Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gudu yake shararawa bana hankali ba ga faisal yanata yi masa waya amma bai dauka ba daf da zai shiga garin misau wata tirela tayi gaba da motarsa ji kake taratsatsatsa tafida bai tashi ganinsa ba sai agadon asibiti, gasu faisal da mai martaba tsaye akansa inno kuwa da momcy sai kuka sukeyi, ya bugu sosai ya karye a hakarkarinsa na dama gashi hatta harshensa ma ya tsage gida biyu banda daddaujewa da yayi, wani likita ne ya shigo yaduba shi anan yace ana bukatar za akara masa jini, jinin faisal akaje aka diba aka kara masa, gaba daya kamanninsa sun canja ko magana baya iya yi duk wanda yaga motar daya yi accident din da ita kuwa bazai yi zaton ya rayuba saboda yadda tayi kwatsa kwatsa, shi kansa faisal duk dauriya irin tasa sai da ya zubarwa da tafida hawaye. [9:12AM, 11/26/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣5⃣ Na UMMI A'ISHA Lokacin da labari yajewa gidansu hanfa iyayenta suka taso sukazo dubashi alokacin baya gane wanda yake kansa hakuri baban hanfa yafara bashi tareda cewa yabashi hanfa ko yau yake son kawota gidansa yaje yadauko ta,har suka tafi tafida bai san abinda ake yi ba, bayan tafiyarsu da kwana 2 iyayen hanfa suka ce tashirya tazo tayi jinyar mijinta babu musu ta shirya ta taho saboda dama kawai dauriya take amma tana cikin damuwa, asibitin tafara zuwa itada zarah sulaiman anan tasamu faisal da mai martaba da momcy, sunyi murnar ganinta sosai tareda jajantawa juna, lokacin dataga tafida kuwa kawai kuka ta fara saboda yana jin jiki. Kwananta 2 a asibitin yafara gane komai har yana dan bude baki yayi magana dayake an cire dinkin da aka yiwa harshensa, zarah kuwa kullum tana zuwa dubashi daga sch, ko abinci ta ruwa ake bashi amma jikin nasa yadanyi sauki. Kwananta 5 yafara magana radau, tana zaune agefen gadon yabude idonsa babu kowa adakin sai su 2 magana yafara yi mata ahankali, hanfa nasan mutuwa zanyi amma ko namutu faisal kawai na yarda ki aura domin shine dan uwana kuma aminina sannan abokina kiyi hakuri hanfa yana fada yana hawaye, cikin hawayen itama tace bazaka mutu yanzu ba tafida insha Allahu ba yanzu zaka mutuba bakinta tasa akan nashi tafara yadda yasaba yi mata duk lokacin da suka hadu wato zagaye lips dinta da harshensa, hanfa mutuwa zanyi nafada miki rungumeshi tayi ba mutuwa zakayi ba tafida ko kamanta da abinda ka fada min? A kunnensa ta rada masa so kake ka mutu ba kayi min cikin ba? Murmushi tafida yayi itama murmushin tafara yi ga hawaye kuma akan kumatunta hannunsa yasa acikin rigarta yafara shafa cikinta zaki haifa min baby? Kai tadaga cikeda jin kunya, ganin wasan nasa zaiyi yawa yasata tashi taje tasawa kofar dakin key tadawo, kokarin cire rigarta yafara yi da hannunsa guda daya mai lafiya, taimaka masa tayi tacire rigar nan fa yafara sarrafata da hannu daya. Sai da ya nishantu sannan ya rabuda ita, jin ana kwankwasa kofa yasa hanfa tashi tasaka rigarta da hijab dinta ta nufi kofar dakin tabude, faisal ne yashigo shida wata bakuwa suna shigowa faisal din yafita ita kuma bakuwar takarasa ciki daidai lokacin tafida yafarka yabude idonsa akan kujerar dake gaban gadon tazauna tana fadin sannu baby, cikin sauri hanfa ta kalleta baby kuma? Hmmm wai nidai ummi Aisha nayi nan. Ausar! Ausar! Naci karo da sakonki, mun gode Allah yabar kauna da zumunci on behalf of hausa novels [truncated by WhatsApp] [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:14PM, 11/26/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣6⃣ Na