Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hangota lokacin data shige lungun momcy. [8:37PM, 11/28/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 8⃣7⃣ Na UMMI A'ISHA Yana nan tsaye yana murmushi hannuwansa cikin aljihun wandonsa faisal yazo ya tarad dashi sannu dan iska faisal yafada yana harararsa,wlh ka kusa barin dakin nan dan banga dalilin da zai sa ka rinka yimin abinda kaso aciki ba, murmushi tafida yayi yadan lashi lebensa wlh kaine dan iska kuma saurin me kakeyi dama ai nakusa barin dakin saboda nafi son nazauna da matata zama na dindindin amma koda yaushe ni atakure ita atakure, dariya faisal yayi yaro wannan karon sai dai kaje wurin mai martaba kai daya amma ni bazan rakaka ba, dariya tafida yayi haba abokina tare zamuje murmushi faisal yayi yaja hannunsa suka shiga falo. Hanfa nazuwa dakin momcy takwanta tafara shafa cikinta dagaske tafida yake har yabata ajiyarsa? Murmushi tayi inama a school nake da nayi test nagani idan hakane amma kuwa indai maganar tafida tazama gaskiya yazama sharp shooter daga yi sau 1 sai in samu ciki, haka tayita raya zancen acikin ranta ita kadai tana yi tana murmushi. Tun daga lokacin tafara shirin komawa disina tunda tafidan ya warke kaya aka harhada mata na alfarma tun daga kan wanda zatayi tsaraba har zuwa wanda yake nata, ana igobe zata tafi tashiga lungun inno babu kowa afalon dan haka takarasa cikin dakin nanma babu kowa sai tafida data hango yana kwance agadon inno yana bacci yana sanye da three quarter ja da bakar Riga,kallonsa ta tsaya yi ikon Allah da girmanka kazo ka kwantawa tsohuwa agado, sadaf sadaf ta karasa bakin gadon, hannunta tasa tashafi sumar kansa ta karkata kanta ahankali ta lashi lips dinsa, bude ido yayi kamar a mafarki yaganta hannunta dake kan kumatunsa ya dafa yaushe kika shigo? Yanzu nashigo naganka kana bacci, kallonta yayi yanzu tafiya zakiyi ki barni? Murmushi tayi kajika sai kace idan natafi natafi kenan, zaune ya tashi yakama hannunta yafara yi mata dabara wai zai taba babynsa yaji lafiyarsa, daga taba babyn kuma yafara yin sama kokawa suka fara dakyar tasamu ta kwace ta gudu. [9:03PM, 11/28/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 8⃣8⃣ Na UMMI A'ISHA Tana guduwa takoma dakin momcy nan ta zauna suka yita hira har dare yayi washe gari kuma tashirya faisal yadauketa sai disina tun ahanyarsu ta tafiya faisal yafara bata labarin cewa yana son kawarta zarah adan zaman da sukayi a asibitin nan har sun daidaita nanfa hanfa tashiga murna tayi fatan Allah yasanya alkhairi, karfe 1 suka shiga disina dayake basu tafi da wuriba ,suna zuwa gidansu hanfa iyayenta taresu da murna tareda bawa faisal kyakkyawar tarba, sai da yayi salla sannan yayi musu sallama yatafi nan kuma hanfa ta shiga maraicin mijinta da dokin ganinsa amma kusan koda wanne lokaci tana shafa cikinta tana kulada ajiyar da yabata. Satinta 2 da dawowa ta tafara shirin komawa makaranta wannan lokacin ma tafida babu abinda bai siya mata ba domin provision yayi mata nagani nafada komai da zata bukata sai da yasai mata ranar dazata tafi kuma yaturo su sarkin fada da babban zaginsa suka dauketa domin alokacin faisal yana yin wani aiki, katuwar mota Highlander baka mai bakin glass ya turo a ita aka dauketa yayinda ita kuma tayi shigarta cikin bakar doguwar riga da dan karamin hijab dayake tafiyar yamma tayi karfe 5 ta isa makaranta, tana zuwa hostel suka rungume juna itada zarah nan tashiga taya zarah murna domin tasan faisal yanada kirki ita da tafi ganin kirkinsa ma fiyeda tafida sai daga baya sannan ta fahimci shima tafidan yanada halin kwarai. ALHERI