Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yakaimu goben. Acikin kankanin lokaci faisal yaje garin disina yasiyawa su hanfa hadadden gida mai kyau wanda yadace da zamani yazuba musu furnitures dama unguwar ba unguwace mai hayaniya ba babu bata lokaci suka koma gidan nan iyayenta da ita kanta suka shiga yiwa faisal addu'a domin duk atunanisu shine yake yi musu wannan hidimar, lokacin da faisal yadawo gida ya sanar da tafida ba karamin dadi yajiba anan yake sanar da faisal cewa an hadashi da wani malamin addini wanda yake taimakawa mutane dan haka zaije ya duba hanfa ko Allah zai sa adace, hakan kuwa akayi faisal yaje yadauki malami suka tafi gidansu hanfa, suna zuwa malamin yace taje tadauro alwala sannan ya bukaci da abashi ruwan zamzam original ba jabun ba nan faisal yatashi yaje wani Islamic chemist anan cikin garin ya siyo yakawo, ruwan zamzam din malamin yajuye acikin wani koko yafara addu'a yana watsawa akan fuskar hanfa take tafadi akasa, cigaba da watsawar yayi yanayi yana addu'a har aka kwashe tsawon lokuta alokacin yafara yiwa su faisal bayanin cewa hakika hanfa tana fama da matsala ta jinnu kuma kurame ne gashi sunfi wahalar sha'ani amma aci gaba da addu'a, nan faisal ya zauna agarin bai tafi misau ba sai dai suna yin waya da tafida. Kwana uku malamin nan yayi yana yiwa hanfa magani amma shiru sai akwana na hudune Allah yabada nasara jinnun sukayi magana amma da hannu suke nuni da haka malamin yace sufita daga jikinta amma da yake masu taurin kaine sai da suka sha wahala sannan suka fita. [9:56AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣5⃣ Na UMMI A'ISHA Sai da malamin yaja musu kunnen cewa su sakar mata kunnenta da bakinta kafin su fita, suna fita tayi wata irin atishawa mai karfin gaske, Allahu akhbar hakika sauki da rashinsa daga Allah suke tuni tafara wani bacci mai nauyi, malamin ne yajiyo gasu faisal yace wato abinda yafaru shine ruwan zafi ita wannan baiwar Allah ta zuba musu to shine suka shiga jikinta amma insha Allahu yanzu tasamu waraka farin cikine ya mamaye zukatansu asannan mamanta tayi magana tace dama lokacin taliya tadafa tana tacewa tashekar da ruwan shikenan tun daga lokacin tafara jinya, girgiza kai malamin yayi shiyasa ba aso azubar da ruwan zafi akasa dan haka sai akiyaye nan suka zazzauna suna jiran farkawarta sai da ta dade tana bacci sannan ta farka bakinta dauke da addu'a nan fa ta kalli mamanta tace mama! Wato masu karatu ni ummi Aisha sauran kadan nasaki wayata tafadi taci screen saboda tsananin zakin muryar hanfa danaji wata irin zazzakar murya ce da ita shi kansa faisal ji yayi kamar wata balarabiya balarabiya tazama maida kallonta tayi ga faisal tace nagode Allah yasaka da alheri tana gama fadin haka tatashi hawaye suna bin kumatunta tashiga daki tayi alwala tafara salla domin nuna godiyar ta ga Allah yayinda shi kuma faisal yadauki malam suka koma misau suna zuwa yafara yiwa tafida albishir ai tafida bai san lokacin da yadiro daga kan gado ba yazo ya rungume faisal tuni yaji jikinshi yaware nan yafara tambayar faisal nawa za abawa malam? Yace duk abinda yasamu domin shi bai yanke ba, ok to zan bashi dubu dari biyar da mota daya da gida guda daya take shima tafida yafada bathroom yadauro alwala yazo yafara nuna godiyarsa ga Allah. Bayan hanfa ta warware ne tafara shirin komawa makaranta nanfa tafida yayi siyayya mai tarin yawa yabawa faisal ya kaimata duk abinda yasan zata bukata sai da yasai mata kayan kwalliya da kayan abinci da drinks kala kala hatta pad sai da ya siya mata ga turarruka masu tsada nan iyayenta da