Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
Download Book

jin zafi yakara tarwatsata a kasa duk tafashe a dakin, karar fashewar kwalbar yasa rumaisa taja nunfashi da karfi, tana tari, saikuma tayi shiru, Fahad dake kuka yakara kiran sunanta cikedajin dadin bata mutuba, da sauri ya ciro wayarsa yakira Doctor. . Yana rike da hannunta yana shanshekar kuka, akayi knocking din kofar dakin, da hanzari ya mike yakarsa bakin kofar ya bude, bodyguard dinshi yagani a tsaye, " likitane yazo, yana falo " bodyguard din yafada, Fahad bai furta masa koh uffanba, yajuya da sauri ya koma wurin rumaisa, hannunsa yakai yana kokarin daukoto, sai kuma ya tuna da magabar data masa jiya, (HARAMUN NE NAMIJI YATABA MATAR DABA TASHIBA) Yayi jim yana nazarin maganar ya kalleta, hawaye suna fita a edonsa, a koda yaushe kara jinson rumaisa yakeyi a zuciyarsa A hankali bakinsa ya iya furta "kai bazai yuyuba, noo" hannunsa yakai ya tallabo rumaisa, wani irin nishadi yaji ya ziyarcesa, da sauri ya lumshe edo, sai kuma ya bude, edon sunyi ja sosai, ya nufi waje da ita akan kujera ya saukar da ita, likita yafra dubata .... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 41 and 42 Via *OHW* _A love story_💝 Tare dashi ake aikin domin tsaye yayi yana kallon duk abinda likitan keyi, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa cike da takaicin giya data sakashi yayi wannan aika2, gashi yanzu yayi yunkurin kashe a bar sonsa a banza da wofi, Dafe kansa yayi kafarsa sai rawa take yakasa tsayuwa guri daya, Bayan Likita ya kammal mata dressing, sannan ya juyo ya kallo fahad yace "ogaa komai ya kammala insha Allah nan bada jima waba zata sami sauki" Fahad ya girgiza masa kai, yana hawaye, nan likitan yayi sallama dashi yatafi, Da kyar ya iya karasa bakin kujera wadda take duban tata shima ya kwanta yana kallonta... jira yake ta farka, 7:52am Har safiya tafara bayyana, rumaisa ta bude idonta, zafi taji a kanta hakan yasa tasa hannu ta dafe kanta tana wasshh, jin bandeji a goshinta yasa tafara tuna abina yafaru jiya, da sauri ta mike tana kokarin tashi, nan kuma jiri yakara d'ibanta, tangal-tangal tayi zata fadi a lokacin fahad yakaraso gurin da sauri ya rikota tafada kirjinsa tana mayar da nunfashi, shikuwa ya kura mata edo, yana kallonta, Ita kuwa edonta a rufe yake domin ida ta bude edon gani take dakin na juya mata, Tajima a kirjinsa, kafin ta fara bude edon a hankali, caraf edonta suka sauka akan nashi, da karfi ta mike tana kallonsa, ranta a bace, wani irin haushinsa takeji, Harara ta auka masa sannan tanufi hanyar dakin datake, biyota yayi yana kiran sunanta amma ko juyosa bata yiba, tana karasawa bakin kofar dakin tashiga sannan ta turo kofar da karfi kamar zata game da hannunsa da sauri yaja baya, tasaka key ta rufe kofar, ta jingina jikinta a jikin kofar, kuka ta somayi mai sauti a hankali take sulalewa kasa tana kuka hartakai zaune, Fahad kuwa sai knocking kofar yake yana kiran sunanta amma taki budewa, jin sautin kukanta dayake yakara tayar masa da hankali, A hankali ya ke furta "plx rumaisa kiyi hakuri, wallahi bada sanina komai yafaruba, dan Allan kibude kofar" rumaisa tayi bnza dashi kuka kawai take, Fahad yaja nunfashi yace " nayi miki alkawarin daga yau nadaina shan giya, dan Allah kibud'e kofar" Duk da kukan datake amma saida tayi murmushin karfin hali, jin kalaminsa nacewa zai daina shan giya, Amma kuma saita gagara tashi ta bude masa kofar, Fahad yayi jim, yajita shiru, hakan yasa yajuya ba'ason ransaba zaibar kofar, Sautin karar budan kofar yatsayar dashi, yatsa cak guri daya, yana kallon kofar, Tana bude kofar