Chapter 13
Chapter 13
kuwa nan mai martaba ya rufeta da fada baji ba gani, cikin fuskar alhini momcy tace to ranka yadade ni kayi min izini gobe sai naje disinan da kaina nataho masa da matarsa, hajiya mabruka muddin kikaje to wlh bada yawuna ba kuma babu hannuna aciki,aure dai ai nine nayi masa ko? To babu ruwanku aciki ku zuba min ido kawai, tashi momcy tayi tana fadin Allah yahuci zuciyar ka ranka yadade amma mai martaba sai fada yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tashi momcy tayi ta koma sashenta tana shiga tasamu su faisal suna zaman jiranta, cikin damuwa tafara magana, nayi duk iya kokarina amma mai martaba bai saurareni ba asalima cewa yayi idan naje disina to bada yawunsa ba, amma abinda nake so dakai tafida shine kayi hakuri mujira muga nan da gobe ko Allah zai sa ya sauko, kai kawai tafida ya iya dagawa yamike faisal yabishi suka fita, suna zuwa dakinsu tafida ya zube akan gadonsu yafara fitar da numfashi mai zafin gaske shikuma faisal ya zauna yafara bashi baki, wunin ranar nan tafida yayi shine kawai amma acikin bacin rai yake shi kansa a matsayinshi na likita yasan bp dinsa yahau sosai ba kadan ba dan yaji alamun hakan ajikinsa, gashi ko ruwa bai sha ba bare yaci abinci har dare yayi. Wurin misalin karfe 10 nadare tafida ya kalli faisal yace abokina dan Allah kayi min wani taimako, ina jinka fadi injishi, so nake gobe katafi disina gidansu hanfa kasamu mahaifinta kuyi magana ta fahinta kaji ko ahaka aka haifeta da lalurar kurmanci da bebanci, idan ba haka aka haifeta ka dauketa ka kaita asibitin tafawa balewa teaching hospital akwai likitan kurame acan kuma insha Allahu akwai taimakon da zai bata, cikeda tausayawa faisal yace dama kurma ce? Kai yadaga wlh faisal kurma ce kuma bebiya bataji kuma bata magana amma tahadu fiyeda yadda baka zato gata da hazaka domin ahakan take karantar nursing, girgiza kai faisal yayi Allah sarki Allah yabata lfy ya daidaita tsakaninku, amin faisal sa'ar danayi ma da ban saketa ba tun da farko da matsalar da zan shiga sai tafi haka, kayi hakuri dai tafida ka kwantar da hankalinka tunda kasan illar saka damuwa acikin zuciya daga kai tafida yayi yashiga duniyar tunani har faisal yayi bacci amma shi faisal yadda yaga rana haka yaga dare ga wani azababben ciwo da kansa yake yi masa dakyar yatashi ya dauko brief case dinsa ya bude yadauki abin auna jini yafara auna jininsa nan yaga yahau fiyeda zatonsa ahankali ya mayar yakoma ya kwanta, alla alla yake gari ya waye dan faisal ya tafi disina. [9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣3⃣ Na UMMI A'ISHA Wayewar garin ranar faisal yashirya ya tafi disina alokacin tafida ko tashi zaune baya iya yi, lokacin da faisal yaje gidansu hanfa tarbar arziki mahaifanta sukayi masa, bayan sun gaisa yace baba dama zuwa nayi naji ko dama hanfa haka aka haifeta da wannan lalurar? Cikeda alhini mahaifinta yace wlh faisal da bakinta da kunnenta muka haifeta har ta girma ta xama budurwa, haduwarta da lalurar shekaru uku baya ne da suka wuce tayi wata rashin lafiya mai tsanani tun daga lokacin tadaina magana tadaina ji, amma da lafiyarta lau yakarashe maganar yana kwalla, ayya Allah ya rufa asiri faisal yafada yanzu tana ina? Tana ciki, dama ina sone zan kaita asibiti likita zai dubata, cikeda farin ciki mahaifinta yace Allah saka da alkhair madallah madalla nagode, tashi yayi ya shiga ciki bai jima ba sai gasu sun fito tare da ita kallonta faisal yayi agaskiya kyakkyawa