Chapter 20
Chapter 20
kumafa hakane, Allah dai yasa shiyafi zama alkhairi" Abba ya amsa da ameen , sannna yace "mukoma ciki koh" Daddy yace "eh muje, yanzu ma zamu wuce gida, domin inaso naje wani gun, zuwa gobe insha Allah zamu dawo mukara dubata, Abba yace "to shikenan Allah yakaimu goben" Nan dai suka dan daidai kansu kafin sukoma cikin asibitin amma dakaga yananin daddy zaka gane cewa baya cikin farin ciki, domin edon nan nasa sunyi jajir.... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:46 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 81 and 82 Via *OHW* _A love story_💝 Dakin jinyar rumaisa suka karasa, momy tana zaune akan kujerar roba, suka shigo, daddy yadanyi murmushi karfin hali ya dube umma sannan yace "toh mu zamu wuce, Allah yakara bata lafiya" sai kuma ya juya ya dube momy yace "tashi muje koh" momy ta mike itama tana kallon yanayin fuskarsa kamar marar gaskiya, saidai ta basar ta juya gurin su umma da hajja luba "Allah yakara bata lafiya yasa kaffarace" su umma suka amsa da ameen, Sannan daddy yasanar dasu cewa gobe zasu dawo, yana gama sanar dasu, sukafice daga dakin, Suna fita abba yasamu guri yazaune, anan yafara bayyana musu komai da yafaru tundaga zuwa dauko majnoon dakuma mantawa da abubuwan da yayi dama komaima saida yasanar dasu, daga karshe dai yace musu yanzu an cire haukar dake kansa, Bakaramin dadi rumaisa tajiba, umma ma haka, hajja luba kuwa tsoro lamarin yabata itamadai tana tsoron kar yaje yatuna daga baya ya gujesu, Tayiwa abba magana akan wannan dalilin kawai saiya nuna mata cewa bakomai. Shidai kawai 'yarsa tasamu lafiya, edonsa ya rufe baya ganin komai sai lafiya 'yarsa ,,, ******** ******** ****** Tunda suka shiga mota daddy bai furta uffaba haka zalika momy, har suka karasa gida, itadai ta lura da yanayinsa yana cikin damuwa, Suna karasa gida a falo suka dire, daddy ya zaune akan kujera ya furzar da iska, Momy tadan dubesa kadan, bayan tazauna ta kasa hakura tanason tasan matsalar mijinta "abban faisal wai meke damum kane naga tunda muka baro asibitin nan baka cikin hankalinka, yana yinka gaba daya ya chanza, wai meke faruwane" Daddy ya dago edonsa ya kalleta, yajima yana kallonta kafin yace "zan iya bawa faisal kowane gata da d'a ke samu agurin mahaifinsa, amma bazan iya saka soyayyarsa a Cikin zuciyar dabata sonsa ba, ni mahaifinsane zan kara umartarsa akaro na biyu daya fita harkar rumaisa, idan kuwa yaki magana to wlh zamu samu sabani dashi, domin ni bazanyi sonkai irin nasaba na kashe 'yar aminina" Tunda yafara maganar momy ta tsorata sosai domin tana fargatar ayya kuwa faisal zai iya rabuwa da rumaisa, cike da mamaki da fargaba take tambayar daddy" meya farune ko wata matsala takoma taso wane" Nan daddy ya fede mata biri har wutsiyarsa kamar yadda abba yamasa bayani, itama ta gamsu sosai kuma ta tausayawa rumaisa bakaramar girgiza tayiba dataji labari saida tayi hawaye, Jikinta duk yayi sanyi, murya kasa2 tace "nima na goyi bayan maganarka domin nina bazanso araba wannan soyayyarba ta rumaisa da majnoon ta hanyar faisal ba, kawai fatana Allah yasa shiyafi zama alkhairi" daddy ya amsa da ameen, sannna yace tatashi taje tahada masa ruwanka zai fita yanzu" Momy ta mike taje tahada masa ruwan wanka, sannna tazo tasanar da shi yatashi yaje yayi wanka ya shirya sannna yafita, ****** ******* **** Daga dawowar abban zarah daga dubai yasa akayi mata transfer aka maida wani company, Daya daga cikin nasa, ta samu natsuwa sosai, kuma ta daidai kanta ta rage tunanin faisal a kai kai, daman ganinsa ne kesa tana yawan