Chapter 12
Chapter 12
aura maka yatane dan mutuncin mahaifinka to yanzu nafasa, yana gama fadin haka yakoma cikin gida tareda doko kofar gidan da karfi, sai asannan tafida ya iya motsawa daga mutuwar tsayen da yayi dama hanfa itace matar da mai martaba ya aura masa? Wata zuface ta fara karyo masa kamar an kwara masa ruwa ga kafarsa tayi wani irin nauyi marar misaltuwa, ahankali ya zare gilashin dake idonsa yafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai yafashewa aciki, batare da tsoro ba yatura kyauren kofar ya shiga gidane na talakawa babu yabo babu fallasa komai na cikin gidan irin na talakawa ne,yana shiga ya fara sallama tamkar mai yin rada, zuruf masu gidan suka fito daga daki baban matarsa ne yataso cikin fada, waye yayi maka izinin shigowa cikin gidana? Kai kafita daga idona yanuna shi da yatsa nadade da sanin kai marar kunya ne kuma bakasan mutuncin nagaba da kai ba, kafitar min daga cikin gida tun kafin nayi maka kamun kazar kuku, cikin rawar murya tafida yace baba zan fita amma sai ka bani matata, kar ka kuskura kasake kirana da baba domin baka daukeni uba ba kuma nima duk cikin yayana babu mai wulakanta mutane wanda bai san darajar mutane ba, kayi hakuri baba amma dan Allah kabani matata tafida yafada tamkar zai fashe da kuka, wai wacce matar yake fada? Wata mata ta tambaya cikin fada, wannan akwai marar kirkin yaro, sai yanzu kasan da matar taka, yau auren naka yafi wata 6 ko sau daya baka zo kaganta ba saboda kana gadarar kuna da sarauta? Kai gaka dan gata to mu bamu da sarauta amma Allah shine gatanmu, nuna masa hanya baban hanfa yayi fice min daga cikin gida marar kunyar banza marar kunyar wofi, cikeda rashin karfin jiki tafida yajuya yafita yayinda mahaifin hanfa yabiyoshi yayi masa korar kare, dakyar tafida yashiga mota yacewa su sarkin fada sushiga su koma misau take suka bi umarninsa. [8:28PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣0⃣ Na UMMI A'ISHA Gudu sosai sarkin mota yayi amma tafida gani yake kamar ba tafiya sukeyi ba alla alla yake yaga sun isa garin misau, wani jiri yaji yana daukarsa wannan abin al'ajabi da yawa yake, tun farko dayasan wannan kurmar ce matarsa ai da ya amince, to ai sai da mai martaba yabaka hotonta amma kaki gani, shiyasa aka ce komai idan aka bishi a sannu yafi armashi zuciyarsa tafada masa, gefen kansa yaji ya sara kamar wanda zai tsage gida biyu, da sauri yasa hannunsa ya rike, sai yanzu yasan wulakanci bashida rana gashi yanzu yanaji yana gani yataho yabar hanfa batare da yaganta ba, amma da ace alheri yayiwa mahaifinta tun farko da bazai yi masa wannan cin mutuncin ba domin shi ALHERI DANKO NE! Baya faduwa akasa banza ko baka samu alokacin ba to agaba zaka dauki abinka watikil ma harda riba, wayarshi yadauka yafara kiran number faisal bugu biyu faisal yadaga abokina ya? Kana ina faisal? Ni gani a office kaifa kadawo daga disinan ne? A'a nakusa zuwa dai yanzu gamu acikin azare dan Allah kadawo gida nafi son da nazo nataradda kai agida pls abokina, ok dama nima nagama aikin da nakeyi yanzu zan koma gida, Allah yadawo daku lfy amin faisal, tafida yafada yakashe wayar, kansa yadafe yana ji kamar zai bar jikin wuyansa dakyar ya iya mikewa ya kwanta akan kujerar da yake, gudu sarkin mota yakara dan danan sai gasu acikin disina, suna isa gida tafida yatashi yafito anan yabar gilashinsa da wayoyinsa, sai sarkin fada ne ya dauko masa, yana shiga dakinsu yasamu faisal zaune yana waya kusa dashi yazauna faisal yagama wayar ya jiyo gareshi yace abokina