Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

murmushin mugunta take yi masa tsaki yadan ja ni kike yiwa dariya ko? Hmm ki gama dariyarki yau yarinya yana gama fadin haka yatashi yafita yana cewa ki zo na maidaki inda na daukoki saboda yau amfaninki kadanne, yana fita ta tashi ta shirya tafito lokacin har ya fita daga falon yashiga motarsa, motar taje ta shiga suka tafi, in banda tsaki babu abinda tafida yakeyi domin yau gaba daya ya gama sa rai da samun hanfa, dariya hanfa tayi aranta tace bakayi tsaki ba sai ranar da kaji nabar misau na tafi disina, hannunta ya kamo kamar yadda ya saba yafara wasa da yan yatsun hannunta har sukaje wani store inda ake sayar da kayayyaki kala kala, ciki yashiga yasiyo mata dan karamin gas wanda zai ishesu girki har na tsawon wata uku sannan ya iyo mata shopping din kayan cooking daga nan yafito yashiga restaurant yasiyo mata take away da drinks masu sanyi yadawo motar, dan kallonsa hanfa tayi sai kuma taji tausayinsa ya shigeta saboda yadda taga yana yi mata hidima ga kudinsa da yake kashewa akanta, makarantar ya mai data yayi packing a inda yasaba tsayawa dama gaba daya motocinsa gilasan tintac ne sai kace wani marar gaskiya, kinje kallon hawa? Ya tambayeta yana lankwasa yan yatsun hannunta, kallonsa tayi eh naje ananma naga yan matanka ai, dariya yayi har hakoransa suka fito, ni inada yanmata ne? Kodai yanmatan faisal kika ga? In dai faisal shine tafida to yan matansa naga. [7:04PM, 11/25/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣2⃣ Na UMMI A'ISHA Tafida daban faisal daban amma ni banida wasu yan mata faisal ne mai yanmata, sai dai nima nakusa nayi budurwa acikin makarantar nan, kallonsa hanfa tayi tafara kokarin kwace yan yatsunta daga hannunsa ai ya halatta kayi tunda an baka dama kayi mata 4 babu laifi, sake damke hannunta yayi yace ni bazanyi 4 ba amma zanyi 2 shine ra'ayina murmushi hanfa tayi duk kuwa da cewa kishi ya tuketa, Allah yabaka ikon yin adalci amin uwar gida yafada yana murmushi, kinga wata fine baby can ko da ita zanyi miki abokiyar zaman? Waiwayawa hanfa tayi ta hango mami wata yar room 4 tana karantar midwifery bazata fita a haifeta ba yar kano ce daidai lokacin tazo kusa dasu, sauke glass din tafida yayi yace yanmata ji mana, babu musu mami tadawo tace gani, kallon hanfa yayi tayi kicin kicin ta hade girar sama data kasa, yi hakuri dama sako zan baki amma barshi kawai, ok babu matsala amma da ka fadi sakon naka, ki barshi nagode yafada yana daga glass din sama, kallon hanfa yayi kema haka kike da kishi? Dubawa zakayi sai kagani tafada tana kawar da kanta, to ai gashi naduba nagani kinada kishi, meye abin kishi? Ni indai ta nine ka auro mata 3 banida damuwa, karya kike kawai dai kin fada ne, amma dagaske fa yarinyar nan kyakkyawa ce, da sauri ta jiyo ta kalleshi dagaske fa kace, to ko dagaske auran nata zakayi? Eh ai na fada miki aure zan kara sai ku tare lokaci daya, shiyasa kake so kayi min ciki saboda zakayi sabuwar amarya? Sai kuma hawaye yafara bin kumatunta cikeda mamaki ya kalleta meye abin kuka? Nifa da wasa nake miki jawota jikinsa yayi ya rungumeta yafara lasar lebenta kidaina kuka wlh wasa nake miki kuma duk kyanta kinfita kyau bata da wani kyau ma, ki kwantar da hankalinki ni ke kadai kin isheni rayuwa kuma wlh banida wasu yan mata, dariya tayi bata shirya ba saboda jin abinda yafara yi mata, sakinta yayi yana dariya wannan dan karamin cikin naki yakusa zama babba, fuskarta ta dauke daga kallonsa