Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yashiga yazauna cikeda nuna isa yake daddana wayar hannunsa fadawa sai kawo gaisuwa suke yi amma yakasa amsawa,asibitin Rasheed shekoni specialist hospital suka dosa inda tafida yake aiki. [7:48PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 8⃣ Na UMMI A'ISHA Suna zuwa kamar kullum yafito yashiga office dinsa wanda yake jere ajerin gwanon ofisoshin kwararru na asibitin, yana zama wata nurse tashigo tana sanye da fararen kaya,morning sir! Morning ya amsa mata idonsa yana kan laptop dinshi yana daddannawa, sir akwai patient wanda jiya kayiwa operation tofa har yanzu bata farfado ba, cikeda damuwa ya tashi domin shi yana tausayin mata duk lokacin dayaga mace acikin halin rashin lafiya sai yaji kamar zaiyi kuka, maternity yanufa wannan nurse din tana biye dashi abaya ita dai wannan likitan yana burgeta domin yasan aikinsa matsalarsa kawai yanada girman kai ga nuna isa kamar shine sarkin ko dan sarauta ne? Yahadu sosai ga kudi da sarauta ga ilmi ga uwa uba kyau, yana shiga maternity yafara bin patient din daya bayan daya yana dubasu har yagama yakoma office dinsa alokacin yafara ganin marassa lfy wadanda suka zo ganin likita kuma gaba dayansu matane domin shi mata kawai yake dubawa baya duba maza sai wurin 11 yagama ganin marassa lfy yayi breakfast yatashi yashiga round. [8:16PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 9⃣ Na UMMI A'ISHA Yana dawowa daga round yanemi wuri a office dinsa yazauna lokaci lokaci fadawansa suna lekowa domin ganin lafiyarsa, sai misalin karfe 5 yatashi lokacin yafito daga theatre cikin gari suka shiga akan hanyarsu ta tafiyane suka ratsa tawani dan kauye anan yaga wata makekiyar gona wadda akalla zata kai kilo mita 5 anyi shukar shinkafa aciki, shukar tayi kyau sosai sarkin mota ya yiwa magana cewa ya tsaya cikin sauri ya taka birki yaja ya tsaya yabude kofa yafito suma fadawan firfitowa sukayi suka tsattsaya, gonar ya zubawa ido ta kayatar dashi hakika wannan zatayi daidai da wurin da yake nema domin gina business suit dinshi hadida gidan shakatawarsa motar ya koma yashiga ya zauna, fadawansa suka shisshiga suka nufi gida tun da suka shiga yasan cewa mai martaba yau yana fada dan hakan fadan yashiga wacce ta kayatu sosai, mai martaba yana zaune akan wata karagar mulkinsa ta alfarma wadda tasha ado da zinare, gefe daga hannunsa nadama wazirine da galadima ga chiroma, kusa dashi kuma hakimin cikin garine, daga hannun hagu kuma wani dan dattijone zaune wanda shekarunsa zasu kai na mai martaba kusa dashi kuma san turakine wato faisal aminin tafida, cikin sallama tafida yazauna yayi gaisuwa yatashi yashige cikin gida yawuce dakin inno yau bai wani jimaba yafito yashiga dakinsa yayi wanka yafito cikin bakar riga da bakin wando, yanufi lambu wanda yake girke acikin gidan, wurin yasha shukoki na kayan marmari ga wata korama daga tsakiya tana gudana can gefe wasu kujerune hadaddu aka ajiye saboda hutawa kan kujerar yaje yazauna amma ko minti 5 bai yiba yatashi yafita yanufi dakinsa yashiga yakunna tv yakamo tashar kwallo yafara ganin wasan arsenal da man u, wasan yafara kayatar dashi faisal yashigo remote ya dauka yakashe tv din domin yasan yanzu zasuyi fada saboda faisal dan arsenal ne shi kuma tafida dan man u ne gashi ancisu har 2-0 yasan idan faisal yagani yau zai sha tsiya, kusa dashi faisal yazauna. [8:32PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 1⃣0⃣ Na UMMI A'ISHA Kusa dashi faisal ya zauna yafara dariya ko kallonsa tafida bai yiba yadauke kansa shikuwa faisal sai dariya yakeyi, haushi tafida yafara ji