Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Alheri Danko Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwance inda ya barta rigarshi yadauka wadda tagama yin squeezing kallonta yayi cikeda tausayawa amma sai ya fuske yace kitashi ki shirya kifito na maida ki makarantar yana gama fadin haka yafita yana kokarin saka rigarsa, yana fita tatashi dakyar ta jawo kayanta tasaka duk idonta yayi hulu hulu kamar wadda yayiwa mai gaba daya, tsaki tayi wlh bazan ma shiga ko toilet din ba idan nakoma school nayi wankan, hijabinta tadauka tasa ta tashi tana cewa ko haka ka barni nayi hankali daga yau bazan kara rainaka ba kuma bazan sake kin bin umarninka ba, afalo tasameshi yana zaune yana shan lemo tsayawa tayi har yagama yace zaki sha lemon? A'a bazan sha ba tafada, tashi yayi yace to zo muje, bin bayansa tayi suka fita ya bude motar suka shisshiga suka zauna sannan ya tada motar sai da suka fita da gate din gidan sannan yace bana son nakara ganinki cikin maza, to tafada tun kafin ya rufe bakinsa har abin yaso bashi dariya saboda yadda yaga yanzu tafara tsorata dashi alhalin shi kuma ba wani abu nakuzo ku gani yayi mata ba, hannunta yakama yasarke cikin nasa, ki rinka saka dogayen rigunan nan kinji? Eh naji zan rinka sawa, kissing din hannunta yayi. Ayshkaus oasis yanufa yayi packing yafita yashiga Jim kadan yafito hannunsa dauke da leda yashigo ya zauna ita dai hanfa mamaki tafida kawai yake bata dan binsa da ido take tayi duk abinda yayi burgeta yakeyi, kuma yanzu ta gane tafida gwarzo ne ba kadan ba, school of nursing yashiga ya tsaya akusa da gate din hostel,kusa da ita ya matsa nan idonta yayi tsuru tsuru kirjinta yashafa yace nifa ba komai zanyi miki ba, daga yau ina jin bazan sake shigowa ba sai nan da bayan 2 weeks saboda munata shirye shiryen bikine, ki kula da kanki kinji? Kai ta daga insha Allah, ledar ya mika mata yace kigaida zarah, zataji tafada tabude motar tafita tashiga hostel tana shiga hostel ta shiga dakinsu lakacin duhu yayi dan har isha'i takusa, tana shiga ta ajiye ledar ta fada kan gado kallonta zarah tayi mrs tafida lfy? Lfy lau hanfa tafada tareda tashi ta dauki bucket tafita taje tuka tuka tadebo ruwa tadawo tazo tacire kayanta tadaura zani tasa hijab tadauki soup case ta kinkimi ruwan tanufi bathroom dariya zarah tafara yau dai duk yadda akayi tafida yayi babban aiki, wanka tayi tai alwala takoma daki tafara shiryawa nan zarah tafara tambayarta wai me kika kawo mana ne? Duba kiga zarah dan nima ban san menene ba, ko sallar magrib banyi ba, sallaya tashinfida tayi sallah sai data idar sannan zarah tafara kokarin bude ledar wadda nikaina ummi na kagu naga abinda ke ciki. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:01PM, 11/23/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 6⃣6⃣ Na UMMI A'ISHA Tana budewa taga drinks kala kala da fresh yo milk, da snacks dangin su miet fie da cake da spring rolls, da sauransu ga robar ice cream nan guda 2 da gasasshiyar kaza katuwa, nanfa ummi Aisha taji yawun bakinta ya tsinke, murmushi zarah tayi kawata irin wannan kaya haka? Lallai yau duk yadda akayi kin jiyar da tafida dadi dan naga kina dawowa da wanka kika fara, harararta hanfa tayi kin manta, ato ai gaskiya ce tunda ni dai nasan ba mensuration kikeyi ba kalau kika fita yanzu kuma gashi kina dawowa kin fara da bath, zarah tafada tana dariya murmushi hanfa tayi zarah kece abar dariya amma bani ba domin ni yanzu nafara sanin rayuwa ke kuwa babu abinda kika sani amma ina addu'ar Allah yakawo aurenki nan da wata 3 yadda kema zaki dandana kiji yadda naji, dariya zarah tayi