ta kalli window,idan kinje kiyiwa zarah sannu kinji, zataji hanfa ta fada tana kokarin bude kofar motar, kayanta yafito mata dasu ta dauka ta tafi hostel. [7:22PM, 11/25/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣3⃣ Na UMMI A'ISHA Juyawa tafida yayi yatafi yana cike da kewar matarsa ya nufi asibiti domin yanada theatre. Ita kuwa hanfa hostel tashiga hannunta dauke da kaya niki niki lokacin zarah har ta dan warware shewa zarah tafara yi dakyau mrs tafida muma mun zama yan gayu mun daina amfani da stove mun dawo girki da gas, zama hanfa tayi tana dariya kwarai kam, ai ke kam kinyi sa'a tafida yana ji dake ban san me kika bashi haka ba yabi ya rude, ke kika sani kuma hanfa tafada tana murmushi domin ita kanta tasan tafida yana sonta saboda abubuwan da yake yi mata kadai sun isa su tabbatar da hakan, lumshe idonta tayi ta fara hango soyayyarsa mai dadi da tsayawa arai, haka tayita gudanar da abubuwanta cikin nishadi da annashuwa amma tun daga ranar tafida bai kara shigowa school dinsu ba saboda wai baya so yazo yaganta tayar masa da hankali zata yi alhalin kuma tana fashin salla ba wani abune zai gudana a tsakaninsu ba, haka yayita daurewa amma kullum yana yi mata waya ta wayar zarah. Ana igobe zata fara salla tashirya tayi tafiyarta disina bayan sun gama waya da tafida amma bata sanar dashi zata tafi gida ba saboda tasan idan tafada masa zaiyi amfani da karfin ikon igiyoyin aurensa dake kanta ya hanata tafiya tunda yanzu a karkashin ikonsa take, haka taware abinta batare da saninsa ba shi kam tafida alla alla yake jibi tayi domin lokacin yasan tagama period yaje ya dauketa amma koda dare yayi yakira zarah yace tabashi matarsa sai zarah tayi mamaki tace bata fada maka dama zata tafi disina ba? Gabansa yaji yafadi yaushe ta tafi? Wlh da safe lokacin da kuka gama waya ta tafi, amma da nasan bata fada maka ba wlh da nafada maka, yaushe zata dawo? Sai nan da 3 weeks wlh, to zarah nagode sai da safe yafada cikeda damuwa. [9:06AM, 11/26/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣4⃣ Na UMMI A'ISHA Ajiye wayar tafida yayi cikeda bacin rai, har tayi tafiya bata sanar dani ba ina matsayin mijinta? Yayi mata kyau yafada afili nan ya kwanta yana mai cikeda kunar rai ahaka faisal yazo ya riskeshi awannan halin shi dai agaskiya yanada bukatar matarsa dan haka gobe ko jibi zai je disina koda kuwa mahaifin hanfa zai koroshi haka ranar yayi bacci cikin damuwa. Wayewar garin ranar bai samu yaje disina ba saboda patients din da ya wuni yana dubawa dan haka washe gari yashirya tsaf cikin shadda mai tsada fara yasa hula yasha turaren active man yatafi disina shi kadai yatafi bai tafi da kowa ba domin acewarsa sirrinsa zai je yagano. Karfe 11:30 ya isa gidansu hanfa yana yin packing yafara tunanin ta yadda zai tunkari gidan, ta maza yayi sannan yafito yashiga gidan yana sallama baban hanfa ne yafito yana ganinsa ya murtuke fuska yafara tambayarsa me kadawo yimin agida? Ban gaya maka kar nasake ganin kafarka agidana ba? Maza maza ka fice min daga gida kar nasake ganinka agidana har abada sannan kuma ban yarda kasake koda magana da yata ba bare har kabita makaranta, cikeda damuwa tafida yace dan Allah baba kayi hakuri, ka fitar min agida nace kuma ko kofar gidana ban yarda kasake zuwaba, zubewa tafida yayi yafara rokonsa amma bai saurareshi ba haka ya koreshi fata fata nan fa idon tafida yakada yayi jawur yafita yashiga motarsa yatafi,

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});