Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tashi kayi yana tashi ta juya baya har yayi yagama madam baki bani ruwa ba ai, robar ruwa tadauko ta rufe idonta tazo ta bashi har yagama idonta a kulle yake sannan ta karbi silbar ta nufi toilet. Zaman hanfa a asibitin nan yasata daura aniyar bawa mijinta soyayya domin kullum yan mata wuni suke suna yi musu zarya a asibitin domin duba tafida, kwanansu 15 aka ce zasu iya tafiya gida in yaso sai arinka zuwa gida ana dubashi nan suka shirya kayansu suka tafi, wannan shine karo nafarko da hanfa zata shiga gidan sarauta tun daga bakin kofa tafara kallon tsaruwar gidansu tafida wanda yake makeken gaske yasha shuke shuken kayan itatuwa su dabino da dogon yaro, shi kansa wurin packing din motar unguwa gudane gashi waje waje lungu lungu, lungun su tafida sukaje wanda yake babban falone da katon daki wanda yasha kayan ado masu kyalkyali da kyau ga shinfidu daki daki, dakin kuwa ba a magana domin wani mulmulallen gadone da jibgegiyar katifa akai ga labulaye nan masu design mai kyau kai abin dai sai wanda yagani. [8:09AM, 11/27/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣8⃣ Na UMMI A'ISHA Tunda sukaje gidan hanfa take kallon abin mamaki iri iri agidan komai kuyangune keyi kuma alokacin jakadiya tasata agaba zuwa fada inda zata gaishe da mai martaba,suna shiga fada taga fadar mai girma ce ga ado da kwalliya da aka yi mata sannan ga wata kujera mai kamada gado da dan abin dora kafa agaban kujerar wadda aka yita da barawon gold domin in banda kyalli babu abinda takeyi, bayan hanfa ta kwashi gaisuwa ne suka koma lungun inno anan aka yi mata masauki acikin dakin inno ai tuni inno tashiga nan nan da hanfa domin tana sonta sosai ganin yadda take kula da tafida a asibiti. Tunda suka dawo gida ita taci gaba da kulawa da tafidan kuma yanzu alhamdulillah jikinsa yayi sauki hakarkarinsa ne har yanzu bai gama warkewa ba amma kamanninsa sun dawo. Yau tunda yamma tadawo dakin inno tayi wanka tashirya domin ta baro tafida yana bacci, bayan ta shiryane tasake komawa tana shiga taji motsinsa acikin toilet nan ta zauna tana jiran fitowarsa tana nan zaune har yafito yana ganinta yafara murmushi tareda wucewa inda kofa take yatura kofar yasa key yadawo, kallonsa hanfa tayi ya haka? Hannunta yaja yahadata da jikinsa yafara kissing din bakinta,wuyanta da goshinta nan yafara rudata da soyayyarsa tareda janta zuwa gado acikin dabara ya rabata da kayan jikinta nan yafara shakar kamshin dake fita ajikinta, wasannin daya saba yi mata yafara amma na yau yasha bamban dana kullum nan hanfa tafara fita hayyacinta saboda wahala amma yau tafida yarantse sai yanemi hanyarsa yabi, duk kukan da hanfa take yi bai sashi kyaleta ba har sai da yasamo hanyar yabi, hanfa ta jigata sosai ga azabar datake ji ajikinta,dakyar tafida yadan kyaleta ta huta in banda hawaye babu abinda take yi, tana dan hutawa tafida yafara shafarta tareda kokarin maimaita abinda yayi domin hanfa tagama rudashi, nan kuma tafara kokarin hanashi amma takasa sai da yajishi zamzam sannan ya iya hakura amma dakyar ya iya barinta,dakyar tayi masa magana da dasasshiyar muryarta, bani ruwa nasha cikin sauri tafida yadauko mata babbar robar ruwa yabata tana karba tafara sha bata ajiyeba sai data shanye ruwan ciki tas. [8:29AM, 11/27/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣9⃣ Na UMMI A'ISHA Tana shanyewa ruwan baccin wahala yace muje zuwa take baccin wuya ya dauketa, zuba mata ido tafida yayi yana kallonta hakika hanfa tazama wani sashe na rayuwarsa, Allah sarki yau namiki rashin tausayi hanfa yafada acikin zuciyarsa