tunaninsa, to yanzu kuwa tadaina ganinsa, Tafito daga wanka tana shirin fita aiki feena tashigo dakin, zarah ta dube "yan mata lafiya kuwa" Feena tayi saurin haurawa kan gadon ta kwanta tana dariya "lafiya lau anty zarah kawai fira nazo muyi, yau surutu nakeji" Zarah tadanyi dariya sannna tace "nikuwa gashi yanzu fita zanyi, sai dai idan zakimun tatsuniya toh zan saurareki" Dariya feena tayi kafin tace "toh shikenan anty zarah zan miki, badai kinason ta gizo da koki ba" Zarah tace "eh inaso fara muji" zarah tahaura kan gadon tana kallon feena cike da farin ciki, Feena tace "wata rana gizo...." sai kuma ta tsaya tana kallon zarah Zarah ta daga mata gira "yane yan mata naji kinyi shiru" Feena tace "anty zarah, sonake na tambayeki" "Uhim ina jinki" zarah tafada tana kallon Feena Feena tace "anty zarah wai naga yanzu kindaina kuka ko kindaina zuwa gurin faisal ne" Zarah ta tsuke fuska tadakawa feena tsawa "tashi kifita daga dakin nan" ta nunawa feena kofa Feena ta mike sum2 kamar wacca kwai yafashe mata a ciki, tana tafiya tana juyowa tana kallon zarah, Zarah tace "idan kika kira sunan faisal a gidan nan Allah saina yankaki" Feena tashe da kuka tafita da gudu tabar dakin, Tana fita zarah ta dafe kanta ta furzar da iska "bazan iya manta dakaiba faisal kaine farin cikin zuciyata kaine muradin zuciyata" duk a zuci take wannan zancen, A fili kuwa tsaki taja " nifa dole na cire sonsa a cikin zuciyata" tafada tana hawaye, (kujimun zarah wai dole ta cire sonsa, sai kace wani cire takalmi, hmm sone fa) .. Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:47 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 83 and 84 Via *OHW* _A love story_💝 Da yamma faisal yadawo daga gurin aiki, tun a gurin aikin yayi kudurin daya dawo zai shiryane yaje gurin rumaisa, domin shi haryanzu bai samu labarin rumaisa batada lafiyaba, Haka kuwa akayi yana dawowa yafada toilet yayi wanka, bayan yafito yafara shirinsa, yana cikin shirin yaji anturo kofar dakin, yad'ago kansa yana kallon kofar momy yagani, washe baki yayi yana murmushi "momy yanzu nake kudurin da nakammala shirin nan nazo nasameki, tund'a nashigo naji gidan yayi tsit, kamar bakowa" Momy tayi murmushi tace "eh ina daki, ai naji shigowar motarka, tashi kawai banba, yanzun nanma abban kane yafito dani, yace nazo nafadama yana nemanka" Gaban faisal yafadi, cike da mamaki ya dube momy yace "nemana kuma momy, Allah yasa dai lafiya" Momy tace "koma dai meye zakaji, karkayi jinkiri yana dakinsa yana jiranka" tana gama fada tajuya tabar dakin, Faisal yabi kofar da kallo harta fice, yana yin dayaga momy a ciki bai gamsu dashiba, yanaji a jikinsa kamar akwai matsala, furzar da isaka yayi a bakinsa, yaci gaba da shirinsa, tunani kala2 yarika zo masa, Yakasa samun sukuni, ya kosa yaji me daddy zaice masa, Kasa kammala shirin yayi, ya tashi ya nufi dakin daddy, Yana karasawa ya tura kofar dakin yashiga, zaune ya sami daddy saman wata 'yar karamar kujera dake d'akin, Momy kuwa tana zaune bakin gado, ko wannen su yayi shiru, fuska ba annunuri, Yana shigowa dakin yaji gabansa yafadi, ya sunkuyar dakai kamar marar gaskiya, yakarasa kusa ga daddy ya durkusa sannan yace "daddy gani" cikin ladabi da biyayya Daddy yayi ajiyar zuciya yana duban faisal "faisal kana son farin cikina kuwa" Cike da mamaki Faisal yayi saurin dago kansa ya dube daddy yace "sosai makuwa daddy, fatana akoda yaushe naganka cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai kuma yayi shiru yana kallon daddy Daddy yakara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37