Chapter 2
Chapter 2
irin gadone nakarfe mai runfa fentinsa kalar ruwan hoda yasha lallausar katifa da shinfidu na alfarma ga kamshi mai dadi dayake tashi daga cikin dakin, barka da hutawa inno yafada yana wani lallausan murmushi, yawwa barka da zuwa tafida tafada tana murmushin itama, kallo daya zakayi mata kagane cewa mahaifiyarshi ce domin babu ta inda ya barta akama, kamarsu daya dashi kuma da alama tana jidashi sosai, macece mai fara'ar gaske kuma bata tsufa ba dan shekarunta bazasu wuce 45 amma bazaka taba gane hakan ba saboda jikinta bai nuna ba ko kusa, cikeda kulawa tace zakaci abinci ne yanzu? Kai ya girgiza tamkar wani karamin yaro yace a'a inno sai anjima yanzu bacci nakeji, to atashi lfy tafada tana murmushi,murmushi yakuma yi yakwanta akan gadon mahaifiyar tashi yaja filo yatasa kansa dandanan bacci yayi gaba dashi, tashi inno tayi takoma falo tazauna gudun kada azo adameshi yana bacci. 5⃣ Karfe 3:40 yatashi daga baccin da yakeyi yafito idonsa duk yayi kalar masu bacci afalo ya taradda inno tana salla dan haka bai tsayaba yawuceta yafita daga lungunta yanufi nashi yana shiga yafada toilet ya hada ruwan zafi yayi wanka yafito yasaka farar t. Shirt mai gajeren hannu yasa wando jeans baki yafesa turaren FOGG yafito yanufi masallaci lokacin dayaje har anshiga salla, yana idarwa ya fito ya wuce ma 'ajiyar dawakai yasamu an shirya masa dokinsa anyi masa shimfida an gyarashi domin fita kilisa bai bata lokaci ba yahau suma fadawansa wanda suka hada da sarkin fada, sarkin mota, da maja sirdi suka hahhau nasu suka fito daga gidan ahankali suke tafiya tacikin garin har suka fita suka shiga dokar daji, dama idan da sabo sun saba dan kusan kullum sai tafida yafita kilisa, kilisa tana daya daga cikin abubuwan da suke burgeshi a harkar sarauta, tafiya kawai suke suna shakar iskar dake ratsa dajin sannan suka billa tawata hanyar domin komawa gida alokacin mangariba takusa yi har ta kawo jiki, suna zuwa gida ana kiran salla, akasalance tafida yasauka daga kan kosasshen dokinsa yayi alwala yashiga masallaci ana idar da salla yafito adaidai lokacin wata hadaddiyar mota tashigo baka kirar croutoure mai tsananin kyau ajiki an rubuta TAFIDA 1 kallon motar yayi yai tsaki yawuce gaba, agabansa aka yi packing din motar aka fito wani saurayine wanda zai kaishi atsaye kuma ashekaruma bazai fishiba yafito daga cikin motar yana dariya Allah yaja zamanin tafida, batare da tafidan yayi masa magana ba yawuce yafara tafiya shikuma yabishi abaya har suka karasa sashen tafidan suka shiga, afalo suka zauna cikin muryar iyayi tafida yace wai kai faisal meyasa bakada mutunci ne? Motar tawa kadauka katafi yawon iskanci? Dariya yayi wanda aka kira da suna faisal yace haba abokina kaima iskancin nan kana dan tafabawa, fuska tafida ya yamutsa, ni bana wani iskanci kaine dan iska, ok naji ni dan iskane saboda ina neman mata kai kuma dan ganye? Filon kusa dashi tafida yadauka yajefeshi kai dan iska ne idan ni dan ganye ne ai dasauki tunda har yanzu ni saurayine cikakken saurayi kuma, dariya abokin nasa yayi dakyau virgin boy, amma dai abi ahankali banda ganganci,shiru tafida yayi bai kara magana ba domin shi baya doguwar magana idan kajishi yayi magana mai tsawo to da mahaifinsa ne ko mahaifiyarshi ko kuma abokinsa faisal. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [7:23PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE ! 