yace ya isheka haka,dariya faisal yayitayi sai da yayi mai isar shi sannan yace kasan me nake yiwa dariya? Jiya jiyan nan kagama yimun bayanin kaifa bakasan hanyar da zakabi ba awurin mace idanma aka ajiye maka mace bakasan yadda zaka bida itaba to sai gashi yanzu za abaka mace nan da sati 2,kaga ashe kenan ka kusa kasamo hanyar ko? Wani kallo tafida ya watsa masa ni zanyi aure amma ba yanzu ba sai nan da 3years dariya faisal yakumayi kasan Allah? Kai angone kakusa ganin hanya, wai kai waya fada maka aure zanyi ne? Uhm abokina bazaka yarda da abinda nake fada maka ba sai kaji kira daga wurin mai martaba sannan zaka gasgata ni, tsaki tafida yayi insha Allahu kai zai yiwa aure amma baniba,ni daba dan iska ba wa zaiyi min aure yanzu? Kai da kasan mata kake nemansu ai kai yadace ayiwa aure, dariya faisal yayi kasan Allah? Wlh kakusa zama ango kai barima kaji dazu daka zo kasamemu da mai martaba wlh maganar aurenka akeyi kuma nan da sati biyu za ayi, cikeda mamaki tafida ya kalleshi wai dagaske kake yi? Wlh Allah dagaske nake tafida wlh aure mai martaba zaiyi maka dazu akanka mukayi meeting da yamman nan kuma wani abin burgewar ma zaka samu virgin girl kamar yadda kake virgin boy, zumbur tafida yamike ni za ayiwa aure yanzu? Wanne laifin nayiwa mai martaba da zai hukantani ta wannan hanyar? Wa zai aura min? Yaya kamanninta suke? Girgiza kai faisal yayi wlh ban saniba abokina, to nima dai ummi Aisha ban saniba sai muci gaba da bibiyar tafida, masu karatu muje zuwa kubiyo Aisha. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [8:53PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 1⃣1⃣ Na UMMI A'ISHA Kallon faisal tafida yayi ai kuwa wlh bazai taba yiyuwa ba nikadai ne da agidan? Akan me za ayi min wani aure yanzu kai ba gaka nan ba haba da Allah wlh bana so babu wanda zai rabani da gidan nan yanzu, kuma wlh duk yarinyar da tayi kuskure ta aureni sai ta raina kanta, dariya faisal yayi wadda takara kular da tafida kaga bani zaka fadawa ba kamata yayi kaje gurin mai martaba kayi masa wannan bayanin amma nidai ina tayaka murna sai dai shawarata agareka itace kasan mai martaba baya yin magana 2 daga yayi magana to yagamata so be careful kar kaje kajawa kanka, kaga mitumin nan nadazu daka samemu afada dashi? Shine mahaifin yarinyar wlh kayi dacen suruki cikeda bakin ciki tafida yace malam banfa tambayeka ba dan haka kayi min shiru banza kawai dariya faisal yaci gaba dayi ganin haka yasa tafida ficewa daga dakin yatasamma lungun inno wadda yake da dan tazara daga sashensa, yana shiga yatarar da bata cikin dakin sai kuyanginta suna gyara dakin kusan ko wanne lokaci dakin nata cikin gyaransa ake, shiyasa koda yaushe yake cikin tsafta tamkar dakin sabuwar amarya, suna ganinsa sukayi waje suka bar aikin da sukeyi, gadon inno ya dale yakwanta idan dasabo kowa agidan yasaba ganinsa akan gadon inno koda wanne lokaci yagadama zai zo yahaye yasha baccinsa akai kamar wani yaron goye. [9:36PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 1⃣2⃣ Na UMMI A'ISHA Rufe idanuwansa yayi amma yasan ba bacci zai iya yi ba maganganun faisal ne kawai suke dawo masa jiya jiyan nan kagama fadamin idan an baka mace baka san yadda zakayi da itaba sai gashi nan da sati 2 zaka zama ango an baka mata, zunbur ya tashi zaune jin abin yake kamar a mafarki aurefa? Daidai lokacin inno tashigo taganshi zaune akan gadonta, tafida ashe kana nan? Nima daga wurin mai martaba nake yakira ni yabani wani sako wurinka ras! Gabansa yafadi wato maganar faisal ta tabbata kenan ai kuwa tunda yake da

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});