Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dakai ba kenan tunda har za muyi maka umarni amma kasa kafa ka shure, saboda baka daukemu da daraja ba shine zaka ki halattar daurin aurenka ko? To ka kyauta kuma duk abinda kayi daidai ne domin ahalin yanzu sai dai kanemi wani uban amma baniba aure kuma nayi maka shi sai dai zaka iya nunawa duniya rashin matsayina ta hanyar sakin matar, nanfa inno itama tadauka ya saketa mana shiyasani kuma mutumin banza kawai kai in banda tsabar raini har ayi maka umarni ka ki bi? Yaran yanzu bakuda kunya kota sisin kobo muda aurenma basai an tare zakaga matar ba,waye zai tsaya jin ra'ayin mutum, hakuri momcy tafara basu hajiya inno ayi hakuri dai, mai martaba dana yayi kuskure amma ayi hakuri ayi masa gafara ayafe masa kar yashiga cikin wani hali dan Allah aduba kokena, tashi inno tayi tafita tanata fada shima mai martaba tashi yayi yafice yatafi fada, kallonsa momcy tayi tafida baka kyauta ba meyasa zakaki zuwa wurin daurin auren? Cikin kasala yace momcy ni auren ne bana so, 27 years nayi aure? Is too early wlh,murmushi momcy tayi babu komai yanzu abinda nakeso dakai anjima da daddare kuzo kaida faisal kubawa sarki hakuri kaji? Naji momcy, yawwa Allah yayi maka albarka, tashi yayi shima yafita. [9:47PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 2⃣2⃣ Na UMMI A'ISHA Da daddare faisal yasaka tafida agaba sukaje wurin sarki suka bashi hakuri amma sai dakyar suka samu ya sauko sa'arsu daya su yan lelensa ne domin badan hakaba da zai dade yana fushin bai huceba, daga nan sashen inno suka shiga itama suka bata hakuri tsakanin da da uwa sai Allah nan itama ta huce tace tahakura suna dawowa dakinsu faisal yafara bawa tafida shawara, abokina kafin katafi India yakamata kaje kaga amaryarka kayi mata sallama, tsaki tafida yayi naji zanje, yawwa mutumina yakamata kaje. Abangaren gidansu amarya kuwa koda mahaifinta yaje musu da batun rashin tariya dawuri nan dangi suka fara kace nace wasu kuma mamakine ya kamasu wannan wanne irin aure ne kodan anga basuda kudi shiyasa za araina musu wayo? Shidai uban amarya baice komai ba kuma zancen da nake yimuku har yau nidai ummi Aisha banga kalar amaryar tafida ba balle na zayyano muku yanda take, kasancewar sarki mutum ne mai adalci yasa ya aikawa da gidansu amarya kayan abinci kala kala yace arinka ciyar da amarya kuma duk lokacin da yakare zai aiko wani sannan duk wata bukata tata arinka sanar dashi hakan da yayi ba Karamin dadi gidansu amaryar sukaji ba. Tafida shirin tafiya yagamu domin yau saura kwana 2 yabar kasar, wanka yayi ya shirya yadau kwalliya cikin bakin danyen boyel yasa bakar hula takalmin kafarsa ma baki yaafito sai zuba kamshin turare yake take fadawansa suka bude masa motarsa yashiga suka rufa masa baya driver yaja sai disina, suna zuwa suka zarce wani dan madaidaicin gida daga ganin gidan gidan talakawa ne masu rufin asiri, cikeda yatsina fuska tafida yafito daga motarsa yanufi cikin gidan fadawansa suna take masa baya, babu ko sallama yakutsa kai cikin gidan yana rayawa aransa wai dan abin kunya nanne gidan sirikansa kai Allah ya kiyaye, atsakar gida yahango mahaifin matarsa da mahaifiyarta tana hura wuta, kafarsa yasa yayi bol da wata buta ta farin karfe atsakar gidan da alama butar mai gidan ce, dayake gwanine wurin kwallo take butar tawuce tasaman kan mai gidan taje tadaki bango tadawo baya tafadi atsakar gidan ta tankwashe yanda bazata moruba har abada. [10:07PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 2⃣3⃣ Na UMMI A'ISHA Cikin tashin hankali mahaifiyar matarsa tafara magana suwaye ku? Me kukazo yi anan gidan? Cikin