Chapter 3
Chapter 3
uwarki uban me za ki mini a ɗaki ni z.. Bata ƙarasa ba taji an yi caraf da hannunta an zafga mata wani gigitaccen mari wanda ya yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta na wani dakikun... _*Maman Nusaiba ce*_ [25/11, 19:47] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *Littafin Aljanar gidanmu na kuɗi ne only N300* _WhatsApp number. +966599791573_ بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣2️⃣ Baya Fadila ta yi tana murza idanu dan tabbatarwa da abin da taji, bata yi aune ba taji ta jikin miro ta buga hannunta. "Kan uban can! Ta faɗa da ƙarfi tana yarfa hannunta da yake mata azabar zafi. Ɗago da idanunta ta yi ranta a matuƙar ɓace ta kai kallonta bakin ƙofar, Auta dake rakube jikin bangon ɗakin ta ƙara rungume ƴar Teddynta tana kuka marar sauti.. A fusace Fadila ta iso gaban Auta ta watsa mata wani irin kallon wulaƙanci sannan ta ce" Ke! A zabure Auta ta ɗago idanunta ta ɗaura su akan Fadila jikinta na rawa, ja da baya Fadila ta yi tana waro idanu ta ce" Uban me ya kawo ki ɗakina da daren nan? Ko kin fara hauka bayan ɓakin halin da ki ka kwaso na Mommy? Ni ki ka mara Auta? Za ki yi magana ko sai na ɗauki wannan kwalbar na fasa kanki da shi?" Ta faɗa tana nuna mata kwalbar... Baki na rawa Auta ta soma faɗin" Anty Fadila yunwa nakeji banci komai ba ga Mommy bata dawo ba, muje ki dafa mini indomie please " Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka tare da riƙe cikinta." "Mutumelesy! Yanzu saboda kina jin yunwa ne ki ka shigo mini ɗaki, to wai ma waye ya mareni iye? Ta kuma faɗa tana son ɗamko Auta.. Nima ban sani ba Anty" Cewar Auta tana ɗago Teddynta. Tsananin mamaki da tsoro ne suka cika zuciyar Fadila har bata san lokacin data miƙe tsaye ba tana riƙe baki. "Wai da gaske kina nufin ke kaɗai ki ka shigo ɗakin nan? Tabbas nasan tsayinki ba zai kai nawa ba har ki iya marina, to amma waye ya mareni ko dai mafarki na yi? Ta faɗa tana kallon Auta da itama ita ɗin take kallo tana cuno baki gaba. "Ni dai banga an mareki ba kawai dai naga kin yi baya" Cewar Auta tana haɗe rai ta kuma cewa" Abincin nakeso Anty ki dafa mini yunwa nakej." "Tsuww ashe ma mafarki ne na yi dama bacci ne a idanuna na tashi, ke kuma daga yau in ki ka sake shigo mini ɗaki a irin wannan lokacin sai na murde wannan bakin naki na rashin kunya" Ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannu ta kama bakin Auta, ji ta yi an huta mata iska a kunne ta yi saurin juyowa taga wayam, tsaki taja. " Kinga bari naje ko apple ne na ɗauko miki kin san dai ko ruwan shayi ban iya dafawa ba a gidan, gashi har kin sa ina jin tsoro alhalin ba abin da ya tsoratar dani... Ita dai Auta kallon Fadila take har ta gama zazzaginta da rankwashinta ta fita zuwa kitchen.. Tana saukowa palo an kashe wutar falon, kasancewar wayarta na a hannunta sai ta haske da hasken wayar har ta isa kicthen ɗin, wutar kitchen ɗin ta kunna tana kai dubanta fridge. "Ihu ta kwalla ta mannewa da jikin bango tana cewa" Waiyo! Mage me ya kawo mage kitchen kuma? Juyowa ta yi tana kallon kan kukagas, tukwane guda uku ne akan kukagas ɗin sai tafasa suke, cikin Fadila ne ya bada kuuuuuu zufa ta