Chapter 22
Chapter 22
ciki ya cikata "umma zan iya tashi, harda guduma zan iya, muje " tafada cike da zumudi tana kokarin tashi Umma tayi murmushi sannan tataimaka mata takarasa tashi tsaye, Faisal dake tsaye a gefe duk mamaki yacikashi waye shi wannan majnoon din dahar fadar sunansa zai saika rumaisa dariya da farin ciki haka, kodai shine wanda takeso? Basu kula Faisal ba har suka fita daga cikin dakin suka nufi dakin jinyar majnoon, Faisal ya tsaya turus yana mamaki, zaiso yaga wanda rumaisa takeso, yaga dame yafishi, Kasa hakura yayi dole yabi bayansu, A tare suka shiga dakin umma da rumaisa, sai kuma ga faisal a bayansu, Hajja luba, likita , da kuma abban rumaisa duk suna cikin dakin, Majnoon ya dube mutanen dake zagaye a dakin yana mamakin suyawe su, Edo kawai ya kura musu yabisu da kallo Likita yakarasa kusa dashi yace "ya jikin naka, me kakeji a yanzu" Majnoon ya dube likita yana mamaki, muryarsa na rawa yace "miya samenine " Likita ya sauke ajiyar zuciya, a lokaci yatuna matsalar ciwon mantau da kedamun majnoon, sannna yace "kasamu hatsarine akan titi" Cike da mamaki majnoon ya ke maimaita maganar "nasamu hatsari" ya dube likitan yace "a ina nayi hatsari, kuma a yaushe, suwaye wa dannan" ya nuna su abban rumaisa, Likita ya dube su abban rumaisa yayi murmushi sannan ya juya gurin majnoon yace "wadan nan yan uwan kane" Majnoon yakara maimaita maganar " 'yan uwana kuma?, ni harda yan uwa nake dasu" Likita yace "sosai makuwa " Majnoon duk komai yadaure masa kai a hankali ya dube likita yace " Waye ni ?" Gaban kowa dake cikin dakin saida yafadi... (Nimadai mamaki likitan yabani, sai kace ya manta da dacewa majnoon ya manta komai)... Likita ya juyo ya kalli abban rumaisa, cike da tsoro wace amsa zai bawa majnoon, Dakin yayi tsit, majnoon sai kallon su yake, rumaisa kuwa duk jikinta yadau rawa, tana fargabar kar majnoon yakasa fahimtarsu, Wata idea tafadowa likiti, dasauri yace "amm wannan sunansa abba, ya nuna abban rumaisa yana murmushi Sannan yajuya gefen umma "wannna kuwa sunanta umma" ya nuna umma, Sai kuma yakara juyawa gefen hajja luba "wannan kuwa sunnan ta kaka" ya nuna hajja luba, Yana kai ga rumaisa sai kuma yayi shiru, taya zai yiwa majnoon bayanin cewa wannan itace masoyiyarsa mutumen dako kansa baisaniba, Likita ya nuna rumaisa yace "wannn kuwa itace matarka" Gaban majnoon yafadi, da sauri yamike zaune yana kokarin tashi, likita yamaidashi kwance yadafe kansa, har saida yayi kara kadan, wani irin zafi yaji kwakwalwarsa tafara dauka, yana nishi kadan kadan, edonsa suka rikide zuwa jan launi, Likita yace "lafiya kuwa, meke faruwa" Majnoon ya dago kansa da karfi ya kalli rumaisa yace "ina yarona,,,," Tashin hanakali ya ziyarci zuciyar rumaisa, jitakeyi kamar ta zube a gurin, tambayar kanta take, me yake nufi da ina yaronsa, kardai ace majnoon yanada aure, Daf taji gabanta yafadi... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:50 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 87 and 88 Via *OHW* _A love story_💝 Rumaisa tasoma ganin jiri, habar bakinta tasoma rawa kamar zatayi magana, likita ya kifta mata edo, alamar tayi shiru, Likita yayi saurin yin mumushi ya dube majnoon yace "ai bakuyi auren ba tukunna kafin kusami yaron" Majnoon yayi shiru kamar mai nazarin wani abu, sai kuma yajuyo yaci gaba da kallon mutane, Kan abba kallonsa yatsaya, yakurawa abba edo sosai, cikin saukankiyar murya yace "abba naji kowa an fadi sunansa amma ni banji anjira sunanaba, meye sunana" Abba da duk ya tsorata da lamarin majnoon, cikin inada2 yace "amm ...umm..sunanka....ammm." Likita yakarbe maganar dacewa "sunanka *KABIR*" Majnoon yayi