Chapter 6
Chapter 6
A'ISHA Laptop dinsa yabude yashiga email dinsa anan yaci karo da wani sako daga kungiyar litocin mata ta duniya ta shirya musu wani course har na tsawon wata 5 kuma har dashi aciki zasu gudanar da course din ababban birnin kasar India wato Mumbai dadi yadanji domin dama garin yayi masa zafi da azamarsa yatashi yanufi maternity domin duba halin da suke ciki. Tunda yadawo daga office yakule adaki shi kadai yafara cike ciken takardun tafiya course dinshi anan faisal yazo yasameshi abokina dama kana ciki, eh gani kaganni kuwa, akusa dashi faisal yazauna me kakeyi? Wlh wani course zan tafi na 5 months, kai dazakayi aure wanne course kuma zakatafi bayan ga babban course zaka samu duka tafida yakaiwa faisal yace zan yimaka rashin mutunci wlh, dariya faisal yayi duk tsiyarka dai ana daura maka aure kazama bazawari,waya fada maka? Wlh karya kake kaine bazawari amma ni virgin ne dariya faisal yayi ai mun kusa muga karshen virgin domin virgin zai koma disvirgin dariya tafida yayi yace ka karaci iskancinka kagama akwai ranar ramuko. Tuni aka fara shirye shirye agidan mai martaba har an hada kayan aure irin na al'ada dana zamani ankai gidansu amarya kullum bushe bushe da raye raye akeyi agarin mai girma tafida zai angwance,ni ummi Aisha hannuna asama nace Allah yaja zamanin mai girma tafida, tunda aka fara shirin biki tafida baya shiga sabgar kowa agidan tsakaninsa da kowa gaisuwa ce daga angaisa shikenan dama can shi ba mai magana ba da faisal kawai yanzu yake magana mai tsawo shima faisal din dan bazai iya fushi dashi bane saboda sun shaku sosai, amma ko inno da mai martaba tsakaninsu gaisuwa ce yadda suke fushi dashi shima haka yake fushi dasu, ana igobe za afara gudanar da biki yafara shirye shiryen tafiyarsa India domin nan da sati 2 zasu fara gudanar da course din mai taken yaki da cutar sankarar mama (cancer),shi dai faisal shine yazama tamkar angon domin komai wanda ango yakeyi shine yayi, shikuma tafida hakan ko ajikinsa tashi yayi yaje wurin mai martaba yayi masa maganar tafiyarsa India maimartaba bai damuba yace babu matsala dama itama amaryar taka karatu takeyi koda tana nanma nace babu maganar tarewarta yanzu tunda bakaso duk lokacin dakaso ta tare nan gaba, dukar da kai tafida yayi yace godiya nake mai martaba Allah yakara nisan kwana yatashi yafita. [8:41PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 1⃣9⃣ Na UMMI A'ISHA Yana fita yayi kicibus da faisal kallon faisal yayi yadauke kai domin yafuskanci faisal ya zake akan auran nan, cikeda dariya faisal yaja hannunsa mutumina ya akayi? Shiru yayi kamar baijishi ba cikin zolaya faisal yace wai kai duk dokin zaka samu hanyar ne ya hanaka magana? Sai alokacin tafida yayi murmushi wlh kai wannan yadama ni yanzu ba wannan ne agabana ba, dariya faisal yayi zo muje abokina kaji hannunsa yakama suka nufi cikin gida har dakinsu suka zazzauna faisal ya dubeshi yace dan Allah tafida ka tsaya ka nutsu ka rungumi matarka shifa aure mukaddari ne, cikin jin haushi tafida yace me zai hana kai ka rungumi kaddarar ka aureta? Dariya faisal yayi ai ni ba abani bane amma kai kaga da yake dan gatane aure za ayi maka kasha sha'aninka tsaki tafida yayi yajawo earphone dinsa yajona ajikin wayarsa yafara shan sauti dariya faisal yayi yace kadai kusa ka zama bazawari, jin shiru tafida bai amsa ba yasashi gane cewa bai ji abinda yace ba domin dayaji da sai ya bashi kyakkyawar amsa domin babu abinda yatsana irin yaji yakirashi da bazawari tashi faisal yayi yafita yana dariya. Shirye shiryen biki ya kankama yayinda shi kuma tafida yaketa shirye