Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

za akwace masa ita. Yauma hanfa zaune take a makeken falon gidansu kasancewar tafida yabawa babanta gidan da yagina a gonarsa kuma gidan babba ne gashi yasha kayan alatu, daga ita sai daurin kirji gabanta da kaskon turaren wuta tana turara jikinta da turare mai kamshi Wanda ni kaina ummi Aisha sai da naji kamshin ya ratsani, wayarta ce tayi kara murmushi tayi tun kafin ta daga domin tasan tafidane yau tun safe bai ber kunnenta ya huta ba, hello munib tafada ahankali, gaskiya ni ban yarda ba ki canja min suna, dariya tayi kabari sai nazo gidanka sannan zan canja maka sunan, murmushi yayi to shikenan ai saura kwana biyu, dariya tayi anjima zan kiraka, haka suka gama wayar suna cikeda shaukin juna. Washe gari aka zo aka dauki hanfa daga,nanfa ta shiga kukan rabuwa da iyayenta duk kuma sai taji hankalinta ya tashi duk da irin son da take yiwa tafida,dakyar aka banbareta daga jikin mahaiyarta, kuka take kamar me har aka sata a mota, momcy ce tafara lallashinta kiyi hakuri kinji hanfa kowacce mace dole sai haka ta faru da ita hakuri zakiyi dakyar tayi shiru da haka sukaje garin misau nan taga garin yacika dam da mutane babu wurin masakar tsinke, cikin gidan aka wuce da ita kai tsaye dakin momcy aka kaita nan aka zaunar da ita, basu jima da zuwaba sai ga zarah ma an kawo ta nan ta danji sanyi, momcy da kanta ta kawo musu kayan karin ni'ima tabasu wadanda yawanci an hadasu da madara ga kazar amare, dakyar hanfa ta iya ci domin har yanzu kuka take dama dama zarah ita tayi shiru koda aka kawo musu abinci hanfa kasa ci tayi. [7:33PM, 11/30/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 9⃣8⃣ Na A'ISHA (UMMI) Karfe biyu daidai momcy tashigo musu da kayan da zasu sa domin za ayi musu cuda wato bikin al'adar da aka saba gudanarwa indai ana biki agidan sarki, wata mata aka kawo mai kwalliya wadda ta tsara musu kwalliyarsu ta daukar hankali pink din leshi suka saka da gwaggwaro pink da takalmi shima pink sai yar karamar jakar hannu ga gwalagwalai da aka zuba musu tun daga wuyansu har abin hannu, fito dasu aka yi aka kaisu inda za agudanar da bikin wanda iya matane suka halarcin wurin nan da nan masu kidan kwarya suka fara kida suna rera waka, inda aka tanadar musu aka kaisu suka zauna tuni aka fara gudanar da cuda abin gwanin sha'awa sai turare kuyangu suke fesawa awurin nan aka gama aka mayar dasu cikin gida, tunda tazo bata ga tafida ba asalima rabonta dashi tun lokacin dayaje wurinta a makaranta, shi kam tafida yana can bakinsa har kunne sai washe hakora yake za akai masa hanfa gida, gashi yana son yaganta amma yana kunyar shiga cikin gidan saboda yasan acike yake da mata, daki yashiga yadauko iPhone dinsa ya kunna yafara lalubo hotunan da yayarsa daso ta daukar masa na hanfa dan takanas ya bata yace ta dauko masa hotunan hanfa har agama bikin, nafarko yafara gani tana gyara agogon hannunta ta sunkuyar da kanta lokacin acikin dakin momcy ne, wani yasake budewa shi kuma tana yiwa zarah magana sai na uku lokacin har anje gurin cudar, haka yayita kallon hotunan nata kwalliyarta tayi bala'in yi masa kyau komai pink murmushi yayi hanfa kenan komai nata mai kyaune, fuskarta yaci gaba da kallo ajikin wayar duk hotunan babu wanda bai yi masa kyau ba amma yafi ganin kyan wanda ta tsaya afilin rawa sai dai da alama ba rawar take ba, murmushi yayi hanfa tanada kunya yasanta yarinyace mai kunya gata da ganin girman nagaba da ita ya tabbata zasu yi rayuwa mai dadi