Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

jin sallamarta yasa ya mike tsaye yana jiran shigowarta.. A tsaye ta samesa fuskarsa a murtuke😡 Sau daya tadaga kai suka hada ido da sauri ta sauke kanta kasa, sum sum take tafiya kamar ba lanka ajikinta, gabanta sai faduwa yake tanufi dakinta... RUMAISA!! Cikin hargowa yakira sunanta saida ta kusan faduwa akan tsoro Hawaye suka soma zubo mata a hankali takarsa gurinsa, tas tas yadauketa da mari biyu kyawawa saida tasaki kara tayi baya tadafa kan kujera, Da gudu umma tafito daga dakinta cikin baccinta tajiyo karar mari, Alhaji lafiya" itace kalmar da umma take fada tana kokarin karasowa gurinsu, rumaisa najin muryarta ta tamike da gudu ta rungumeta tana kuka, cike da masifa yafara mata magana "bana hanaki zuwa gurin majnoon dinnan ba, wato kin maida maganata maganar banza, nizaki mayar karamin mutum, wannan shine karo na biyar kenan danayi miki a kansa amma kinki jih, to wlh kisani yau kinyi kuma kinkai karshe, gobe gaben nan zan daura miki aure da *faisal*, tunda nalura dacewa bakida hankali, meye abinso acikin mahaukaci, shashashar yarinya" Rumaisa takara fashewa da kuka jin yakira sunan faisal, kuma da furucinsa na cewa gobe zai daura mata, batajin zata iya rayuwa da wani da namiji a duniyar nan idan ba majnoon bane, tana manne a jikin umma tafito ta gurkusa a gaban abba tana kuka ta rike masa kafa " dan Allah abba kayi hkr wlh banason faisal" A fusace abba ya dukar da kansa kasa yana kallonta yace "idan bakya sonsa idan na aura masa ke ki kashesa" yana gama fada ya firgi kafarsa yabar falon yanufi dakinsa.. Durkusawa tayi kasan cafet tana kuka sosai, a lokacin umma takaraso gurinta fuskarta ba annuri tadafata tabaya " rumaisa" Dasauri tatashi ta rungume umma tana kuka tace "umma nashiga ukku, abba zaimun aure da faisal, kuma wlh umma bana sonsa" ..... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:33 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 9 and 10 Via *OHW* _A love story_💝 Da sauri abba yakarasa bakin kofar dakin yana dukan kofar dakin akan ta bude, amma taki bude wa, sai kukanta yakeji, Saida yayi mata barazana dacewa idan bata budeba yanzu zaije ya dauko sepia key yabude dakin kuma idan yabude zaiyi mummunar saba mata Sannam tatashi tazo tabude kofar, jikinta na rawa, ta shunkuyar da kanta kasa, Abba yashigo dakin ransa a bace yake kallonta " wlh idan kika fita a gidan nan bada saninaba, banyafe miki ba, kuma wlh zan iya tsine miki, akan wannan *Majnoon* din, kehar kin isa nahaifeki kuma kikibin umurnina" da sauri rumaisa tadago kanta a lokacin har hawaye sun fara ambaliya akan fuskarta, tana kallon abba takara fashe da kuka "kayi hakuri abba bazan jeba wlh bazan je dan Allah karka tsinemun" da sauri ta ajiye kolar dake hannunta takarasa bakin gado ta kwanta sannan tadago kai tana dube abba, muryarta na sarkewa saboda kuka tana cewa "kagani abba na kwanta wlh ba inda zanje yanzuma zanyi bacci, sannan ta hada hannayenta guda biyu tace "Dan allah abba karka tsinemin" takarasa maganar tana kuka, sannan ta noke kanta cikin filo, Abba yana huci yace " nidai na fada miki karkibar gidan nan bada saninaba" yana gama fada yajuya yafita yabar dakin Kuka take sosai zuciyarta har wani zafi take edonta duk sun kunbura, yazatayi da soyayyar majnoon datake sabuwar fill a cikin zuciyarta.. haka dai taci kukanta har aka kira sallar isha sannan tatashi taje tayi alwala, tazo ta dora sallah, bayan tagama sallar tafara kwararo adu a, saida tayi hawaye kafin takarasa adu' ar, tana kammala adu'ar sannan tanade sallaya ta