ce sosai shiyasa tafida ya rikice da hannu suka gaisa ya bude mata mota tashiga yayiwa mahaifinta sallama suka tafi, suna zuwa asibitin faisal yafita yaje yabude mata polder aka nuna masa inda zai ga likita sannan yakoma yataho da hanfa suna zuwa tabi layi tazauna wurin ganin likita basu fi su biyar ba, tana nan zaune har layi yazo kanta suka shiga tare faisal, likitan da zai dubata bature ne nan yafara bincikarta yana wasu yan rubuce rubuce, tare da dauko wani zungureren almakashi yadauki audugu yatura a kunnen yafito dashi nan yacewa faisal gado zasu bata, za ayi mata aiki zasu biya kudi dubu dari bakwai da hamsin tashi faisal yayi yafita yaje banki ya ciro kudin yazo ya biya jifa jifa tafida yana kiranshi awaya yana tambayarshi halin da ake ciki, bayan ya gama biyan kudin ne yatafi gidansu hanfa ya sanar musu abinda zai gudana nan da nan mahaifiyarta tahada kaya suka nufi asibiti sai da faisal yagama yi musu komai sannan yayi sallama dasu yakoma misau sai yamma lis ya isa gida yana zuwa yasamu tafida kwance adakinsu ga ledar ruwa nan ana kara masa ashe duk wannan wayar da yake yimasa karfin hali kawai yakeyi shima yana kwance, sannu tafida yau likita ne dakansa ake kara masa ruwa? Murmushi tafida yayi faisal ya kukayi da hanfa? Cikin fara'a faisal yace an bata gado aiki zasuyi mata nan da kwana 3 fatan dai Allah yasa adace amin faisal nagode Allah yabar zumunci, haba tafida duk abinda nayi maka ai kaina nayiwa Allah yabaku lafiya, tashi yayi yafita saboda tsabar tausayin dan uwansa da ya shigeshi. [9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣4⃣ Na UMMI A'ISHA Acikin kwanakin kullum sai faisal yaje garin disina yayinda shikuma tafida yana nan akwance yana jinya jininsa ne yahau over gashi tunda yake bai taba yin hawan jini ba sai a wannan lokacin, ranar da za ayiwa hanfa aikin aranar faisal yatafi da sassafe dama duk abinda suke bukata shi yake kai musu, yana zuwa asibitin ya samu za ashiga da ita dakin da za ayi mata aikin ga iyayenta agefe ko wannensu zuciyoyinsu babu dadi haka shima faisal yatsaya suna nan tsaye har tsawon awa 2 sannan aka fito da ita kai daga ganinta kasan tawahala mutuka wani daki aka zarce da ita amma da alama ba ayi nasara ba, sai bakar wuya da tasha domin sai da aka fara yimata fanfo sannan aka yimata wankin kunne kai wuya dai kala kala tashata amma bata samu lafiya ba domin sauki daga Allah yake nan mamanta tafashe da kuka shi kansa faisal ji yake kamar yayi kukan domin bai san halinda tafida zai shiga ba idan yaji cewa bata warke ba, tashi yayi yashiga office din likitan dan neman karin bayani anan likitan yake sanar dashi cewa sunyi iya bakin kokarinsu amma ba adace ba kuma amma kunnenta lafiya lau yake dan haka agobe ma zasu iya tafiya gida godiya faisal yayi masa yafito yazo yasamu iyayenta yayi musu bayanin abinda likita yace, babu komai Allah yasa haka shine yafi alheri mahaifin hanfa yafada alokacin faisal yayi musu sallama yakama hanyar misau yana zuwa ya tarar da tafida yana jiransa nan ya zauna yafada masa dukkan abinda ya wakana, cikin damuwa tafida yace babu komai ni dama ita nakeso ba wani abu nata ba amma yanzu abinda nakeso dakai faisal dan Allah kaciri kudi gobe kaje kasiya musu gida mai kyau ka zuba musu furnitures kasiya musu kayan abinci domin babu amfanin ni ina zaune awuri mai kyau ina cin mai kyau amma matata tana cikin kuncin rayuwa kai faisal yadaga hakane Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36