Chapter 23
Chapter 23
Dr bukar yace "to yanzu zan saka nurses subiyoka da gado aje a daukosa kafin naje nadauko wani abun a office" Kai kawai faisal ya kad'a masa Da sauri Dr bukar yasaka nurse suka janyo gado aka biyo bayan faisal Suna karasawa bakin motar yiya sauri ya bude musu kofar motar, Suna ganin wadda ke cikin motar kwance cikin jini suka zare edo, suna mamaki, daya daga cikin nurse din tace " wannan ai Prince Adnan ne " dasauri kaji sauran suna fadan eh wlh shine, Dasauri suka daukesa aka dorashi akan gado, suka kaisa emergency room, Dr bukar nafitowa daga cikin office dinsa, wata nurse cikin wadanda suka dauko prince Adnan ta karaso gurin a tsorace, ta sanar da dr bukar cewa ga Prince Adnan cen a emergency room, bayi wata2 ba yabi bayanta suka wuce dakin, Faisal yana zaune a kujera dake cikin harabar asibiti, har alokacin hankalinsa bai kwantaba duk tsoro yakeji, Yana zaune har gare ya washe, sannan likita yfito yana dube2 shi yake nema, dasauri yakaraso gurinsa, "Doctor meye faradu dashi " Dr bukar yace "dimuwace da firgita, sai yan wasu kananun raunuka dake jikinsa, amma yanzu komai nomal" Faisal yace "alhmdullah" yana fara'a Dr bukar yayi saurin katse masa fara'a dacewa"a ina kasamu sa ne" Nan Faisal yamasa bayanin komai tayadda yasamu Prince adnan, Dr bukar ya girgiza kai yace "yaron chief ne na garin nan, kuma shine kadai yaronsa daya rage masa a duniya, gaskiya zaiji dadi idan yasamu labarin kaika taimaki yaronsa, kuma nasan zai maka alkhairi sosai" Faisal yayi murmushi yace " hakane, amma ni yanzu bashine a gabanaba, inason naje masaukinane na huta domin agajiye nake" Likita yace "bakomai zaka iya tafiya, amma yanzun nan zan kira gidan chief domin susan halin da ake ciki, mezai hana kabayar da number ka koda mai chief yanemi yasan wanda yatai makawa yaronsa" Murmushi faisal yayi sannan yadauki numbersa yabawa dr bukar, Sai kuma yafita yabar asibitin.... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:51 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 93 and 94 Via *OHW* _A love story_💝 Mamaki yakeyi me photon majnoon yakeyi anan, Haj zainab tayi gyaran murya Haka yayi sanadiyar dawowar mai martaba da faisal duniyar tunanin dasuka shiga, mai martaba ya juyo ya kalli haj zainab, Haj zainab tace " kullum kazo gurin photon nan saikayi hawaye, yakama murika manta abunda yawuce, tunda wannna yaron ya mutu adu'a itace kadai abinda yake bukata" Mai martaba yashare hawayensa sannna yace "nima naso nayi hakan amma bazan iya mantawa da Mubarak ba, yatafi yabarni a lokacin da nake bukatarsa, Allah yajikansa da rahama" Duk falon kaji an kwashi sautin ameen, Shikam faisal jukum yayi yana mamaki, to idan wannan ya mutu, toshifa wancen daya baro abuja waye shi, kuma shin taya akayi wannan ya mutu, kuma a ina" duk a zuci yake wadan nan tambayoyin, yana so yasan amsar wadannan tambayoyi kafin yabar gidan nan, A duk lokacin dataga mai martaba yana yiwa photon Mubarak kuka, jitakeyi kamar ta mutu saboda bakin ciki, amma bata nunawa mai martaba hakan, kullum cikin lallashinsa take, hannun prince adnan taja sukabar falon suka wuce sashensu, Bayan haj zainab tabar gurin mai martaba yasa aka kai faisal masaukinsa... ***** **** **** Suna karasawa sashensu, dasauri haj zainab tasa makulli ta kulle kofar dakin ta zaunar da faisal kan gado tana dubansa tace "jiya kana gayamun magana saikuma wayarka ta tsinke, meke faruwane" Cike da tashin hankali, a lokacin datayi masa tambayar a lokacin ya tuna da yadda yaga fuskar majnoon cikin jini, saida gabansa yafadi sannna yace " umma Mubarak nagani a grin abuja" Mummunan