amin ga kayan dadinki kizo kici, fara ci ina zuwa. Tafida kuwa yana zuwa gida yawuce dakinsu lokacin faisal yana nan yana shiga yawuce toilet yayi alwala ya fito yahau kan dadduma yatada kabbarar salla, sai da ya idar faisal yace mutumina yau da wa kukayi dambe ne? Naga kayanka sunyi squeezing,dariya tafida yayi bakada mutunci ni banyi kokawa da kowa ba tunda kasan ni ba dan iska bane, dariya faisal yayi zaka fadi gaskiya shiru tafida yayi yafara tunanin kodai yafadawa faisal yarasa hanyar ne? Ai faisal dan uwansa ne kuma amininsa babu abinda bazai iya fada masa ba, kallon faisal yayi, abokina wai a ina hanyar nan take? Dariya faisal yafara yi harda kwanciya sai da yagama kular da tafida sannan yace amma kai yarone wlh nan yafara wata dariyar tashi tafida yayi yahau kan gadonsu yajawo laptop dinsa yabude yafara binciken female reproductive system, shi kuma faisal sai aikin dariya yake, tsaki tafida yayi yadauki wayarsa yakoma falo yafara kiran zarah, tana ganin shine ta mikawa hanfa wayar, ahankali hanfa tayi magana hello! Hello yafada yakike? Lfy lau, ya gajiya? Shiru tayi tafara murmushi, ok dama kira nayi nai miki sannu, kinyi kokari sannu kinji Allah yayi miki albarka yanzu ki kwanta ki huta, to nagode hanfa tafada ahankali, I luv you yafada, nagode tafada takashe wayar. [2:52PM, 11/25/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗ 6⃣7⃣ Na UMMI A'ISHA Tun daga lokacin tafida bai sake zuwa makarantar su hanfa ba saboda kullum yana busy bashida lokacin kanshi kullum suna hanya shida faisal mai martaba yana aikensu sukai invitation amma kullum sai ya kirata yaji lafiyarta, tunda bikin zumunta ya rage saura kwana 3 tafida da faisal suka tafi kasar Morocco inda suka iyo siyayyar kayan da za ayi hawa dasu. Kwanansu daya suka dawo suna zuwa suka samu garin misau yacika dam da baki mahalatta bikin zumunta ga gari ya rude da kide kide da bushe bushe gamida raye raye nanfa su tafida aka fara tsare tsaren yadda bikin zai gudana. Ranar asabar da misalin karfe 3 shine lokacin da aka fara gudanar da bikin dukkan hakimai sun harhadu kowa yahau dokinsa da yan tawagarsa, gidan sarki kuwa yawan mutanen dake ciki ba agano adadinsu alokacin sarki yafito daga cikin gida yahau dokinsa, shi kuma faisal tawagar tafida yabi, lokacin da aka fito daga gidan sarkine aka hau titi da niyyar zagaya garin missau gaba daya kaf domin sarki yagana da talakawansa. Hanfa tana kwance adaki zarah sulaiman tashigo tace mrs tafida tashi mutafi bakin gate kallon hawa ance tana nan zasu wuce, shiru hanfa tayi azahirin gaskiya tayi missing din tafida sosai kuma tana son ta ganshi, tashi tayi tacire kayan jikinta tasaka wata Arabian gown blue tasa dan madaidaicin hijabi suka fita, abakin titin kofar makarantar suka tsaya inda daliban duk suka firfito kwansu da kwarkwatarsu domin kallon sarki kai harma da baki wadanda ba yan makarantar bane, tuni wuri ya rude da ihun dawakai da kide kide da algaita, tawagar chiroma ce tafara wucewa sannan sai ta sa'i dukkaninsu yayun su tafida ne, sa'in misau yana wucewa sai ga tawagar tafida nanfa yan mata suka hau shewa harda masu yin guda domin yawancinsu shi sukazo kallo,tafida kam yasha kyau tun daga kan kwalliyar dokinsa wadda ta kasance anyita da jajayen yadika masu kyalkyali, sirdin dokinma Jane komai dai najikin dokin ja akasa masa, shima tafida fararen Kaya yasa yadora jar alkyabba asama aka nada masa jan rawani takalmin kafarsa ja ga wani bakin glass dayasa gaba daya fuskarsa arufe take saboda rawanin har fuskarsa aka nade gashi

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});