Chapter 30
Chapter 30
ya zo da gudu ya rungumesa yana kaka, har a lokacin mai martaba yakasa gazgata lamarin, A hankali yake hade hannayensa, yana tabo jikin Mubarak, sai a lokacin mai martaba yaji tabbas mutum nea, Wasu irin hawaye suka gangaro masa akan kumatu, na farin ciki, a hankali bakinsa ke furta "Mubarak" Mubarak yafito daga daga jikin mai martaba yana kallonsa yace " eh nine baba, wlh nine" yakarasa maganar yana kuka, Dariyar farin cikin mai martaba yayi yakara rungumo Mubarak jikinsa, sun jima a haka suna kukan farin ciki, kafin Mubarak yafito daga jikinsa, ya nuna masa ummansa yace " meya faru da ummata, meya sameta" Sai a lokacin hankalin mai martaba yadawo kanta da sauri ya furta "subhanallah, meke faruwa ne" sannan ya juyo yadube bodyguard yace "maza kudau keta kutai dakinta, yanzu zan kira doctor" Suna kakori karasawa gurinta, prince mubarak yadaka musu tsawa "karkowa yatabamun umma kumabarni nadauke abata nakaita daki, kumatsa daga gurin" nan kaga kowa yaja da baya, prince Mubarak yakarasa gurinta, ya tallabota, yanufi hanyar dakinta, Mai martaba yana kallonsa yana murmushi, girgiza kainsa yayi tabbas farin cikin gidan sa yadawo, hakan dayayi yakara tabbatar masa dacewa tabbas yaron sane, Faisal duk jikinsa yayi sanyi, al'amarin sai mamaki yake bashi, taya za'a ce mubarak yamutu kuma yanzu daga ganin wannan sai ace kuma shine Mubarak, shidai haryanzu zuciyarsa takasa samun wannan amsar, Mai martaba yabi bayansu bayan yagama waya da dr bukar, □□□□ □□□□ □□□□ Prince Adnan da ummasa suna zaune a cikin daki sai faman kuka suke, nan sukaji gida yadau hayaniya, sai guda kakeji, Prince adnan yakara rosa kuka ya dube ummansa yace "munshiga ukku umma, wlh yaya Mubarak ne yadawo bakiji yadda gidan nan yadau ihu ba, ni wlh bazan zauna na mutuba, na yafe komai na farin ciki, domin inason rayuwata, guduwa kawai zanyi" Haj zaine ta watsa masa harara cikin bacin rai tace "toh shikenan kagudu, nisai kabarni a kasheni, komai nayi halan badanka nayib, wlh baka isa ka gudu kabarni ba" Cikin gaggawa adnan yace "to kitashi mutafi, nifa bazan zauna a gidan nanba" yana gama maganar yamike tsaye yana kuka, Haj zainab ta janyo mayafinta ta rufe jikinta, har fuskarta ta yadda wani bazai iya gane taba, Sannan ta janyo dayan mayafi ta mikawa adnan tace " kaima ka rufe fuskarka" cike da tsoro yadauka ya nade fuskarsa sai kace buzu, Sannan suka fita, tafiya sukeyi cikin sauri, kamar zasu tashi sama, Dai kofar fita daga sashensu, sukaji ana kiran kaii, kaii, kutsaya a nan" Tsoro da firgita suka kara ziyarar zukatansu, cak suka tsaya guri daya, bodyguard din yakaraso gurinsu, fuskarsa a murtuke yace "suwaye ku" sukayi shiru, suka kasa furta komai, suna sauraronsa, Jin sunyi shiru yasa yakara daka musu tsawa yace " magana nake muku suwaye ku" Cikin bacin rai haj zainab ya yaye mayafinta, tana hararansa, da sauri ya durku kasa yana nonnoken kai " tuba nake sarauniya, Allah huci zuciyarki" uffa batace dashiba takara mayar da mayafinta, sannan taja hannun adnan sukaci gaba da tafiya cikin sauri, Mamaki yacika bodyguard, toh sukuwa wad'an nan ina zasu je, a murna cikin gida amma su kokari suke zasubar gidan, Girgiza kai yayi yace "tabbas akawai abinda ke faruwa wanda yakamata mai martaba yasani, bari naje nasanar dashi" da sauri ya mike yanufi gurin mai martaba, Koda yakarasa dakin, dr bukar yana kan umman Mubarak yana dubata, Mubarak yana zaune a kusa da ita, faisal kuwa yana tsaye bayan mai martaba, Bodyguard din yakaraso kusa da mai martaba, cikin sanyin murya yace "my chief, labari nazo dashi" Mai martaba yajuyo ya dube sa yace " banason