shiga keto mata ta ko ina har bata san lokacin data saki futsari ba a jikinta.. Runtse idanu ta yi tana murza su dan ta tabbatar da abin da take gani, tana buɗewa ta yi saurin isowa gurin tukwanan, abincin ta gani a cikin ɗayar tukunyar farar shinkafa ce har ta yi fiyaya ta yi tsami, ɗayar tukunyar ita kuma farfesun kayan cikine suma sun yi tsami kuɗaje ne yamama a cikin farfesun wasu sun mutu wasu suna ta yawo a ciki, ɗayar kuma taliya ce an yi jalop ɗinta nama ne manya manya a cikin taliyar kamar yanzu aka zuba su a tukunyar sai kannin jini taliyar take.. Ja da baya Fadila ta yi tana mayar da numfashi taji an shafa mata baya. Waiyo! Daddy na mutu na lalace" Ta faɗa tana takurewa a jikin bango.. "Anty ba ki gama ba har yanzu" Taji muryar Auta daga bakin ƙofar kitchen ɗin.. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Fadila ta sauke, a sanyaye ta ce" Ashe ma Auta ce." Kallonta ta yi sake da baki ganin kayan da yake jikinta. "Auta yaushe ki ka canja kaya kuma? Kallon kayan nata Auta ta yi ta dawo da kallonta kan Fadila ta yi dariya cikin nishaɗi ta ce" Anty yau kuwa lafiya kike? Dama ɗazu fa ki ka ce mini wai an mareki kalli jikinki ruwan mene ne ya jika miki kaya?" Tsaki taja tana ƙoƙarin miƙewa Auta ta yi saurin isa gurin tukwanan tana murna ta ce" Anty Fadila ki bari ga abinci ma Kande bata ɗauke ba shi zanci, dama can ke ba iya girki ki ka yi ba sai jin music kamar shedaniya." "Kut ni kike faɗawa magana dan uwarki dan ma kin samu na zo zan haɗa miki abincin? To kin yi da shegiya zan yi maganinki in ki ka sake ƴar wahala" Ta faɗa tana ƙarasa miƙewa." Bata kula ta ba ta isa kan tukunyar taliya ta zuba kaɗan ta dauko gishiri ta ƙara tana jujjuya taliyar tana cewa" Anty zo muci abinci macaroni da naman kifi nasan kina son irin wannan haɗin" Ta ƙarashe maganar tana kai loma.. Shiii! Fadika ta faɗa tana rufe baki ganin Auta ta kai taliyar bakinta sai yafki take kamar an zuba miya. "Ke! Ba ki da hankali taliyar mai yafki za kici tana tsami? Tsayawa Auta ta yi tana kallon abinci cike da mamaki, ita dai macaroni take ci da naman kifi da ɗuminta amma sai ta ce mata wai taliya mai yafƙi da tsami, harara ta watsa mata tana turo baki ta ce" Ni dai ba ruwanki dani tun da yau kin samu ciwon hauka, haka kawai ina cin abinci sai ki ce wai yana yafƙi da tsami? Ki rabu dani yunwa nakeji." Saboda mamaki Fadila kasa cewa komai ta yi sai binta da kallo take kamar an kafeta a gurin.. Kamar wadda ta yi sati bata ci abinci ba haka Auta shiga cin abincin, kafin ta cinye wani ta kai wani, tana gamawa ta miƙe ta wanke hannu a inda ake wanke-wanke ta dawo palo ta zau na akan kujera... Da ƙyar Faɗi taja jiki ta bar kitchen ɗin cike da mamakin Auta wai yau ita Auta ke faɗawa magana? Yarinyar da bata yarda su haɗa idanu . Juyowa ta yi sai taga ba kowa a palon TV kuma kunne yana ta aiki, tsoro ne ya shigeta ta yi saurin yin sama ta nufi ɗakinta da gudu gudu, har ta kusa isa sai ta fasa ta iso ƙofar ɗakin Auta a hankali ta tura ƙofar jikinta na rawa... Waro idanu ta yi tana murzawa ta kuma buɗe su tarr bakinta buɗe take kallon Auta dake kan Sallaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31