6⃣ Na UMMI A'ISHA Tashi tafida yayi ya shiga daki yahaye gado yakwanta minti kadan faisal yabiyoshi cikin dakin abokina ya zaka kwanta bayan ba mugama magana ba? Kai malam bana son surutu, eh nasani ai shiyasa nake son na sanar dakai cewa na dauki wadannan kudin naka nayi sadaka dasu, tsaki tafida yayi mtwww to ina fata ba iskanci kaje kayi da kudina ba? Murmushi faisal yasake yi wai kai finka laifi nayi? Kaima fa mai laifi ne, kana shan ganye over ni kuma ina neman mata jifa jifa ba koda yaushe ba, murmushi tafida yayi yatashi zaune, to ai ni matan ne ma tsoronsu nake, gaba daya ban san ta inda zanbi ba yanzu haka idan ka ajiye min mace wlh ban san yadda zanyi da itaba, wata irin dariya faisal yayi hahahaha! Ammafa kacika dan rainin wayo, ta ina kake karbar haihuwa? Kaida ka karanci mata kasan yadda suke, karfa ka manta kai likitan matane su kake gani kake dubawa akoda yaushe, dan malalacin murmushi tafida yasaki to sai aka fada maka kuma nasan hanyar? Karya kake kasani mana, dariya tafida yayi kai dan iska ne, wlh duk ranar da mai martaba yasan kana neman mata sai ya tube rawanin da ya daura maka,cikin dariya shima faisal din yace kamar yadda kaima mai martaba zai tube rawanin daya daura maka ba duk ranar da yagane kai mugun dan ganye ne, murmushi tafida yayi ra'ayina shine nasamu cikakkiyar budurwa kamar yadda nake cikakken saurayi, taba baki faisal yayi eh munji kai saurayine amma ai dan ganyene, dariya tafida yayi duk da haka dai nafika,ni yanzu ma ka kyaleni wlh yunwa nakeji sai da inno tace naci abinci dazu nace bacci zanyi amma bari nayi mata waya akawo mana, wayarshi ya dauka kirar yota phone yakira inno yace akawo masa abinci shida faisal ba awani jimaba sai ga kuyangi guda 2 sun shigo hannuwansu dauke da tirarrika na silba manya manya anan suka ajiye suka fita, suna fita faisal ya fara bubbude kwanukan abincin, abinci ne kala kala na gargajiya saukowa tafida yayi suna ci suna hira har suka gama, suna gamawa suka tafi masallaci sukayi salla suka shigo gida afalo faisal yazauna yafara waya da yanmatansa shi kuma tafida yawuce daki yafada kan gado yajanyo tabar wiwi yafara zuka. 7⃣ Washe gari dasafe dr tafida yashirya tsaf cikin shirinsa nafita office bakin wando yasa da bakar t.shirt mai dogon hannu yadora jar jacket asama yasa bakin takalmi cover shoe [7:38PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: Yafesa turaren fogg yafito lokacin faisal yanata bacci kasancewar shi a ministry for local government yake aiki baya fita dawuri shikuwa tafida 7:30 yasaba fita office, yana fitowa sarkin fada da sarkin mota sukazo suka zube suka fara zabga kirari barka da fitowa mazajen fama hadiri sa gabanka inda kakeso, murucin kan dutsi baka fitoba sai da ka shirya, atafe dakyau, atsaye dakyau amma azaune kafi dadin kallo dan ahmadu jikan sani gyara kintsi giwa kinfi karfin waiwaye, kura ko kin mutu kinfi karfin kare, wani kaya sai amale wane jaki, cikeda takama yace barkanku da safiya yawuce cikin gida yanufi dakin inno mahaifiyarshi alokacin har ta harhada masa kayan karyawarshi tsaf ta zuba acikin akushi mai kyau tana jiran shigowarsa, yana shiga yazube agabanta tana kushingide hannunta rikeda carbi tana ja sukuma bayinta har sun fara aikace aikacen da suka saba yi, barka da asuba inno yafada idonsa akasa, barka da tashi tafida, kafito lfy? Lfy lau inno, to Allah yabada sa'a, Allah ya tsareka, Allah yadawo dakai lfy, amin inno nabarki lfy, tashi yayi yafita yanufi sashen mai martaba lokacin shima yana zaune afalonsa yana karatun alqur'ani mai girma, cikin girmamawa tafida yadurkusa barka da asuba ranka yadade, cikin murmushi yace yawwa ibrahim har anfito? To Allah yatsare Allah yabada sa'a, amin mai martaba yafada yatashi yafita inda aka adana motarsa yanufa aka bude masa gidan baya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36