kadawo? Kai tafida yadaga yace nadawo sai dai yau nayi dana sanin aikata kuskure da sharri arayuwata faisal hakika nayi kuskuren aikata sharri hakika faisal sharri jakada ne maishi yake dawowa yayinda shikuma ALHERI DANKO NE bazai taba faduwa abanza ba, kallonsa faisal yayi wai meya farune? Cikin damuwa tafida yace faisal yarinyar da nake baka labari ashe itace matar da mai martaba ya aura min sai yanzu da naje gidansu na tabbatar da hakan, dariya faisal yafara har da saukowa kasa daga kan kujera nan ran tafida yakara baci sai hawaye sharr! Cikin sauri faisal ya daina dariyar yace haba abokina be a man mana, ya zaka rinka kuka kamar mace, faisal ina sonta nd i can't do with out her! Hannunsa faisal yarike yace maza tashi muje wurin mai martaba mu rokeshi yabaka matarka, tashi tafida yayi yabi bayan faisal har suka isa fada kuma fadar acike take makil da alama sarki yana ganawa da yayun su tafidan ne, turakin soro shine yayi musu iso wurin mai martaba, a kasalance suka isa cikin fadar nan suka matsa gaban mai martaba suka yi gaisuwa caraf fadawa suka cafke,sarki ya gaisheku samarin alheri, sarki ya amsa gaisuwarku mazajen fama, tafiya dai sannu sannu kwana nesa. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:52AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣1⃣ Na UMMI A'ISHA Cikin fargaba faisal yace ranka yadade akwai abinda yake tafe damu, gyaran murya mai martaba yayi nan da nan fadawansa suka fice daga cikin fadar sai iya su chiroma da galadima da sa'i kawai aka bari awurin,cike da jin nauyi faisal yace ranka ya dade dama tafida ne yace yatuba yanzu yagane abinda yayi bai kyauta ba shine muka zo mu nemi afuwarka ayi hakuri abashi matarsa, cikin fada sarki yace kai! Idan ku shashasu ne to ni ba shasha bane, dama wannan ce maganar da ta kawo ku? Maza kutashi kubar wurin nan tun kafin raina ya baci, hakuri faisal yafara bayarwa yayinda shikuma faisal yakasa furta koda kalma daya in banda fararen idanuwansa da suka rine sukayi jajawur, cikeda fushi galadima yace kai! Akace kutashi ku bawa mutane wuri marassa kunyar banza, tashi faisal yayi yaja hannun tafida suka fice daga cikin fada, suka tafi wurin inno, afalo suka tarar da ita tana zaune kuyanginta zagaye da ita, rai abace tafida ya zauna kallonsu tayi ya akayi naganku duk kunyi wani iri, inno bukata ce take tafe damu inji faisal, kuyangunta ne suka tashi suka fita,meya faru? Inno ta tambaye su, inno daga wurin mai martaba muke dan Allah kisa baki adawowa da tafida matarsa ai abinda ya wuce ya riga ya wuce, au dama wannan ce ta kawoku? To maza ku tashi kubar min dakina kuma kar ku kara tunkarata da wannan maganar kunji dai na fada muku marassa kunya kawai, tana gama fadin haka ta mike tashige dakinta nanfa tafida yaji kansa ya sara, jan hannunsa faisal yayi taso muje wurin momcy bai yi musu ba yabi bayansa har fannin momcy, suna shiga lokacin tana kokarin fitowa ganinsu yasa takoma ciki suka bi bayanta, tafida me yafaru? Ta tambayesu faisal ne ya iya yi mata bayanin abinda ya faru nan tafara kwantarwa da tafida hankali, kar kadamu tafida insha Allahu komai zai zo da sauki kaji, kayi hakuri zanje nasamu mai martaba saboda dama yanzun nan wurinsa zanje jakadiya tace min yafito daga fada, kujirani naje nadawo yanzu, tashi tayi tafita zuwa sashen mai martaba. [9:53AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 4⃣2⃣ Na UMMI A'ISHA Koda momcy taje wurin mai martaba hakuri tafara bashi akan maganar tafida ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36