Chapter 1
Chapter 1
[10/20, 10:33 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJ'NUN*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 1 and 2 Via *OHW* _A love story_💝 *BISMILLAH* " MAHAUKACI !! MAHAUKACI!!! " Shine sunan da dandazon yara kekiransa yana tafiya suna binsa a baya Wasu daga cikin yaran dake biyarsa har rigarsa sukeja Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake** Tafiya yakeyi yaran kuwa sai binsa sukeyi suna masa ihu, wani lokaci idan yagaji da ihun yakan dan juyo yabi yaran da gudu sai su zura da gudu.. Hakadai yaci gaba da tafiya, idan yaga bola a gefen titi yakan tsaya yayi tsince2 sa kafin yaci gaba da tafiya, Wata waka naji yaran sun fara masa suna cewa "ga maj nun uban tanbele, ga maj nun uban tanbele " shikuwa sai dukawa kasa yakeyi yana tsintar ledojin pure water, yana kwasar rawa ga alama wakar tanai masa dadi.. *** *** *** A hankali take taku kamar batason taka kasa, matashiyar budurwace yar shekaru 20 cikin shigar kamala tufafin hausawa atamfa da zani sai kuma katon hijab data saka har kasa. Hannnun rike da 'Yar karamar kula ta abinci... Dai dai kwanar wani layi ta kunnu kai Tun daga nesa ta hangi yara sunai masa waka, "Ga maj nun uban tanbele" Wani zarr taji jikinta yadauka, dasauri takarasa gurin duk ta watse yaran sannan ta dubesa ta saukar da murya tace "haba ! Haba meye haka katsaya yara suna mai maka waka kana rawa" sai tayi shiru tana kallonsa kafin yadago kai ya kallesa, sannan tace "ko so kake na fasa aurenka kane ?" Maj nun yayi saurin girgiza mata kai "a a nadaina " yana gama fada yayi sauri yazauna ya langwabe kansa Murmushi tayi tadawo kusa dashi tazauna ta mika masa kular datazo dashi "ga abincika maza ka cinye kabani kular na wuce gida, tun kafin Abbana yadawo " Da karfi ya firgi kular yana kokarin budewa, da kyar yasamu ya iya budewa shinkaface da namomi akai, karkade hannunsa kawai yayi ya fara aikawa cikinsa sako. Kura masa ido tayi tana kallosa cike da tausayi, bata ankaraba tafara hawaye, wani iri takeji a zuciyarta akansa, tarasa sanin ko meye wata zuciyar tace mata sona wata zuciyar kuwa tace mata tausayine... ita kanta takasa baya kanta amsa, *so ne ko tausayi* Tana zaune tana tunani harya kammala canye abinci ya miko mata kula "ungo" maganarsa tafitar da ita daga duniya tunanin datake ciki, tadan zabura kadan, sannan ta kirkiri murmushi tace "harka cinye " yace "eh " yana wasa da tsunmar rigarsa, Mikewa tsaye tayi shima ya tashi ta dubesa tayi murmushi tace "nizan wuce gida sai nazo da dadare" Maj nun ya hada kansa da kafada yace "nibanason kitafi kitsaya, muyi fira " yakarasa maganar yana gunguni Dariya tayi kafin tace " to shikenan idan nazo dadare zamuyi firar yanzudai zan wuce gida" "Tohm.. toh yaushe zamuyi aure" maj nun yafada yana cizon rigarsa Murmushi tayi tana kalloso tace "gobe " Tsalle yayi yana ihu cike dajindadi yace "idan mukayi aure a jirgi zan daukeki nakaiki india" Dariya tayi sosai, saida taga yafara kuluwa sannan ta tsayar da dariyarta tace "tohm shikenan nidai na tafi sai anjima" tana gama fada ta fice tabar gurin, saida tayi nisa kan dashu saikuma tatuna da maganar daya fada takara saka dariya.. sai kace itama haukar takee Saita fara tafiya ta juyo ta kalle sa tagansa sai tsalle yake wani irin mugun tausayinsa takeji, Hakadai taci gaba da tafiya cike da tausayin maj nun daidai kwatar layinsu ta hangi wata bakar mota da karfi taja da baya gabanta ya fadi sosai "innalillahi wa inna ilaihin raju un " itace kalmar data subuce daga bakinta.. Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.hausanovels001.com.ng [10/20, 10:33 PM] : _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 3 and 4 Via *OHW* _A love story_💝 Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka, nan ta fara salati harta samu na tsuwa tadan wani lokaci sai kuma taci gaba da tafiya Takai dap da Motar taji ankira sunan " *Rumaisa* !!!" Gabanta yafadi ko juyowa batayiba taci gaba da tafiyar ta .. Da sauri yafito daga cikin motarsa ya tari gabanta sukayi ido hudu, ya marairaice fuska kmar zainyi kuka yace "haba rumaisa meyasa bakijin tausayin zuciyatane, plx kitsaya ki saurareni dan Allah koda na minti biyune " Hawaye sunka cinciko a idon rumaisa, a duk lokacin data gansa wani irin bakin ciki takeji ya ziyarci zuciyarta, Muryarta tafarasa rawa kalilan abu zai iya sakata kuka, bude bakinta kuwa sai kuka "wai menai maka kake bibiyana kahanani jindadin rayuwata dan Allah ka fita harkata" *Fahad* yayi shiru yana sauraron kukanta, zuciyarsa na masa kuna, kwata2 bayason ganin kukan rumaisa, idan tana kuka shima jiyakeyi kamar zai tayata, muryarsa na rawa yace " sonki nake rumaisa zuciya ta tsunduma a cikin kogin sonki, iduwana basa muradin ganin kowa saike, a koda yaushe kece a mafarkina, plx rumaisa dan Allah kisoni" Hawayenta ta share ta sakar masa wani irin tsaki tace " ko kai kadaine namiji a duniya bazan sokaba, daidai da dakika daya bantabajin ina sonkaba" kafita daga harkata, kabano hanya na wuce " tanakarasa maganar tana kokarin turesa, shikuwa sai binta yake a duk gefen dataje yana fadan plx rumaisa, Da taga bayada niyar bata hanya taturesa ta wuce, A karo na biyu yakara shiga gabanta yana fadan plx rumaisa, wlh ke kadaice a raina, nayi miki alkawarin zan chanza halina idan har kika amince da soyayya ta, kiduba fa kigani wannan ma kadai ai kinyi jahadii... Bata jira yakarasa kalmarsa ta jahadi ba ta wanka masa wawan mari tas kakeji kafin tace "bana son, kuma natsani ganinka " takarasa maganar tahuci ta zagaya ta gefensa ta fice.. Tsayi yayi a guri daya sai kace bushanshiyar bishiya Dafe gefen kumatunsa yayi yana mai jin zogin marin da rumaisa tai masa, Hartayi masa nisa kadan yak'wala mata kira tajuyo ya saukar da hannunsa akan kuncesa ya share hawayensa yace " bazan iya hakura dakeba, domin kece muradina, tunda nabiki ta laluma amma kinki aminta dani dan haka yau zan saceki" Yana gama fadan hakan yajuya ya shiga motarsa yabar unguwar "Mahaukaci" rumaisa tafada fuskarta a ya tsune sannan taja Tsaki taci gaba da tafiyarta harta isa bakin gidan su gabanta faduwa yake akan maganar daya fada mata nacewa nasaiya saceta... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:33 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 5 and 6 Via *OHW* _A love story_💝 Tana isa kofar gidansu tatura kofar tashiga a harabar gidan taga motar abbanta a gefe yayi parking, cak ta tsaya guri daya, gabanta yayi mummunan faduwa, bugun zuciyarta yakara karfi, duk tsoro yakamata, domin tasan dacewa da suci karo da Abba akan maganar majnoon to gwanda ta fada rijiya zaifi mata sauki, da kyar ta iya taka kafafunta takarasa bakin kofar falo, A hankali take tura kofar falo tashiga tare dayin sallama,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37