takoma bakin gado tazauna ta dafe kanta tana hawaye, A hnkali ya turo kofar dakin yashigo, yakarasa bakin gadon, kusa da ita yazauna, yashare hawayensa, ya kalleta yace " wai garin yayi wannan abin yafaru, ni bnsan lokacin dana aika hakan agarekiba" Rumaisa tayi bnza dashi ko uffan tagagara ce masa, a lokacin ta tuna da batayi salla ba, Tana yunkurin tashi Fahad yace " talk mana" harara ta dalla masa tamike tanufi toilet, dasauri yatashi yabita baya, Takai bakin kofar toilet din taga yana kokarin binta hannu ta daga masa " karka kuskura kabiyoni" Tana gama fada bata jira yayi maganaba, tafada toilet din tamayar da kofar ta rufe,.... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: [8:12am, 09/08/2016] _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 43 and 44 Via *OHW* _A love story_💝 Shiru yayi yana kallon kofar ban dakin kafin yajuya yadaki ginin dakin, yana yajan nunfashi sannan ya koma bakin gado yazauna, yana tunanin rayuwarsa wai yau shine kebiyar macce, shida bai mayar da mace komaiba, amma yau gashi macci na wahalar dashi, A lokacine yaji kamar kafarsa na masa ciwo, kallon kafar yayi yaga jini, kwalbar giyar daya fasace yataka kuma harta fasa kafar, yadago kafar yana kallon, zafi yakeji sosai, A daidai lokacin rumaisa tafito daga ban dakin, yana jin fitowarta yayi saurin sauke kafarsa yana murmushin sai kaice wadda babu abin kedamunsa, Bata kulashiba, yana kallonta ta karkade kasan cafet din tafara sallah, yana zaune yana kallonta tana salla, Jiyayi yana sha'awar yayi sallah, Amma ya gagara tashi, yana zaune har rumaisa ta kammala sallar, sannan tazauna tayi adu oi, tana gamawa ta soke kanta kasa tana hawaye, "Harkin gamane " fahad yafada cike da fargaba, Rumaisa ta dago kanta amma bata juyo gurinsaba tace "meya dameka da sallana, aikai bakayi" tana gama fada saikuma tayi shiru, . Fahad yayi murmushin, yaji dadin data amsa masa maganar mike wa yayi yakarasa gurinta yazauna kafarsa namasa zafi sosai ya dubeta yace "fushe kike dani Rumaisa" yafadi maganar a marairaice , Sai a lokacin rumaisa tadago edota ta dubesa, ta share hawayenta sannan tace " dole nayi fushi dakai domin kasauka akan tafarkin addininka kakama addinin yahudu da nasara, Fahad takira sunansa, ths is th fst tmy data kira sunansa, sai yaji abin wani daban, the way yadda takira sunan yamasa dadi, yace "yes " Rumaisa tace "baka sallah, sannan kuma baka tunanin lahirarka, kadauki duniyar nan kamar wani gidan jindadi, kamanta cewa a koda yaushe zaka iya mutuwa kuma kakoma ga Allah, mezaka fada masa idan kaje garesa, zaka fada masa cewa shan giya da neman mata shiya hanaka yin salla, bazaka iyaba, a ranarma bakinka bazaiyi magana domin baki zai iya shirya karya, sassan jikinka sune zasuyi magana wadanda kasan dacewa kana aikata barna dasu, fahad kaiba yaro bane, kamallaki hankalin kanka, yakamata kagyara zamanka da uban gijinka" nadai tashiga karoro masa nasihohi daban-daban... Jikinsa yayi sanyi sosai, ajiyar zuciya yayi sannan yace "shikenan naji, zan daina komai, indai har hakan zai sakaki farin ciki, ya kara kallonta yana murshi kafin yace "amma namanta komai kikoyamun yadda zanyi" Dadi sosai rumaisa taji, Acen kasar zuciyarta tace yes my mission started,... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10:43am, 09/08/2016] _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 45 and 46 Via *OHW* _A love story_💝 kallonsa tayi tay murmushin tace "shikenan zan koyama" Shima murmushin ya mata, Zafin kafarsa yakai masa ko ina yayi yunkurin tashi, sai a lokacin rumaisa ta

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37