yayyatsina fuska tafida yadubi wannan mitumin yace bawan Allah yadda kasa aka daura min aure da yarka to tun wuri kaje kasa awarwareshi domin bazan zauna da itaba kuma bazan taba sonta ba, banda tsabar son zuciya tayaya zaka dauki yarka ka kaiwa mai martaba rallarta har alika min ita, to bana sonta kuma sai nasaketa sai asannan suka gane ashe shine mijin yarsu sirikinsu duk cikinsu babu wadda yayi masa magana kawai tsayawa sukayi suna kallonsa fadawansa kuwa sai fadi suke hutawarka lafiya tafida wannan sako naka ya je inda kakeso yaje, abi tafida a zauna lafiya tafida buhun karangiya ko an zazzage dole sai ya makale, gaba salamun baya salamun dan sarki jikan sarki, gunbar dotse, icen kan kabari titi kafi karfin a tsallakaka dole sai an waiga, takawarka lafiya toron giwa dawisu da ado aka sanka, ragayar dutse namijin fama, juyawa tafida yayi yafita daga cikin gidan fadawansa suka rufa masa baya kai tsaye fadarsa yawuce inda wakilinsa yake, anan ya tambayi wakilin nasa wacce gonace tafi kowacce girma agarin? Cikin washewar baki wakili yace ranka yadade gonar sirikinka malam faduluddeen gonarsa tafi takowa girma cikin rashin damuwa tafida yace ok to inaso nan da sati mai zuwa agyara min domin zan turo masu aiki zasuyi min ginin gidan shakatawata awurin, cikin mamaki wakili yace yallabai sirikinka fa, ka iya bakinka wakili fadawa suka fada lokaci daya, shiru wakili yayi yace tuba nake yallabai tashi tafida yayi yana bawa sarkin fada sallahun ginin da za azo ayi masa, cikeda farin ciki yakoma gida domin yasan abinda yayiwa mahaifan matarsa dole zasuji haushi kuma kila zasu samu sarki suce yasashi yasakar musu yarsu amma abin mamaki shiru yaji ba wani batu alokacin har ansoma fara yimasa ginin gidan da yabada umarni acikin yanayin yashirya yanufi kasar india yana cikeda haushin auren da yake kansa. [10:45PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 2⃣4⃣ Na UMMI A'ISHA Lokacin da tafida ya tafi india ya samu damar mantawa da auren dayake lankaye akansa sai dai kusan kullum idan sunyi waya da faisal yana yawan yimasa maganar amaryarsa dariya kawai tafida yakeyi domin yanzu ya daina damuwa idan faisal yana yimasa tsiya, cikin ikon Allah yasamu yagudanar da course dinsa cikin kwanciyar hankali da nasara wata 5 daidai yayi yafara shiri ysdawo Nigeria. Ranar da yadawo ranar fada ta cika makil da yan sannu da zuwa faisal kuwa sai zolayarsa yakeyi amma yashareshi har sai da suka koma daki sannan yakalli faisal yace mekake cewa dazu? Dariya faisal yayi abokina kayifa kyau sosai kayi fresh kodai kabi hanyar ne? Tsaki tafida yayi kai wai baka da wata magana sai kwaya daya? Ai ni nafada maka ko zanbi hanyar da kake fada to ba yanzu zan bitaba, dariya faisal yayi to malam yakamata fa kasan inda dare yayi maka dan wlh nakusa korarka daga dakin nan? Wazaka kora? Kai zan kora tunda yanzu Kai magidancine so sai kakoma wurin iyalinka, kamanta zurriyya ba iyaliba tafida yafada tareda mikewa yafara cire rigar jikinsa domin shiga wanka. Washe garin ranar da tafida yadawo yakwanta yayi baccinsa ranar bai je office ba sai wurin 11 sannan yashirya cikin suit milk colour yasa milk colour din takalmi yasha turare yafito dan zuwa asibitinsu yana so yaje yakai report, agidan baya yazauna acikin motarsa fadawansa suna tareda shi har asibitin yana fitowa daga mota wasu yanmata wanda zasu kai kimanin su 20 suna sanye da unifoam suka fara kallonsa da alama yan practical ne aka turosu asibitin duk cikinsu babu wadda tafida bai tafi da imaninta ba nanfa suka fara tattauna maganar a tsakaninsu. Sai da tafida

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});