tashin hankali ya ziyarci zuciyarta, tuni gumi yafara karyo mata, muryarta na rawa tace " Mubarak fa kace, daman bai mutuba " Prince Adnan ya fashe da kuka cike da tashin hankali yace "ina gudu a mota zan dawo gida, akan titi wani mahaukaci ya hauro titin da karfi,ni kuwa ban anakaraba saina kad'esa, bayan nakadesa nafito domin na dubasa, shine naga Mubarak kwance cikin jini ga dukkan alamu yanzu yamutu, yadan yi shiru yana shanshekar kuka kafin yaci gaba dacewa " tashin hankali dana shiga yasa nabar gurin, tsoro da firgita suka kamani, bayan na shiga mota nakara gudu sosai domin nayi saurin isowa gida ina cikin gudu kuma wata dabba takara karamun akan titi, nayi yunkurin na kauce mata amma nakasa, kukan dukan danayi mata kawai naji amma dagashi bankara jin komaiba, bansan meya faru daniba farkawa kwai nayi naga kaina a cikin ciyawa, da kyar na iya fitar dakaina nasamu nahauro titi , ina haurowa kuma sai jiri yafara dibana naga duniya tafara juyamun nan nazube kasa, tun a lokacin bansan meya sake faruwa daniba sai kawai farka nayi nagakaina a asibiti" yaja majinar data cika masa hanci, yana kuka yashare hawayensa, haj zainab duk tafita hayyacinta, tsintsar fargaba ce karara akan fuskarta, tama rasa mezatace, duk jinin jikinta ya tsaya, Prince adnan yana kuka yace " yanzu umma idan yaya Mubarak yadawo shikenan nayi asarar sarautar nan, saida komai yazo karshe yanzu kuma kOmai na neman jagulewa..." Haj zainab tatoshe masa baki ta hanashi karasa maganar, tana girgiza masa kai itama hawaye take "bazamu rasa sarautaba adnan, kaine sarki a wannan masarauta, ai ta yadda muka kawar dashi tsawon shekaru biyu hakan kuma zamu kara karashi lahira, mudin bokana yana raye to insha Allah babu kai babu asarar masarauta, gobe zanje nasami boka zamuyi magana dakai idan nadawo tashi kaje dakinka, karka nunawa kowa kana cikin damuwa" Prince adnan ya mike jiki bakwari yafita yabar dakin, haj zainab tabishi da kallo harya fita sannan tayi ajiyar zuciya ta share hawayenta, a hankali bakinta ya furta " tabbas akwai lauje cikin nadi, Faisal kuwa yana zaune yana tunanin lamarin majnoon yaji an turo kofar dakinsa, anshigo, Wata ma'aikaciya tashigo da farantin abinci a hannunta tazo har gabansa ta jibge masa abincin, sannan ta juya tana kokarin fita, da sauri yace "kee" Matar ta juyo tana kallonsa " yallabai kada matsalane " Faisal yayi murmushi yace " a a bakomai" "Toh shikenan" tafada sannna tajuya tana kokarin fita, Yakara kwala mata kira tajuyi akaro nabiyu "yallabai kodai da matsalane" Faisal yayi dariyar karfin hali, duk alamar rashin gaskiya ta bayya a fuskarshi yana inda2 yace "amm ammm daman tambayarki naso nayi" Tajuyo tana kallosa tace "uhim ina jinka meye tambayar" Faisal yace " wai dan Allah wane d'an sarkine ya mutu " Matar tayi murmushi tace "yarima Mubarak kenan, yaron kirki maison jama'a Allah yajikansa da rahama" takarsa maganar tana hawaye, Faisal yayi mamakin ganin hawaye a idonta, cike tasauyi yace " meya silar mutuwarsa" Matar ta tashe hawayenta ta dube faisal tace "koda biyana kudi zakayi bazan iya fada maka abinda yafaru da yarima Mubarak ba dimin saurauniyar gidan nan tahana kowa yabada labarinsa, duk wadda zaka tambaya a gidan nan bazai gaya maka ba, dazakabi shawarata danace maka kadaina tambayar kowa labarin yarima mubarak, domin zaifi maka sauki, kaga tafiyata " tana gama fada tajuya tabar dakin, faisal ya tsahi kamar zai bita yana kiran ta amma taki juyowa, Bayan tafita yasauke ajiyar zuciya a hankali ya furta "ya Allah" sai kuma yafara zancen zuci " yau naga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37