Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
Download Book

kuka, ya durkusa kasa, sannan yakara dago edonsa yana hawaye yasauke murya abin tausayi yace "umman adnan dan Allah ina matata da yarona" Umman adnan tayi shiru kuka kawai take, Mubarak yajuya gurin adnan yace "dan uwana adnan ina matata da yarona" Cike da tashin hankali adnan yasoma magana, yana fadan "kaicona da wannan sonkai danayi, na cutawa rayuwar dan uwana akan mulki, a yanzu ina mai nadamar abinda zan fada masa" Mubarak yayi saurin cewa "fadamun menene, meyasa faru dasu, adnan kafadamun ina matata da da d'ana" Adnan yana sosai kuka yace "nina kashesu yaya mubarak, wlh nina kashesu da hannuna...." Wani irin gunji Mubarak yayi yakara fashe da wani irn masifaffan kuka, edonsa sunyi ja sosai, Faisal ma haka kuka yake, a zuci yake yafan tabbas har yanzu duniya akwai iblis, Mai martaba, kasa furta komai yayi banda Hawaye babu abinda yake, Sauran mutane dake cikin dakin wasu duk kuka suke wasu kuwa jikinsu yayi sanyi, ( nima dai komawa gefe nayi nashare hawayena sannan nadawo naci gaba da rubutu😭) Mubarak duk ya fita hayyacinsa, harda sambatu yasomayi "sun mutu, gabaki dayansu sun mutu, matata yarona,..." yakara fashewa da kuka, A daidak lokacin sukaji motsin gadon da umman Mubarak take kwance, A hankali mai martaba yake kai edonsa a gurin, yaga farkawa take kokarinyi, A hankali edonta suke kokarin budewa tana kallon dakin, mutanen dake cikin dakin tasoma kallo, har edonta yafada kan Mubarak dake durkushe yana kuka, habar bakinta narawa take furta " Mubarak".... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 113 and 114 Via *OHW* _A love story_💝 Da karfi Mubarak yad'ago kansa ya dubeta, da sauri yakaraso gurinta ya rungumeta suka fashe da kuka, cikin kukan yake fadan "umma sun kashemun matata da yarona, taya akayi hakan tafaru, kina ina kikabarsu suka aika wannan mummunan kudurinsu akansu.." yakarasa maganar yana kuka sosai Muryata na rawa tasoma magana "nasan komai Mubarak, komai akan edona akayi, KISAN GILLA sukayi musu" Mubarak yafito daga jikin ummansa yace "umma mesukayi musu" Umma tashare hawayenta sannan tace "babu abinda sukayi musu Mubarak, ranar dakayi tafiya zuwa abuja, a ranar suka kashesu, bayan tafiyarka, naje sashenka zanje na dauko khalid daga gurin mamansa domin nai musa wasa, ina karasa sashen, natarar da adnan menan kashe matarka, ina sauri nakarasa gurinsu, amma ina kafin nakarasa ya soka mata wuka a ciki, anan nayi saranda nakasa zuwa ko ina, akan edona bayan yagama da matar taka, ya dauko yaron shima yayakashi, tashin hankali nagani karara, ihu nasa haka yayi sanadiyar adnan ya biyoni da gudu, nima da niyar zai kasheni, da gudu nafita ina ihu, neman taimako, harna karasa shigowa sashena, ina shigowa anan kuma natarar da mutane ana kuka, koda na tambaya akancemun kaine ka mutu..." kuka ya kubuce mata ya hata karasa mganar, Zuciyar Mubarak tayi zafi sosai, huci yasomayi duk hankalinsa yatshi mikewa tsaye yayi yana huci, yakarsa kusa da adnan ya shaki wuyansa, yana fadan "kaima saina kasheka irin kisan da kayiwa ahalina" ya shaki yuwansa, shakar dabazai iya furta komaiba, Bodyguard sukayo kansa suna kokarin hanashi, basu karasa gurinba, mai martaba ya daga musu hannu, alamar karkowa ya hanashi, dole sukaja da baya, A haka Mubarak yaci gaba shakar wuyan adnan cikin zafin rai, saida ya dauke nunfashi, tun yana shure har yazo yadaina, (Wannan shi ake kira da KISAN GILLA my next novel ) Saida yadaina motsi Sannan yasakesa, yana huci, Rashin imani karara umman adnan tagani, a hankali take kai hannunta ta riko hannun adnan anan taji hannu yayi nauhi, tana sakin hannun kuma taga ya sulala kasa, Wata irin kara