dariya yana maimaita sunnan sai kuma yayi shiru, ya koma kwance, Likita yayi ajiyar zuciya sannan ya juya ya dube abba yace "muje waje zamuyi magana" yana gama maganar yafita yabar dakin, abba yabi bayansa, A office suka karasa, bayan abba yazauna likita yace "saidai kuyi hakuri domin shi a yanzu komai sabone a gurinsa, saikun dinga nuna masa abubuwa, sannan kuma kusaka rumaisa ta shiga jikinsa sosai ta yadda zai saba da ita, kafin ranar aurensu" Ajiyar zuciya abba yayi ya duban likita " toh shikenan likita insha Allah zamu kiyaye" Likita yace "yawwa, zuwa nan da kwana biyu idan yakara samun sauki zamu iya sallamarku" "Tohm" abba yafada yana kokarin tashi, yafita yabar office din, A harabar asibitin sukayi kicibus da faisal yafito yana kokarin gita daga asibitin, Kala baicewa abba ba, yasa kai yafice abinsa, Abba yatsaya yana kallonsa cike da mamaki, girgiza kai kawai yayi yakara dakin jinyar Kabir (majnoon), ■■■■■■■■■■■■■■■ Koda faisal yafita zuciyarsa cike da k'una da kuma wasu wasi kala2, Daman akan wannan ne rumaisa takasa karbar soyayyarsa, Toh me wannna yafishi, Motarsa yashiga, ya kunna, Sannan ya hau hanyar komawa gida, amma duk hankalinsa yana kan majnoon, duk sai yaji garin yafita ransa, zaiso ma ace a yanzu yabar garin, Tun acikin mota yayanke shawarar bazai kwana a garin abuja ba, domin yaga abin yazo masa wani iri, daman duk akan mahaukaci ne Rumaisa take wannan abun, Yana komawa gida yashiga hada kayansa, Saida yagama hada kayansa kaf Sannan yaje dakin daddy yasanar dashi cewa yanzu zai wuce kogi (lokoja), Daddy bai hanashi adu'a kawai yamasa yace Allah yakaisa lafiya, Sannan yajuya zai fita momy ta kwalla masa kira yajuyo, tace "dan Allah faisal karka saka damuwa da tunani a cikin zuciyarka idan kaje cen" yayi murmushi yace "insha Allah momy bazan yi hakanba, kudai kawai kutayi da adu'a" Nan dai sukayi bakwana cike da kewar juna, sannan yafice yabar dakin Yana fita harabar gidan yakarasa bakin motarsa yasaka kayansa a but sannan yashiga motar yatada yafice yabar gidan, Tafiya takeyi yana hawaye duk tunanin rumaisa ya hanashi sukuni, tukin kawai yake amma hankalinsa gabaki daya baya kan tuki, A hakan yaketa tsala uban gudu akan titi, yafi rabin tafiyarsa dare ya raba sosai, Ta hasken motarsa yake hango kamar Mutune kwance cikin jini, babu nunfashi a tattare dashi, a yashe a gefen titi, sassauta gudun motarsa yayi harya karaso gurunsa, yatsaya yana kallon mutumen, kamar bazai fitoba, Jin wurin yayi tsit babu alamar motsin mutum, ko dabba hakan yasa ya bude kofar motar yafito amma har alokacin jikinsa rawa yake, Yakarsa kusa da mutumen yana kallonsa, babu alamar harbi ko alamar sukar wuka a jikinsa, Durkusawa yayi a gaban mutumen yadora kunnensa akan kirjinsa, sai yaji kijirin na duka a sannu2, zuciyar mutumen tana harbawa, Da sauri yamike yana mamakin meya sami wannan mutumen, Jiyayi yanason yatai maka masa domin yabashi tausayi, kuma mutumen yana bukatar taimakon gaggawa, Tallabosa yayi yasakashi a motarsa sannan ya shiga motar yatada yabar gurin, Gudu yakeyi yana juyowa yana kallon mutumen, ko zai farka amma sai yaji shiru.. haka dai yaci gaba da tafiyarsa Kusan asuba yakarsa cikin garin kogi, Da shigarsa bai tsaya ko inaba ya zarce asibiti, Cike da tsoro yakarasa cikin asibitin, A nan yayi kicib'us da wani doctor yana kokarin fitowa daga wani daki, Dasauri yasha gabansa, doctor yace "malam lafiya" Faisal yace "ina tare da marar lafiyane, tun jiya yake a some har yau bai farkaba" Dr bukar yace "subhanallah yana ina" Faisal ya nuna kofar waje sannan yace "yana cikin motana "
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37