tashi yayi yashiga toilet yayi wanka yafito yasa riga bakar t shirt da green din three quarter yazauna zaman jiran hanfa ta farka, gefenta ya kalla duk wurin yagama baci kai hanfa yau kinsha wuya yafada yana shafa gashin dake kwance a hannunta ahankali tabude idanuwanta wadanda sukayi ja kamar jini, yana ganin tafarka yatashi yadau wayarsa yafara kiran momcy, tana dauka yace momcy dan Allah ki turo min jakadiya amma kutaho tare cikeda tsoro momcy tace lfy? Momcy kuzo dai kawai yana fadar haka yakashe wayar, ai hanfa najin haka sai kuka, wannan wanne irin abune? Komai daya faru sai ansani, kai me za ayi da gidan sarauta sam babu sirri yanzu wannan abinma sai ansani? Nan tasake barkewa da kuka nidai tafida yagama cutata yarasa a inda zai min wannan abin sai agidansu gidan surukaina agaban iyayensa,ganin tanata kuka yasa tafida fara lallashinta sorry my wife, nine ko? Sannu, bata kulashi ba taci gaba da kukanta,tashi yayi yaje yabude kofa momcy da jakadiya yagani, meya faru? Momcy ta tambayeshi momcy yarki ce batada lafiya, meya sameta? Momcy kishiga zaki gani yafada yana shafa kansa, shigewa su momcy sukayi anan suka ci karo da ta'asar daya aikata kallon jakadiya momcy tayi tace maza tashiga bandaki ta tari ruwan zafi ita kuma tafito ta nufi sashenta tadebo wasu maganguna shi dai tafida yana tsaye afalo yakasa zaune yakasa tsaye, har momcy tadawo ta kalleshi sannu da aiki yarinyar tayi zaman jinyarka a asibiti ko gama hutawa batayi ba kabita da wannan danyen aiki tana fadin haka tashige dakin, ita da jakadiya ne suka gyara hanfa sukayi mata komai suka gasata tashiga ruwan zafi sannan suka fito suka barta tayi wanka tafito lokacin an sake shinfida sabon zanin gado. [8:54AM, 11/27/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 8⃣0⃣ Na UMMI A'ISHA Zama tayi tashafa mai tasaka kayanta tabi gadon takwanta sai da tayi bacci sannan su momcy suka fito daga dakin ita momcy mamakin rashin kunyar tafida takeyi kodan yaga shine auta amma in banda rashin ta ido irinta yaran yanzu yaushe zakayi haka agidanku, yana ganin sun fito yatashi momcy kun fito? Eh idan ta tashi dakina zata zo ba dakin inno ba kaji? To momcy, suna fita yashiga dakin yatsaya yana kallon hanfa wadda ta bararraje akan gado tana bacci, falo ya koma sai ga faisal ya shigo yana ganin faisal yaje ya tare bakin kofa ya tsaya, kan kujera faisal yakarasa ya zauna yace mutumin ashe ka warke na tayaka murna da rabon bazaka mutuba sai ka nemo hanyarka, dariya tafida yayi acikin zuciyarsa yace zancen yaushe kuma nikam ai har nasamo hanyata nabita naje inda zanje nadawo, tashi faisal yayi zai shiga daki cikin sauri tafida yasha gabansa, malam yau dakin nan babu shiga fa saboda nayi ajiya aciki, dariya faisal yayi dalla matsa min laptop dina zan dauko, ok to tsaya nadauko maka komawa faisal yayi yazauna tafida yashiga dakin ya dauko masa ya kawo, nan shima ya zauna lokaci lokaci yana leka dakin yaga ko hanfa ta tashi, ba ita ta farka ba sai karfe 6:30 tana tashi tayi yunkurin saukowa daga kan gadon amma ta kasa, nan tafida yashigo yaganta sannu kin tashi? Harararsa tayi tafara saukowa ahankali kamar wata mai koyon tatata tafara tafiya tazo tawuce ta gabansa tana fita falo kuma taga faisal a hankali tawuce tafida yana binta abaya nan faisal yabisu da kallo, suna fita tafida yadauketa a kafadarsa yayi lungun momcy da ita, akan gadon momcy ya kwantar da ita yace bari nakawo miki magani kisha kinji, fita yayi yakoma dakinsu yana shiga faisal yafara tsokanarsa ashe kai yau garin da baka taba zuwa

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});