Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yanmata, gyara kintsi bakuwar tafida alafiya dai gaba salamun baya salamun, ita dai zara'u gaba daya atsorace take domin bata san me zai biyo baya ba, yayinda kawayensu suna can suna ta gulmarta ita da hanfa to ko yanzu zara'u zai ce yana so? Inji wata acikinsu kudai jira muga dawowarta tukunna sakina tafada, zara'u suna zuwa office din tafida bafade yabude mata tashiga abinka ga jinin sarauta akishingide ta sameshi yana jiran zuwanta tana shiga yayi gyaran murya take fadawan sukayi waje suka ja musu kofa. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [6:39PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣6⃣ Na UMMI A'ISHA Fadawansa na fita ya kalli zara'u yana daga kishingide yace hv a seat zarah, babu musu ta zauna akan kujerar dake nesa dashi, kallonta yayi ina hanfa take? Hanfa tatafi gida, a ina gidan yake? Ya tambayeta, acan disina gidansu yake, dagaske ne ita kurma ce? Daga Kai zara'u tayi tace dagaske kurma ce sannan kuma bebiyace, murmushi yayi wanda yasake bayyanar da zahirin kyansa afili to yanzu ki taimaka min kibani address dinta zanje gidansu na sameta amma kuma naji tace min wai ita matar aurece hakane? Girgiza kai Zara'u tayi wlh bani da masaniyar hakan amma nima tabbas ta taba fada min cewar ita matar aurece amma ban yarda ba gaskiya, murmushi yayi hakane metake karanta a makarantar? Lab science take karanta, a school of nursing & midwifery dake cikin garin nan amma asalinsu yan garin disina ne, ok to ke tun wanne lokaci kika santa? Sanina da ita baifi shekara daya ba lokacin da muka shiga makarantar nanne kuma tunda muka fara kawance da ita har yau babu abinda ta taba yi min na bacin rai har gidansu naje itama taxo namu gidan, ok good yanzu ki rubuto min address din ki kawo min nagode amma zan kara nemanki idan bukatar hakan ta taso,daga kai zara'u tayi babu komai tashi tayi zata tafi murmushi tafida yayi nagode zarah amma agaskiya ina son kawarki sosai kuma zan aureta, murmushi zara'u tayi tace Allah ya tabbatar da alheri amin tafada tareda ficewa daga office din. [6:56PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣7⃣ Na UMMI A'ISHA Zara'u tana fita tafida yayi kishingide yazama tilas agareshi gobe yaje disina yabinciko gidansu hanfa, tashi yayi yafito daga office dinsa yanufi motarsa nan da nan su sarkin fada suka tattaso suka fara bin bayansu daidai lokacin zara'u tazo tamikawa tafida address din gidansu hanfa ko dubawa bai yiba yasaka takardar acikin aljihunsa ya wuce yana cewa thank u, ita kuwa zara'u tana komawa wurinsu sakina sakina tayi farat tace wai zarah me wannan gayen yake so awurinki ne? Dariya zara'u tayi address din budurwarsa ya nema kuma nabishi, dakyau sakina tafada cikeda bacin rai. Tafida yana zuwa gida yayi dukkan abubuwan da yasaba yi yafita kilisa yau kilisar tasu daga shi sai faisal, suna tafe ahankali akan dawakansu tafida yace abokina gobe zanje disina, me zakayi a disina? Akwai abinda zai kaini, ok to ko gidansu matar taka zakaje? Eh can zanje tafida yafada ahasale, dariya faisal yayi Allah yabaka hakuri abokina abin bana fada bane daga tambaya? Eh daga tambayar tafida yafada yana harararsa kasan Allah tafida? Ka nemi matarka ku sasanta tun wuri, tsaki tafida yayi haba faisal wayace adaura min auren da banine na bukata ba, wlh babu wani sasanci da za ayi ni yanzu ma aure zanyi wanda duniya zata san nayi aure amma wanccan auren ai na mai martaba ne murmushi faisal yayi to kuwa sai Allah ya tambayeka domin nauyin yarinya yana kanka tun daga ciyarwarta da