da ita. Washe gari aka fara shirin tafiya daurin auren faisal da zarah wanda za a gudanar agarin disina, tafida shine akan komai har akaje daurin auren aka dawo lokacin karfe 2:30 ana dawowa aka fara shirin tafiya hawan dawakai da za agabatar wato (kilisa). [8pm, 11/30/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 9⃣9⃣ Na UMMI A'ISHA Yauma kwalliya aka tsarawa su hanfa cikin wani tsadadden material wanda kudinsa nikaina ummi ban san adadinsu ba amma naga sai kyalkyali suke kalarsa golden yasha ado sosai, gwaggwaro coffee colour aka sa musu da takalmi da yar jaka duk kalarsu coffee colour, sarkarsu itama golden ce da abin hannu da warwaro, motoci aka kawo aka daukesu cikin wata jibgegiyar jeep kirar Toyota, suna zuwa wurin ga kujeru nan an tsarasu kowannesu an tanadar musu wurin zama ita da angonta wato jama'a kyan da hanfa tayi a wannan rana abin ba acewa komai tayi kyau nagaske, suna nan zaune an kunna wakar "lokacinkine amarya yar amana........ Aure ibada ne" ga kawayensu yan makarantarsu sai zuwa suke kasancewar zarah tayi inviting dinsu, shiru hanfa tayi tanata kallon jama'a sai hada hada suke yayinda kawayensu suke zuwa suna ta daukar hoto da ita wasu kuma suna daukarta ita daya, anan nan anata gudanar da bikin sai ga tawagar angwaye akan dawakai nanfa wuri ya rude da guda daidai lokacin aka sauya waka aka kunna wakar "Ran rabuwa ake yin kuka inna da baba sai watarana ku yafen dukkanin laifina zan tafi dakin aurena" hanfa ji tayi kamar ta fashe da kuka amma ta daure sai dai duk da haka kwalla taciko idonta, kallon wurin tayi yakayatu mutuka harta decoration din wurin coffee & golden ne kalar shigarsu itada zarah, daidai lokacin ta hango tafida yana saukowa daga kan dokinsa yana sanye da shadda light brown yasha rawani da alkyabba, hannunsa rikeda sandar sarauta yanufo mazauninsa, dauke kanta tayi daga kallonsa har ya karaso yazauna shima faisal yaje ya zauna, yana zama yaji kamshin turarenta da humrar data shafa sun taru sun cika masa hanci ga wani kyau datayi kamar aljanna lallai sai yau ya yarda da maganar bature da yace black is beauty & unique, idan kana son ganin kyau na hakika to ka kalli bakar mace,kallonta yayi amma sai yaga ta dan rame, hannunta ya kama yafara murza yan yatsunta su kuwa masu video camera da masu hoto sai daukarsu sukeyi tunda suka zauna, ahankali yace maman baby ya naga kin rame? Bakya cin abinci ko? Murmushi tayi babu komai,to meyasa kika rame? Ni ban rameba tafada cikin shagwaba to ki kwantar da hankalinki kinji, nasan abinda kika saka aranki har kika rame, murmushi tayi batace komai ba tana jinsa yanata wasa da yan yatsunta sai shafa kunshin hannunta yake amma koda ta kalli su faisal sai taga su abin ba haka yakeba ko kusa da zarah bai jeba balle ya tabata, kallon tafida tayi tace kaga fa mutane sai kallonmu sukeyi. [5:06PM, 12/1/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 1⃣0⃣0⃣ Na UMMI A'ISHA Murmushi tafida yayi ya matsa yatsun hannunta dakarfi yace to meye? Su kallemu mana and so what? Cigaba da murza yatsun hannunta yayi har aka gama program din aka tashi, tundaga lokacin duk inda ka leka a social ntwk babu abinda zaka gani sai hoton tafida da hanfa an rubuta Tafida & his beautiful wife hanfa@ hawan angonci day, kar kuso kuga comments da likes da suka rinka samu,nikaina ummi A'isha sai da abin ya burgeni har nayi comment, can nahango yan uwana marubuta suma sunyi comments babu adadi. Bayan

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});