Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a nice eyes,and some hv a nice faces, you u hv all of them & nice heart Good morning & hv a nice day! I. T, tana gama karantawa sai kuma tasoma hawaye wanda nikaina ummi Aisha ban san ko na menene ba. [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣2⃣ Na UMMI A'ISHA Kuka take sosai wannan wanne irin abune da aurenta ta rinka son wani mutum nadaban, istigfari tafara yi ba kakkautawa acikin yanayin kawarta zara'u sulaiman tazo ta sameta zama tayi gefen gadon tafara tambayarta da hannu meyafaru? Dakyar tadauki biro zara'u yau zan bar asibitin nan dama kin san acikin satin nan zan gama practical dina gida zan koma idan kingama naki ma hadu a sch dariya zara'u tayi to kijirani zanje nadawo tana gama rubuta mata ta tashi tafita, hawayenta tagoge tadauki takardar taboyeta acikin rigarta, tana nan zaune aka kawo wata mata marar lafiya agadon kusa da ita aka kwantar ta Jim kadan sai ga likitanta yazo wato dr tafida idonsa akanta yaje yagama duba matar nan yabata dukkan taimakon daya kamata sannan yadawo inda take, da ido yayi mata alama wai meya sameta idonta yayi ja, murmushi tayi takada hannu alamar babu komai takarda yadauka yarubuta mata meye sunanki? Da babban baki tabashi amsa sunana HANFA yana karantawa yayi murmushi meye ma'anar hanfa? Dan ni ban taba jin wannan sunan ba, murmushi tayi yakamata ka rinka bibiyar tarihi amma nabaka assignment go and find out d meaning of hanfa murmushi yayi yace zan kuwa baki mamaki domin zan samo miki ayau basai gobe ba yana gama rubutawa yabata yafita daga masu jinyar har nurses din kallonsu suke tayi to kodai sun san juna wannan abin mamaki ya isa domin ada ibrahim tafida (I.t) baya tsayawa yayi magana da patient amma gashi yau yatsaya yanata rubuce rubuce da kurma gulma nurses din suka fara yi agefe daya duk dai sun san ita wannan marar lafiyar yar practical ta hadu ta cancanci hakan. [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣3⃣ Na UMMI A'ISHA Agurguje yagama abinda yakeyi ya koma gida abinda bai saba yiba tashi karfe biyu amma yau yayi saboda yana so yasamu damar binciko ma'anar sunan hanfa, yana zuwa gida yasamu sirikinsa yana fitowa daga fada ko kallonsa bayi ba balle yasa ran zai gaisheshi tafiyarsa yayi cikeda takama fadawa suna biye dashi suna takawarka lafiya dan toron giwa gaba salamun baya salamun dahaka yashige gida dakinsu yaje yabaje ya jawo laptop dinsa yafara searching din hanfa sai da yadade yana nema sannan ya samo cikeda farin ciki yatashi yaje dakin inno bata cikin dakin dan haka kan gadonta ya haye yayi dai dai yana tunanin hanfa ba shakka sunanta ya dace da ita kuma ya cancanceta ganin inno bata shigoba yasashi mikewa zai fita daga dakin sai gata kuma ta shigo,a'a tafida dama kana nanne? Kai yadaga mata ina nan inno ai tun dazu nadawo amma sake fita zanyi, to amma dai sai kaci abinci ko? Murmushi yadanyi to inno abani kadan naci dakanta tafita ta hado masa abinci takawo masa harda kayan marmari agefe zama yayi yadanci abincin kadan yatashi yafita yakoma dakinsu yayi wanka yafito yashirya tsaf cikin blue colour din jeans da riga dark brown mai gajeren hannu yana fitowa yahadu da faisal ya yau da wuri zaka fita kilisar ne abokina? Faisal ya tambaye shi, no zanje asibiti ne amma bazan wani jimaba zan dawo, ok sai kadawo faisal yafada yawuce ciki shi kuma tafida ya fita, yana zuwa su sarkin fada suka bude masa kofar mota ya shiga ya zauna sai asibitin kwararru na rasheed shekoni wanda yake da xango acikin garin