jin kowane labari a yanzu, kajirani zuwa anjima" Bodyguard din yace "my chief wannan labarin bana wasa bane, wani abin mamaki nagani" Mai martaba yace " uhim ina jinka menene" Bodyguard yace "hajiya zainab tare da yaronta prince adnan suna kan haryar barin gidan nan" Cike da mamaki mai martaba yace " what! Da gaske kake wannan maganar" "da gaske nake fada maka wannan maganar, domin yanzu nahadu dasu kuma harsun rufe fuskokinsu, ga dukkan alamu ba lafiya ba" Cikin sauri mai martana yace "jeka zomin dasu, maza kaje ka danna kararrawar gidan nan kar a bar kowa yafita" Dasauri bodyguard yafita yana fadan "angama my chief" Yana fita yaje ya danna kararrawar, nan kaji gida yada sauti, Babu tsaiko aka fara rufe kofofin gidan, Haj zainab da adnan, daidai kofarsu, ta fita harabar gidan aka tsayar dasu... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 111 and 112 Via *OHW* _A love story_💝 Bude mayafinta tayi bodyguard dinda ke gurin gabaki dayansu suka durkusa akasa, cikin tsawa tace " kubudemun kofa nawuce" D'ayan bodyguard din yace "angama ranki shidade" Dasaurin yatashi yana kokarin Bude mata kofar, saida ya wangale kofar baki daya, sannan tamayar da mayafinta, ta dora kafarta daya a waje daya acikin falon, A daidai lokacin, bodyguard dinda mai martaba yacewa yazo dasu yakaraso gurin cikin gudun masifa, tun daga nesa yake cewa sauran bodyguard din da ke gurin "kutsayar dasu karku barsu sufita, umarnine daga mai martaba" Ai kuwa kamar daga sama sukaji a chafkosu, haj zainab ta juyo cike da bacin rai, domin bataji abinda ake fadaba, tace "kankuwasan kowa kakama" bodyguard din yace "nasani mana, matar mai martaba, amma kuma ai mai martaba ne yabada umarnin cewa kar' a barki kifita" Gabanta yayi mummunan faduwa, cike da tsoro, take kallon mutanen gurin, ba musu tajuya ta koma ciki, jikinta na kyarma, aka sasu gaba ita da adnan, suka nufi gurin mai martaba, □□□□ □□□□ □□□□ Yana tsaye akashigo dasu, yasa aka yaye masu lullubin da sukayi, adnan kuka yake sosai, haj zainab tarika kafar mai martaba tana kuka tace " dan Allah kayimun rai, ka gafarceni" Cike da Mamaki mai martaba yace "mekikayimun ne, aini bakimun komaiba, tambaya daya kawai zan miki, ina zakije keda adnan" Tana kuka tace "guduwa zamuyi saboda tsoron abinda zai samemu" Cike da mamaki mai martaba yake kallonta ya maimaita kalmar "guduwa zakuyi, me kukayine" Haj zainab tace " komai yafaru a gidan nan mune silar, sanadiyar wannan mulkin naka, naso ace d'ana adnan shine zai gajeka amma hakan bata kasanceba, shekaru biyu dasuka wuce, naje gurin boka nasa akayiwa Mubarak magana akan inason yahaukace ko kuwa ya akashesa, bokan yake cemun shibazai iya kisaba amma zaibamu maganin dazan sakawa Mubarak idan akayi amfani dashi zai haukace, inyaso da yadda zan iyayi acikin haukar nakashesa toh shikenan, haka na karbi maganin nadawo gidan, a ranar dana dawo gida nasamu labarin cewa Mubarak zaiyi tafiya zuwa abuja, To ta wannan hanyar nasamu damar saka masa maganain a cikin motarsa, Toshine bayan yatafi muka samu labarin cewa yayi hatsari a mota kuma motar ta kone kurmus, tana kuka takarasa maganar dacewa " wannan shine gaskiyar abinda yafaru akansa, tasanadiyar hakan ne yasa mahaifiyarsa takamu da wannan ciwon, kuma matarsa da yaronsa..." sai kuma tayi shiru tana kuka, Edon mai martaba sukayi ja sosai, ransa yabace Mubarak dake zaunr akusa da ummansa, yamike cike da bacin rai yana huci yace "ina kuka kaimun matata, da yarona, wlh idan kuka kashesu, kuma zan kasheku, kunkuwasan yadda nake sonsu,... suna inaneeee " yakarasa maganar yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37