ita suka shiga godiya bayan tafiyar faisal mahaifinta yake ta yabon faisal sannan yabata labarin cin mutuncin da dan uwan faisal din yayi masa wato mijinta tafida tun daga nan taji ta tsani tafidan tun kafin ta ganshi. Ranar Monday ta shirya tadawo makaranta nanfa yan makaranta suka shiga mamaki jin hanfa bebiya tawarke yayinda wasu kuma suke cewa ai babu mamaki da sha'anin Allah, ranar data dawo makaranta ranar tafida yafara zuwa office bai dawo ba sai 5 tunda yadawo yaci abinci yayi wanka yafita shida babban zaginsa da sarkin mota yana daga baya azaune yace musu school of nursing zasuje haka kuwa minti kadan sai gasu acikin makarantar suna shiga suka fara tafiya ahankali har sukaje gaban wani hall inda dalibai ke tsattsaye group group da alama daga lecture suka fito nanfa daliban suka fara bin motar tafida da kallo wata babbar jeep ce kirar kamfanin crotoure baka mai bakin gilasai an rubuta tafida 4 ajiki, ba aganin wanda yake ciki, ido tafida yafara budewa yana kallon daliban can ya hangota da uniform ajikinta da dan karamin hijabi iya kafadarta tayi wani kyau sosai tana tsaye cikin maza sunfi biyar da modern biology a hannunta da alama bayani take musu nanfa yaji ransa ya sosu, babban zaginsa ya cewa yaje yakira masa ita koda yaje hanfa bata kulashiba sai ma gurmuda baki da tayi duk abinda tayi akan idon tafida yana kallonta ta glass din motar dan haka koda babban zagi yadawo bai jira bayaninsa ba yabude motar yafita nanfa kallo yakoma kansa yatsuke cikin bakar riga mai gajeren hannu ajikin rigar an rubuta big guy da jan fenti yasa jan trouser da jan takalmi irin nasu na sarauta hatta belt din da yadaura ja ce yadora bakar jacket asama ahankali yafara tafiya yana zuwa yajiyo da ita yaja hannunta nanfa tafara turjewa ganin haka yasa tafida fizgota jikinsa ya rungumeta nan fa su babban zagi da sarkin mota suka fito da gudu suka zo inda suke suka baza babbar rigarsu sukayi musu runfa suka lullubesu ahankali tafida yadago kanta yasa bakinsa akan nata yafara zagaye lips dinta da harshensa,tofa muje zuwa dai masu karatu. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [5:39PM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣6⃣ Na UMMI A'ISHA Cikin sauri hanfa ta bude idanuwanta ta fara kallon fuskarsa bakinsa kan nata gashi ya wani kankameta duk kamshin turarensa na fogg ya cika hancinta ras! Taji gabanta ya fadi, jan hannunta yayi yakaita cikin mota yabude gidan baya yasata shima yashiga sukuma su babban zagi suka zauna daga waje, yayinda dalibai suka yi cirko cirko suna tattauna wannan lamari da ya afku wasu kuma ba karamin burgesu tafida yayi ba, suna shiga cikin mota hanfa tafara matsawa yana binta, tana matsawa yana matsowa har taje jikin kofa daidai lokacin ya karasa matsowa kusa da ita kallon fuskarsa tayi yawani rankwafo jikinta, jikinsa yana gogar nata hatta numfashinsa akan fuskarta yake sauka, tunani tafara yi, yana yi mata kama da faisal sosai sai dai yafi faisal kyau, komai nashi ya tsaru sai kace shi yayi kansa dan kyau, to kodai shine tafidan? Duk yadda akayi wannan shine tafida mijina sannan kuma still dr din da ya dubani a asibiti tafada acikin ranta, hakika taji dadin kasancewarsa a matsajin mijinta amma kuma sai ta wanashi ta nuna masa kuskurensa na ciwa mahaifinta mutunci da yayi domin tana son ta nuna masa cewa iyayenta suna da martaba da kima a idonta, iska ya hura mata akan fuskarta take tajiyo wani kamshin strawberry me hade da splash ya fito daga bakinsa, ahankali kamar meyin rada yace kin

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});