misau. [4:08PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣4⃣ Na UMMI A'ISHA Suna isa asibitin ya nufi female ward yashiga nurses din dake ciki sai fadi suke welcome sir! Last bed ya hanga amma babu kowa cikin rudewa ya tambayi daya daga cikin nurses din ina patient din dake last bed? Ahankali tace dr dazu tatafi, ahargitse ya kalleta are you mad? Danme zaku barta tatafi ban sallameta ba, meye amfaninku agurin? Wannan ya nuna min cewar baku san aikinku ba, sai kun karbi query saboda sam bakuda hankali hakuri suka soma bashi we are sorry sir! Ko kulasu bai yiba yafice daga cikin ward din, to shi yanzu ina yanufa? Tunda bai san inda yarinyar nan takeba sa'arsa daya yasan sunanta, fita yayi yashiga motarsa fadawansa suka rufa masa baya, ransa abace yake yau sanadiyar rashin ganin hanfa da wannan bacin rai suka karasa gida yana zuwa dakinsu ya fada akan gado ji yake kawai kamar ya fashe da kuka, tabar wiwi ya janyo ya kunna ya fara zuka nan fa ya turnuke dakin da hayaki kamar salansar babur, faisal dake kwance kusa dashi yana bacci ya bude ido yafara kallonsa dan ganye ka fara zuke zuken naka ne? Shiru tafida yayi masa domin bacin ran dayake ciki baxai barshi ya iya yin magana ba tabarsa yaci gaba da busawa batare da yace komai ba tuni idonsa ya kada yayi jajawur kamar jini ganin abin bana kare bane yasa faisal kwace sauran wiwin ya boye yana cewa kai meyasa wani lokacin baka da saiti ne? Sai kaje kajawa kanka wata cutar, kana likita amma baka san abinda zai illataka ba, dakyar tafida ya iya bude baki yace faisal ban ganta ba, wacece? Faisal ya tambayeshi yarinyar da nace maka nahadu da ita a asibiti, to kuma shine zakazo kayita shan wiwi? Ai kamata yayi katsaya ka nutsu ka binciko inda take amma baka zauna kayita bunkawa cikinka hayaki ba lumshe idanuwansa tafida yayi yace nagode abokina insha Allah zan kokarta kwanciya yayi yafara hango kyakkyawar fuskar hanfa, Allah sarki kowa da yadda Allah yake jarrabarsa ita kuma haka Allah ya halittota kurma sannan kuma bebiya amma ya tsara halittarta yadda bazai kwatantu ba, dan tsaki yaja ni ba muryarta nakeso ba kuma ba jin maganarta nakeso ba ita kanta nake so kuma insha Allahu sai na mallaketa. [5:09PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣5⃣ Na UMMI A'ISHA Zama jugum tafida yayi yana ta sake sake acikin ransa gamida tunanin yadda zai nemo sahibarsa hanfa daren ranar bashida wata walwala har gari ya waye, shiryawa yayi yadda yasaba cikin suit bakake yasa bakin takalmi yasa glass dinsa fari dan siriri yafito agurguje ya leka wurin mai martaba yafito yashiga wurin inno yana fitowa yanufi asibiti koda yaje tuni har ma'aikata sun firfito manyansu da kananansu, gakuma yan attachment suma duk sun fito, yana zuwa yawuce office dinsa yafito yashiga maternity jim kadan yafito yashiga female ward nanma bai fi minti biyar ba yafito yana fitowa yashiga antenatal,yana fitowa yadaga yan yatsunsa guda biyu yashiga office take dogarawansa suka furtsa aguje suka nufi office dinsa nanfa yan practical suka fara kace nace wato wannan daga yatsun dayayi ashe fadawansa yayiwa magana lalle sarauta sai me ita,basu farga ba sai ga wani bafade guda daya yazo inda suke yayi musu sallama yace wacece zara'u acikinku? Gani zara'u ta amsa, to kizo mai girma tafida yana son ganinki, hanzarta yanmata, tafida ikon Allah tafida mai jan doki, dasauri zara'u ta tashi tanufi office din dr tafida yayinda dogari yake biye da ita yana fadin takawarki lafiya

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});