shiryen barin kasar, ranar alhamis aka sanya amarya a lalle faisal shine yake tsaye akan komai kullum baya samun lokacin kansa daga nan zai yi nan gidan mai martaba kuwa ya cika yayi dam da al'umma garin in banda kade kade da raye raye babu abinda akeyi domin sarki zai aurar da dan autansa kuma dan gaban goshinsa amma shi tafida in banda fushi babu abinda yakeyi gaba daya yadaina walwala yazama marar fara'a gashi kullum sai sunyi fada da faisal, ranar juma'a aka fara niyyar daura auren tafida amma kememe yaki kirshayawa. [9:05PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 2⃣0⃣ Na A'ISHA (UMMI) Babu yadda faisal bai yi da tafida ba kan ya shirya su fita domin da misalin karfe 1:30 za adaura auren amma yaki yarda yatashi ya shirya tun faisal yana yimasa cikin lallami har yafara fada shiru tafida yayi masa bai tanka masa ba, ganin haka yasa faisal yakara tunzura ya hasala yafita daga dakin, lokacin har su mai martaba sun tafi inda za adaura suren, faisal shi kadai yatafi yasha fararen kaya masu tsada yana zuwa lokacin wurin yacika makil amma haka yasamu ya kutsa ya isa wurin mai martaba sarki yana ganinsa yafara tambayarsa ina tafida cikeda damuwa yace ranka yadade bashida lafiya ne bazai iya zuwa ba, cikin fushi mai martaba yace yayi daidai kuma rashin zuwansa bashine zai sani nafasa yimasa wannan auren da nayi niyya ba, hakuri faisal yafara bawa sarki tuba muke ya mai martaba ayi mana uzuri,galadima ne ya matso yace ranka yadade ni ina ganin afasa daura auren nan da tafida abawa faisal, girgiza kai sarki yayi a'a galadima banki ta takaba amma nidai da tafida zan daura auren nan, nan aka fara daurin aure waliyyan amarya sunzo aka daura auren tafida da amaryarsa akan sadaki naira dubu dari, ana gama daurin aure sarki yakira uban amarya gefe yafara yimasa bayani kan cewar amarya ba yanzu za akawota ba sai lokacin da yayi magana gyada kai mahaifin amaryar yayi tareda yiwa mai martaba godiya, ana kammalawa faisal ya koma gida afalo ya taradda tafida kwance yana danna wayarsa dariya faisal yafara yi yamikawa tafida hannu assalamu alaikum mr ango harara tafida ya cilla masa yayi tsaki wata dariya faisal yayi mr ango asamo hanya lafiya amma banda rashin imani dan wlh idan kayi mata takarfi zaka iya kasheta, tashi zaune tafida yayi wlh faisal kar ka kaini bango, ya isheka, murmushi tafida yayi daga fadar gaskiya? Allah yabaka hakuri gyara kayanka baya zama sauke mu raba, murmushi tafida yayi yau kam yazama amma kabari duk lokacin dana nemi hanyar narasa zan nemi taimakonka, zama faisal yayi bawani nan dama can kasan inda take, wai kai sau nawa zan fada maka ne? Wlh Allah ni ban san ta inda take ba kai nifa ko haihuwa idan zan karba bana tsayawa naduba kawai aikina nakeyi dariya Faisal yayi to congratulations yanzu zaka gane ta inda take sallamar jakadiya ce ta katse musu hirar tasu. [1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:27PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE! 2⃣1⃣ Na UMMI A'ISHA Har cikin falon jakadiya tashigo tarussuna barkanku da hutawa samarin kwarai tafida ta kalla ranka yadade mai martaba yana kira tana gama fadin haka tajuya tana cewa afito lafiya, tashi tafida yayi yafita shikuma faisal bai bishi ba domin yasan fada zaisha awurin mai martaba yana tsoron kar yaje ahada dashi, tafida yana isa dakin mai martaba yasameshi shida inno da momcy zazzaune gabansa wuri yasamu yazauna gabansa yanata harbawa, cikin fada mai martaba yafara magana ibrahim ka raina kowa agidan nanko? Kanuna mana mu bamu isa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36