takoma saman gado ta kwanta zuciyarta cike da tunanin majnoon komai zaici yau cikin darenan, a dai dai lokacin hawaye suka sauko kan kumatunta, koda tagama tunaninsa hawaye sharkaf a fuskarta, a hankali take fitar da sautin kukanta, tarasa gane wane irin sone takeyiwa mahaukacin nan, Sai a lokacin tatuna da bata rufe kofar dakin taba, da kyar ta iya tashe taje ta rufe dakin sannan tadawo tayi shirin bacci sannan takara komawa kwance, tana cikin tunaninsa bacci ya kwasheta... *2:39am Na dare* Majnoon yana kwance a gefen layin wata unguwa mai mota yabiyo layin, ga alama mai motar nan yayi mankas da giya tun daga nesa yake masa hoh amma Majnoon yaki ko motsawa dominshi baccinsa yayi nisah, mai motar na karasa wurinsa yatakashi ya wuce .... *Majnoon* ta furta Da karfi rumaisa ta farka daga mummunan mafarkin datake, da salati a bikinta, kuka yasoma zo mata, tayi jim tana tunani mafarkin, karde ace hakan tafaru da Majnoon, saitaji tanason ganin Majnoon a yanzu amma kuma saita tuna da maganar abbanta, hawaye suka sauko kan fuskarta a hankali ta sulale takoma kwance, tundaga lokacin bata kara komawa bacci ba sai sake2 take a zuciyarta.. *Asuba tagari* Bayan Rumaisa tayi sallar asubah tashiga bandaki tayi wanka sannan tafito har a lokacin bata dawo normal domin gaggar jikinta ce kawai a tare da ita amma zuciyarsa zakatakaf tana gurin tunanin Majnoon, Bayan taga shirinta tadauko littafanta tanufi dakin abba, zaune tasame saman kujera, nan ta durkusa har kasa ta gaidashi sannan tace "abba kayi hakuri da abinda yafaru jiya, kabani izini na fita, zanje makaranta" Abba yadago kai ya kalleta har yanzu fushi yake da ita yayi jim, sannan yace " ai fita kije makaranta yazama dole nabarki kije amma kisani bazan barki kitafi ke kadaiba zansa driver yakaiki, domin banason wata alaka takara hadaki da waccen mahaukacin, wai shin meyake dashi da sauran maza basa dashi, yaja nunfashi kafin yace " kuma maganar aurenki munyi magana da abban faisal yace na kara masa kwana biyu domin yanason yayi shirya2 amma badan hakan ba da yau dinnan zan daura miki aure, yasa hannu yaciro kudi ya mika mata yace "kije waje kicewa drive yakaiki makaranta kuma idan aka tashi yaje ya daukoki" Koda ta dago kanta idonta sunyi ja sosai takarbi kudin sannan tatashi tafita... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:34 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 11 and 12 Via *OHW* _A love story_💝 Tana zuwa tasanar da baba driver cewa abba yace yakaita makaranta, ba musu bb driver ya shiga mota suka lula makarantar, Yana ajiyeta a harabar makarantar ya juya, tun a cikin mota ta sanar dashi cewa idan suka tashi zata kirasa yazo yamaidata" tohm kawai yace, Bayan bayar makarantar Rumaisa tayi tsaye tana kallon makaranta kafin tad'aga kafarta tafara tafiya cike da yanga take tafiya harta karasa cikin aji, ganin kawayenta yasa takirkiri murmushi nan dai tadan waye fuska suka gaisa kafin malami yashigo a fara lecture, 1:30pm na rana Suka karasa lectures dinsu baki daya, kowa yafito nan tayi saida safe da kawayenta sannan tafito waje takira bb driver, bada jimawaba kuwa saigashi yakaraso.. Shiga motar tayi suka dauki hanyar gida, Rumaisa ta dube bb driver tace "baba dan Allah inaso naje nan layin kusa da namu wurin wata zanje" bb driver yace "tohm shikenan ba matsala" Bata kara maganaba saida suka kusa karasawa kusa dayin sannan tafara nuna masa hanya, dai dai inda tasan majnoon yana zama ta tsyar da bb driver sannan tafito tana dubinsa amma bata ganshi, danmm taji

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37