UMMI A'ISHA Kallonta hanfa ta farayi daga sama har kasa, farace sosai dogawa mai manyan idanuwa kyakkyawa ce ta ajin karshe kuma daga ganinta yar masu kudi ce, ahankali tafida yabita da kallo amma bai yi magana ba ita kuwa bakuwarsa ci gaba da yi masa sannu tayi, sannu baby ashe haka abu yafaru wlh sai jiya nakira faisal nake tambayarsa me yasamu phones dinka inata kiran ka bana samunka shine yake fada min kasamu accident ne, to yau kuma ban samu flight din safe ba shiyasa, ita dai hanfa tsaye tayi tana jin ikon Allah wannan shine karfin hali wai barawo da sallama agabanta wata tana kiran mijinta da baby abinda ita bata taba kwatantawa ba lallai dole ta daura damara kuma yazama dole tasake shiri na kulawa da tafida, nan fa kishi ya motsa ta bata rai, hannu tafida yadaga mata alamar zai sha ruwa, ruwa marar sanyi ta dauka fuska babu walwala ta isa bakin gadon tazauna babu damar ya tashi zaune kuma idan tasa masa robar ruwan a bakinsa ruwan zai tafi har ta hancinsa, abakinta ta dura ruwan sannan ta hada bakinsa da nata tafara zuba masa ruwan acikin bakinsa ahankali yana shanyewa har yakare tasake guntsar wani ta zuba masa haka tai tayi har ya koshi ita kuwa bakuwarsa har yanzu bakinta bai yi shiru ba sai cigaba da jajantawa take yayinda shi dai tafida yaki magana saboda bai san yadda hanfa zata dauki bakuwarsa ba, domin tare sukayi makaranta da ita a lokacin da suke karatu itama doctor ce kuma tun a makaranta ta nuna tana sonsa amma shi baiji yana sonta ba saboda ko ashekaru ma shekarunsu zasu zo daya gashi babanta shahararren mai kudi ne jin dadi da hutu sun gama baibayeta hakan yasata wayewa sosai shi kuma yafi son ya auri wadda bata wayeba domin yafi son wadda komai shine zai koya mata kamar hanfa babu abinda ta sani sai abinda yayi mata, hankalinsa ne yadawo jikinsa jin hannun nana ajikinsa tana tabashi cikin sauri ya kalleta yace nana meye haka kuma? [8:05AM, 11/27/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 7⃣7⃣ Na UMMI A'ISHA Ayya sannu baby kawai ina sone naji yadda temperature din jikinka take aiki amma naji normal take, kallon hanfa tafida yayi tagama kuluwa kawai kallonsu take, shigowar zarah ne ya sata samun sukuni, duba tafida zarah tayi sannan taja hanfa suka fita suna fita hanfa tafara yiwa zarah korafi tana cewa ita zata tafi gida cikeda mamaki zarah tace saboda rashin wayo ko me? Mijin naki bashida lafiya kitafi ki barshi? Anya kuwa kina sonshi? Shiru hanfa tayi aranta tace lallai zarah bakida seti ai tun ranar da nafara ganinsa nakamu da sonsa kuma tun lokacin da ya nuna min soyayyarsa mai dadi najishi yashiga raina, zama zarah tayi tabata shawarwari masu amfani sannan tayi mata sallama ta tafi. Tunda zarah ta tafi bata shiga dakin ba sai da bakuwar tafida tafito suka tafi da faisal sannan hanfa takoma cikin dakin, tana shiga tafida yakirata madam zo nan, shareshi tayi taki zuwa, idan baki zo ba wlhi ban yafe miki ba jin haka yasata tashi taje inda yake, hannu yasa yajata gefen jikinta ya kwantar da ita yafara yi mata kalamai masu dadi nan taji hankalinta ya kwanta jin tafida ya fada mata ita kadai ce a birnin zuciyarsa, kanta ya shafo fitsari nakeji da sauri ta tashi fitsari kuma? Kaga faisal yafita kuma dama shine yake taimaka maka kayi, to yanzu meye nufinki? Zama zanyi tayi da fitsarin har sai faisal yazo? Kallonsa hanfa tayi to ya za ayi? Kira min nurse din nan ita tasan yadda zatayi harara ta watsa masa tadauko wata ya silba ta bashi

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});