tayi tana kuka tace " ya mutu, adnan karka mutu, dan Allah karka mutu kabarni, wayyyyyoo, takara saka ihu, ta dora kanta kan kirjij gawar adnan, tana kuka, Mubarak yana gurfane agurin, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa sai zogi take masa, har yanzu bai huce yakaicin rashin matar saba da yaronsa, Kamar daga sama umma adnan tatsayar da kuka ta dago kanta ta dube Mubarak, edonta sunyi ja sosai, tayi ihu ta cafki wuyan Mubarak tana sunbatu "kaima saina kasheka kamar yadda kakesemun yarona" mugun shaka tamasa Mubarak yakasa kwabar kansa, Bodyguard sukayo kanta, da kyar suka iya babbare hannunta akan wuyansa, Mubarak ya galabaita sosai, tana sakinsa ya sulale yafadi kasa somamme, Ita kuwa ihu ta saka, tana kuka take fadan "sunkashe, wlh banyafe mukuba, mugaye azzalumai, maciya amana" tana cikin magana saikuma tasaka dariya, Bodyguard suna rike da ita tasoma, kuce kuce tana ihu da karfi, tamkar zautanciya, sambatu kawai takeyi, Mai martaba yana tsaye, tunda aka fara maganganun yakasa iya furta komai, tunanin yadda abin yakasance kawai yake, Ihun umman adnan ne yadamesa, da karfi ya juyo, cike da hargowa yace " kufitarmun da ita daga cikin dakin nan, kukaita cen cikin dakin bayan gida kujefata a ciki kurufeta" Haka kuwa akayi, suka fita da umman adnan aka kaita cen dakin bayan gida aka rufeta, Suka dawo aka kwashi gawar Adnan akaje a kayi mata salla, harda mai martab, dakuma faisal, sannan aka kaishi makwancinsa, anyi masa hukunci daidai irin wanda ya aikata, kuma wanda shari'ar musulunci tatanada, wannan shine gaskiya □□□□ □□□□ □□□□ _Bayan wasu awanni_ Mubarak yafarfado, duk ya jigata, hankalinsa, baya kansa sai sabbatu yake, yakasa natsuwa Daman dr bukar yana gidan, yacewa mai martaba, kawai yabari amasa allurar bacci, idan yasamu bacci kona wuni daya ne to tabbas idan yatashi kwakwalwarsa zata samu relax, Mai martaba ya amince da maganar dr bukar, aka narkawa Mubarak allurar bacci, nan yashiga sharara baccinsa, Bawani zaman makoki da akayi, kowa ya watse yakama gabansa, A daren ranar mai martaba yasa aka kira masa faisal yace yanason faisal yasanar dashi komai daya sani akan Mubarak, kafin suzo dashi nan.. https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 115 and 116 Via *OHW* _A love story_💝 Faisal yayi shiru, yana nazarin mema zai fada nan, sai ce dai yafara fadowa mai martaba komai daya sani akan lamarin majnoon, tun daga mahaukansa, har zuwa cutar daya samu sannan kuma da maganar aurensa da Rumaisa, wanda ya tarwatse ana daf da daurasa, Mai martaba ya girgiza akan lamari, kuma yaji dadin taimakon da abban rumaisa yayi akan Mubarak, Tausayawa 'yar tasa yayi kamar yadda yaji faisal yafada, tana matukar sob Mubarak sosai, lokaci daya yaji son, yarinyar yashigo ransa, saboda shi yanason duk wani maison Mubarak, ajiyar zuciya Mai martaba yayi sannan ya dube Faisal yace " kabani number mahaifin rumaisa zamuyi magana dashi" Cike da rawar murya faisal yace "banada numbansa, amma zanbaka ta daddyna atare suke komai, duk maganar da kukayi zaije yafada masa yanzu" Mai marta yace " bani number abban naka" Nan Faisal yashiga karanto masa yana yasakawa, Saida yagama sannan mai martaba yakira number, cikin sa'a kuwa wayar tashiga, Mai marta yayi sallama, daddy ya amsa, sannna mai martaba yace "mahaifin Mubarak ke magana, daga kogi" Muryar daddy na rawa yace "eh nagane.." Mai martaba yace "yawwa, nasamu labarin kunason kuhada aurensa da 'yarku" daddy ya tsora sosai,har lokacin muryarsa bata daina rawa ba "Eh hakane yallabai" sai kuma yayi shiru, Mai martaba yayi murmushi yace "karka samu damuwa, daman nakirakane inaso nasanar

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37