Chapter 16
Chapter 16
Dije. Dariya Dije ta yi taja da baya ta dunƙule hannu, Bala na ɗagowa ta kai masa naushi a hanci nan take ta fasa masa hancin. Ihu Bala ya kurma yana sa hannu ya riƙe hancinsa da yake jin kamar ba a jikinsa yake ba, cikin kuka ya ce" Dije kin fidda mini hancin fa, waiyo Dije anya kuwa Dije na ce wadda na sani ko dai an canja mini ita?" Iska ce taso a cikin ɗakin aka ɗauki Bala ana yin royal dashi a saman ɗaki, kallo ƙasa ya yi yaga Dije ce ta ɗaga shi da hannu ɗaya ta ɗaga shi take wurga shi a sama... "Innalillahi! Dije kasheni za ki yi wai? Ki dawo hankalinki mana nine ba Bala ɗin ki fa. Sai da ta jijjiga shi ya galabaita sumar da Bala ya yi tafi biyar a cikin wannan yanayin, wani irin juyi Dije ta yi da Bala ta sako shi kan gado tana yin dariya, mari ta zabga masa mai zafi hakan ya sa ya dawo daga sumar da ya yi, ihu ta kurma ya janyo bargo ya lulluɓa da fargo yana roƙon Dije ta dena dukansa. Dif yaji komai ya tsaya cak an dawo da wutar ɗakin, leƙo kansa ya yi yana fatan Dije kar ta kuma masa irin wannan damƙar, wayam ya gani ba kowa a cikin ɗakin mamaki da al'ajabi ta kama Bala, a sanyaye ya tashi daga kwanciyar da ya yi soma duba ko'ina amma bai ga alamar Dije ba. "Dije! Dije! "Na'am Maigida ka dawo ashe? Wallahi ina ɗakinka ina yin sallar shafa'i da wutiri dan bacci naji yana neman ɗaukeni shi ya sa na tafi can da na gyara ma ɗakin sai na yi sallar, a a wai lafiya naga hancinka a fashe ko bugewa ka yi da wani abu ? Maigida ka yi shuru baka ce mini komai ba?. Bala da ya saki baki da hanci yana kallon Dije bai san lokacin data ƙaraso kusa da shi ba har sai da takai hannu ta dafa kafaɗar shi. Da sauri ta zabura ya ce" Waiyo Allah! Ki yi haƙuri Dije Wallahi ba zan sake dukanki ba." Cike da tashin hankali Dije ta rungumi Mijin nata, addu'o'i ta shiga tofa masa a kunne tana shafa bayan shi kamar wani ƙaramin yaro, can taji ya shiga sauke ajiyar zuciya yana sumbatu, sosai Dije ta tashi hankalinta ganin Bala a cikin wannan yanayin, ɗago dashi ta yi cike da kulawa ta ce" Maigida wai lafiya kake kuwa?" "Dije ki yafe mini dukan da ki ka mini ya isa haka ina jin ma kin targada mini ƙafa. "Riƙe hannun shi ta yi ta dube shi ta ce" Maigida yaushe kuma aka yi haka? Ni da kaina zan iya sa hannu na dakeka kamar ban san darajar aure ba? To duka ma nawa nake da har zan iya dukanka ka tsaya kana kallona, ka dawo hankalinka nifa ina ɗakinka ban shigo nan ba sai yanzu.. Da sauri ya kalleta zufa na tsatstsafo masa ta ko'ina, cikin shi ne ya bada kululuuu, miƙewa ya yi cike da tsoro ya ce" Dije zawo nake ji ki rakani yau naga rayuwa Dije ki taimaka karki sake dukana aradu na daku, Dije rakani rakani Dije" Ya ƙarashe maganar yaan riƙe cikin. Kafin Dije ta sauko daga kan gado Bala ya soma sakin zawo a jikinsa, da sauri ta kama hannun shi suka nufi banɗaki, suan shiga ta juya za ta fito ya yi saurin riƙe hannunta ya sa kuka kamar wani yaro ya ce" Dije na karki tafi ki barni Wallahi za ki iya rasani in ki ka tafi daga banɗakin nan." Dije ta rasa abin