanki ne zai kawoni, ya ma ce na gaishe ki" Ta ƙarashe maganar tana dariya tunawa da ihun da Sudas ya dinga zundumawa a daren." Dariya itama ta yi ta ce" E lalle ƙila ya yi gamo ne." Kama hannunta ta yi suna ƙoƙarin ficewa Auta ta juyo, waro idanu ta yi ta tsaya bakin na rawa ta ce" Amra ke kalli wata mai ciki ƙila bata da lafiya." Da sauri Amra ta juyo taga abin da Auta ta gani, da gudu suka isa gareta suna faɗin" Baiwar Allah sannu lafiya dai?" Da ƙyar matar ta iya buɗe bakinta ta ce" Ku taimaka mini ku buɗe jakata ku ɗauko wayata ku kira layin mijina shine a sama ,ku faɗa masa halin da nake ciki." Da sauri Amra ta buɗe jakar ta fito da wayar ta dannawa mijin nata kira, har ya yi ringing ya gama ba a ɗauka ba, sake kira ta yi nan ba ba a ɗauka ba har ta katse ran Amra ya yi bala'in ɓaci ta kuma kira, sai da ta kusa tsinkewa kana aka ɗauka muryarsa taji yana faɗin" Haba Bintu wai ke wata irin mata ce kin fitar ma ba za ki rabu dani na huta ba, ba na baki naira dari ba na ce ki hau machine ko wani sabon salon iskanci kike ji da ki ka dameni da kira tun ɗazu? Ballagazar mace kawai na dawo daga kasuwa na kwanta ina hutawa ba za ki barni naji sanyi ba, ke bakya gane lokacin kiran mutum da lokacin da ba na kiran shi ba ki fita idona fa kin sanni ba sanin shanu ba dan miki rashin mutumci in ki ka dawo gidan nan , ina dalili ina mafari in banda nemawa kai fitina ina baccina mai daɗi sai kin tasheni meye haka? Nifa bani da mutumci kin sani kuma na kusa aure na huta dake dama dai ke kin sani ba sonki nake ba Baba ya matsa saina aureki, to dan haka kar ki takurani Wallahi kina dawowa na nakada miki mugun duka ba ruwana da cikin dake jikinki, in ba kwartanci ba ma ai nasan magani ki ka sa mini a cikin abinci har na kwanta dake cikin ya samu, kin san dai da kaina ba zan taɓa nemanki ba dan banga abin so a jikinki ba ƴar gidan mayu kawai, kuma daga yau I... "Kai dalla can dakata! Amra ta faɗa ranta ya yi mugun ɓaci. "Ke kuma daga ina ? Owo wato ke kike daure mata gindi take bijirewa duk dokokin dana shinfida mata ko? Lalle shi ne yanzu ki ka ɗauki wayarta ki ka kirani, to in asiri ne ma ku koma a sake muku wani bar ci ba... "Kaga Malam bana son maganar banza matarka ce ke nakuɗa a tsakiyar titi ka zo ka kaita Asibiti, ki shiga hankalinka shashashan namiji kawai.. "A a fa yarinya karki zageni fa bani da mutumci nan da kike ganina zan miki rashin mutumci yadda bakya tunani... "In ka sake magana saina karya maka wuya azzalumi macici" Tana gama faɗin haka ta kashe wayar ta dubi Auta ta ce" Kinga wannan mijin nata bashi da tausayi, mu tsayar da mota a kaita Asibiti." Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Shi ne abin da matar ke faɗa. "Sannu baiwar Allah yanzu za mu samu mota a kaiki Asibiti" Cewar Amra tana ɗagawa wata mota hannu. Tsayawa motar ta yi ta ce" Don Allah ka ɗaukar mana waccen matar zuwa Asibiti." "To maza ku taimaka mata ta shigo. Da sauri ta dawo suka ɗaga matar har jini ya soma zuba a jikinta, da ƙyar suka sakata a motar suka juya za su tafi suak jiyo mai motar yana cewa" Kai yara ina za ku je ba Antynku ba ce za ku bar mini ita? Ki dawo mu tafi tare." Amra ta dubi Auta ta ce" Ki tafi school ɗin ni zan kaita Asibiti." "A a mu tafi tare gaskiya. To kawai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31