shayarwata ga uwa uba hakkinta na aure tunda ita macece mace kuwa kasan tanada rauni, kuma duk duniyar nan kai kadaine zaka iya yi mata wannan domin babu wanda zai bata sai kai, uwar me zan bata? Tafida ya tambayeshi kafini sanin abinda zaka bata to ai kuwa sai dai ta mutu wlh dan banida lokacinta, dariya faisal yayi yace Allah ya shiryeka abokina, da haka suka juya suka koma gida. [7:18PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣8⃣ Na UMMI A'ISHA Suna komawa gida tafida yashiga dakinsu ya zauna yafara bincike acikin laptop dinsa wanda ni kaina ummi A'isha ban san me yake nema ba sai da ya dauki tsawon lokaci sannan yarufe laptop din nasa yanufi masallaci yana dawowa yadora daga inda ya tsaya yaci gaba da bincikensa har faisal yazo ya sameshi yafara yimasa hira amma shi tafida sama sama yake jinsa duk hankalinsa ya tattara akan binciken da yakeyi. Washe gari da misalin karfe 11 nasafe tafida yayi shirinsa tsaf cikin wani tsadadden boyel fari yasa hula yasha turaren fogg ya daura agogon azurfa kirar kamfanin omega yasa farin takalmi cover shoe yafito yayiwa mai martaba da inno sallama cewar yatafi disina duk babu wanda yasan abinda yatafi yi sai faisal amma su mai martaba basu tambayeshi me yatafi yiba kasancewar sun san garinsa ne shine yake mulkar garin, wata jibgegiyar jeep yashiga wadda akalla zata iya daukar mutum goma ita yashiga yazauna agidan baya sarkin fada yashiga gaba yazauna yayinda sarkin mota shikuma yazauna a mazaunin driver yaja suka tafi, tafiya sukayi ba mai nisa dayawa ba suka karasa garin disina, address din da zarah ta basu sarkin fada yarinka bi har suka isa wata unguwa mai suna gangare, anan sarkin fada ya tambayi wani yaro ko inane gidan su hanfa? Wancan mai koren fentin ne yaron ya nuna musu shidai tafida yana zaune abaya kishingide ajikin kujera yana latsa wayar hannunsa, adaidai kofar gidan sarkin mota yayi packing din motar yafito shima sarkin fada fitowar yayi ya isa bakin kofar gidan yafara kwada sallama sai da yayi sau wurin biyar sannan wani yaro yafito, yana amsa sallamar, yaro nanne gidansu hanfa? Eh nanne,tana ciki? Eh tana nan to kaje kace ana sallama da ita, to yaron yafada tareda juyawa cikin gidan da gudu, Jim kadan kuma sai gashi yadawo wai ance inji wa? Kace inji tafida, dagudu yaron ya sake komawa can sai ga wani mutum yafito daga cikin gidan waye yake nemanta? Mutumin yafada cikin fada, daidai lokacin tafida yafito daga cikin mota wazai gani? Sirikinsa yagani mahaifin matar da mai martaba ya aura masa. [7:50PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 3⃣9⃣ Na UMMI A'ISHA Bata fuska tafida yayi yasauko dakyau ya tsaya yana kallonsa dama shima sirikin nasa kallonsa yake, cikin murtukewar fuska mutumin yace, lfy kuka zo min gida? Cikeda isa tafida ya kalleshi amma baiyi magana ba sarkin mota ne yace barka da safiya dama yallabai ne yazo gurin yarinyar gurinka hanfa, wata harara mutumin yayi musu sai yanzu yasan da ita? Da lokacin da aka daura auren ya nemi inda take balle ace ya ganta, tunda aka daura auren nan bai san cinta ba bai san Shanta ba bai san sutturarta ba uwa uba bai san lafiyarta ya takeba dan haka nidai nayi dana sanin aura maka yata kuma nayi bakin cikin auran yata da kayi domin kai ba mutumin arziki bane bakada wata kama ta mutanen kirki,dan haka ina mai shawartarka da kadauki sahunka a likkafa tun dare baiyi maka ba kabar kofar gidana sannan kuma yazama tilas, dole ka saki yata domin bazan hada zuri'a da mutumin banza ba irinka dama na

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});