da yake mata daɗi ta tsaya tare da done hancinta jin wani mugun tsami na bugar mata hanci.. Ranar dai Bala kwana ya yi a bakin banɗaki warwas ya yi a ƙasa yana juyi, ganin abin na yi ne ya cire kayan jikin shi daga shi sai gajeran wando shi ma sai tsami yake, Dije ta rafka tagumi tana kallon Bala, jin bai dena sumbatun kar ta dake shi ba ta tashi ta ɗauko Alkur'ani ta shiga karantawa tana tofa masa a haka suka kwana.... ______________ Mommy na fita daga gida gidan Malamin da yake koya mata karatu ta nufa tana kuka, ikon Allah ne kawai ya kai Mommy gidan Malam, tana zuwa ta durƙusa a gaban shi sai kuka take ta kasa ma yin magana.. Malam ya dubi Mommy cike da mamaki ya ce" Azima lafiya? Yaushe ma ki ka shigo ƙasar ne?" "Baba ka taimakeni Auta na cikin wani hali ka zo muje kaga abin da take yi ,lafiya lau na barta amma na dawo na samu yarinya ta canja, labarin da Fadila ta bata ta zaiyanewa Malam.. "Subhanallah! Lalle lamarin nata kamar mai shafar aljannu yanzu kije gobe ki kawo ta nan inma sune za mu gani. "Baba da ka zo yanzu dan ni Wallahi na tsorata da abin da na gani, abincin na kusan mutum 10 fa Auta ta cinye kuma duk cikin minti ɗaya yadda kasan iska haka ta cinye tass ta miƙe tabar mu baki buɗe, Baba ka zo muje don Allah kar wani abu ya sameta iafin safen nan ina jin tsoro.. "Ki kwantar da hankalinki Azima babu abin da zai sameta sai wamda ya rubuto mata a shafin ƙaddararta, ki dena jin tsoron komai in sha Allah zan je goben yanzu kinga dare ya yi maigidanki zai iya dawowa kuma kin san halinsa dai , ki kawo ta nan na mata addu'a ko ma mene ne za mu gani goben da izinin Allah.. Haka ya shiga kwantar mata da hankali yana nuna mata duk abin da yafu da Auta sufa dama can rubutacce ne a shafin ƙaddararta dole sai ya faru , ka ba su da ikon da za su canja mata ƙaddararta Allah ne kaɗai zai iya canja mata ƙaddara ba dai mutum ba.. Jiki a sanyaye Mommy ta tashi ta nufo gida cike da damuwa.. Yau tun da sassafe Auta ita ta tayar da Mommy daga bacci tana kukan wai zazzaɓi take ji, hakan ya sa Mommy ta shiryata tsab suka fito palo suka zau na, Kande ta iso ta kalli Auta ta ce" Autarmu ya dai naga kina kuka? Ko yunwa kike ji na kawo miki abinci?" Fashewa da kuka ta yi ta miƙe tare da riƙe cikinta tana kallon Kande ta ce" Anty Kande ki zuba mini abinci dayawa yunwa sosai naje zan ci kaɗan tun da ina jin zazzaɓi kinga jiya har kaina ciwo ya yi ki kawo mini nan kinji Anty" Ta ƙarashe maganar tana zaman 'yan bori akan carpet." Murmishi kawai Kande ta yi ta juya ta nufi kicthen ɗin, Auta ta kalli Mommy ta ce" Mommy bayana ciwo yake ina za ki kaina a bani magani?" Zuba mata idanu Mommy ta yi duk ta kasa gane kan yarinyar, da farko ta ce zazzaɓi dazu kuma ta ce cikinta yanzu kuma ta ce bayanta, kamo hannunta ta yi ta janyota jikinta ta rungume tare da bubbuga bayanta tana mata sannu a haka Kande ta kawo mata soyayyan kwai da bred haɗe da shayi mai kauri ta aje mata a gaban Mommy ta ce" Autarmu tashi na kawo miki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31