DANKO NE! 8⃣9⃣ Na UMMI A'ISHA Tunda tadawo bata ga tafida ba shima bai ganta ba sai dai waya da sukeyi awayar zarah yauma zaune take bayan sun gama wayar zarah ta kalleta wai mrs tafida anya kuwa? Dariya hanfa tayi meya faru mrs faisal san turaki? Kallonta zarah tayi kin ganki ne? Menayi? Wlh kinyi kiba kinyi kyau kuma kirjinki sun ciko tashi hanfa tayi taja doguwar riga tasa tace wlh zarah lafiyata lau kawai dai kibari acikin zuciyarta tace ai tafida ne bana wasa bane wlh duk dafin hannunsa ne yasani cikin wannan yanayin, kallon zarah tayi bari naje lab nadawo,fita tayi tana tafe tana tunani gwara yau nayi test dinnan nagani koda gaske cikin gareni, tana zuwa lab tayi test amma sakamako yana fitowa taga bata da juna biyu. [9:34PM, 11/28/2015] Ummi A'isha: Nan tadawo hostel cikeda murna domin tasan da dagaske ne da zata sha kunya duk da cewa ba haramun bane amma da kunya ace baka tareba kayi ciki, zama tayi agefen gado tafara kallon zarah wadda tayi hade hadenta na Karin ni'ima tana sha kallo kawai hanfa take binta dashi har tagama bayan tagama tadauko wani turare wai na matsi ne dariya hanfa tayi zarah kinada hankali kuwa? Meya faru? Kidaina shan wadannan abubuwan kijira kiga yadda faisal zai yi dake tukunna, kallonta zarah tayi malama barni nagyara nayi tsam, kada kai hanfa tayi nabarki amma nidai nan da shekara ma idan kika bani maganin matsi bazan yiba, saboda me? Saboda wahala zarah, zaro ido zarah tayi dan Allah hanfa dagaske da wahala? Dariya hanfa tayi ai zarah ki kaddara tunda kikazo duniya baki taba shan wata wahala wadda zakisha akan wannan abun ba, nidai tunda uwata takawo ni duniya ban taba shan wuya samada wannan ba shiyasa nayi mamakin yanmatan da suke iya bada kansu awaje, tsuru tsuru zarah tayi yau nashiga uku, ai zarah baki shiga uku ba sai ranar tazo, ni saboda tsabar wahala ana gamawa sai da na shanye babbar robar ruwa anan take, saboda tsabar wahala, tofa lallai wahala tayi wahala inji zarah, ai zarah wahalar ta isa wlh danni ranar kasa bacci nayi ga ciwon jiki shiru zarah tayi barni haka karkisa na sume dan Allah kyaleni haka dariya hanfa tayi tace zakiyi bayani. ALHERI DANKO NE! 9⃣0⃣ Na UMMI A'ISHA Yau tunda wuri tafida yataso daga office yataho wurin hanfa amma koda yazo bai samu ganinta ba yadda yakeso domin alokacin ma lecture takeyi haka suka gaisa aguguje ta tafi duk da haka yaji dadin ganinta domin yasameta da shigar da yace ta rinka yi haka yatafi yanata tuninta domin kwalliyarta tayi masa kyau sosai saboda jar arabian gown tasaka tayi rolling duk da bawata kwalliya tayiwa fuskarta ba da tunaninta daren ranar yayi bacci kamar yadda itama tayi bacci da tunaninsa. Washe gari takama juma'a tunda yaje office yaduba patients yanufi makarantar su hanfa lokacin dayaje yayiwa zarah waya yace ta turo masa ita nan hanfa tashirya taci kwalliya dama daga wanka tafito tasha turarenta na night feelings tasa doguwar riga tafita, tun daga nesa tahango motarsa kirar Mazda 6 ash colour mai bakin glass murmushi tayi wai kai wannan kowacce motarka haka take da bakin glass kamar wani barawo, motar tabude tashiga yana zaune yasha farar shadda wadda ta dau dinki irin nasu na masu rawani, ina yini? Tafada kanta akasa lfy maman baby, ya baby na? Murmushi tayi wlh babu wani baby acikina ni dayace, kallonta yayi ban yarda dake ba, tashin motar yayi yana cewa sai munje na aunaki fita sukayi daga cikin makarantar yanufi asibitinsu yana zuwa yace tafito tashiga office dinsa shi zaije round, office dinsa tashiga tazauna tafara kalle

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});