Chapter 37
Chapter 37
yace "ga alama nan kingani, bayan rabuwarmu nasamu shiryuwa sosai, nazamo cikakken mutum, sannan kuma nayi tunanin bakomai mutum ke nema a rayuwarsa yasamuba, daman tun cen Allah yayi keba mamata bace, nayi nadama sosai akan abinda namiki, najima ina nemanki akan nabaki hakuri, sai yau Allah yahadamu, dan Allah rumaisa kiyafemun" Rumaisa tayi murmushi, yabata tausayi sosai "nayafe maka fahad, nidaman ban rikeka a rainaba, ina matar taka take" Yajuya yana nuna mata mota, a daidai lokacin wata farar mata tass tafito daga cikin motar tana rike hannu rumy, suka nufo inda su Fahad, Rumaisa tace wow!! Beauty ce, Allah yabarku tare" murmushi kawai yamata tare da cewa "ameen" Suna kara sowa suka gaisa ita da rumaisa, Matar tace "rumaisa koh?" Takarasa maganar tana kallon rumaisa Rumaisa tayi yake tace "eh nice kefa ya sunanki" Matar tace "sunana Sadeeya, amma anfi kirana da ummi" Rumaisa tace " to fa, sannu ummi, ya gida" Ummi tace " lafiya lau, amm my husband yajima yana bani labarinki, yacemun kece silar gyara masa rayuwasa, gaskiya ngode miki sosai, domin ni kika taimakawa, yanzu jinake kamar nafi kowacce macce sa'ar miji aduniya, kinga yana bani kulawa, tufafi..." Fahad yayi saurin katseta dacewa "toh bbc yanzu zata fara ruba miki surutu, idan kika biye ta wannan saimu kwana anan Allah" sukayi dariya su duka, Fahad yasha kan areef yace " wannan yaronkine, ya sunansa" Rumaisa tace "sunansa Areef" Fahad ya dube areef yace " sannunka malam areef mugaisa koh" Areef ya mika masa hannu suka gaisa, rumy ma ta mikawa areef hannu "mugaisa areef" saboda yarinyar akwai kaudi, da surutu saikace mamanta, areef shima yabata hannu suka gaisa, Nan dai suka kulla zumunci, sannan fahad yaja iyalinsa suka wuce, ta glass din motar rumy take yiwa areef hannu har suka bar gurin, Rumaisa tayi tsaye tana kallon titi, tafada duniyar tunani, tunani take ashe haryanzu fahad bai manta da itaba, Areef ya tabota tadan zabura Sannan tadawo hayyacinta sannan suka shiga mota suma suka koma gidan, □□□□ □□□□ □□□■ _Bayan sati biyu_ *KOGI* Mai martaba yayi murabus aka dora Mubarak aka karagar mulki, A ranar da aka nad'a Mubarak akan karagar mulki, a ranar haj zainab rai yayi halinsa, ta mutu, sakamakon bakin ciki daya saka zuciyarta har bawa lokaci daya ta gaggara zuea lahira, Mai martaba yasa aka kaita gidanta, na har abada wato(kushewa) _BAYA WANI LOKACI_ Hakadai rayuwarsu tayita tafiya cikin Farin ciki da kumwa kwanciyar hankali, Mubarak yana kwance saman gado, yayi shiru kamar bacci yake, rumaisa taturo kofar dakin tashigo, karasawa tayi bakin gado, tana kallon mijinta, tayi murmushi sannan tajuya masa baya itama ta kwanta, Sai yadaina jin motsinta sannan ya bude edonsa ya juyo ya kalleta yaga tajuya baya tana bacci, A hakali ya yaye blanket dinda ke jikinsa yakarasa kusa da ita yasa hannu ya juyo da ita daidai kirjinsa, yahauro ta kanta, yadora goshinsa akan nata, Suna shakar nunfashin juna, a hankali take bude edonta sukayi edo hudu, murmushi yasakar mata itama tayi masa a hankali yake furta "yau fa MAJNOON yanason yanema areef kane" kanne edonta tayi tana murmushi, Shima yayi dariya sannan yafara gudanar da aikinsa,.......😜 _BAYAN SHEKARU DARI UKKU DA HAMSHIN_ Kowa ya mutu, tun daga kan makaranta har zuwa marubucin😂😂😂 KURUNKUS, ALLAH YASA MUCIKA DA IMANI ALHAMDULILLA Anan nakawo karshen wannan d'an takai tancen labari nawa wanda nayiwa take da suna MAJNOON( the mad man, become a prince), abinda nayi kuskure a cikinsa Allah yayafemun, domin duk dan Adam ajizine, Ina miki sakon gaisuwata ga dukkanin ilahirin masoyana wadanda suka nuna kaunarsu akan wannan novel nawa, dafatar ya nishadartar daku kuma ya ilmantar daku, Allah yasa sakon dana keson isarwa agareku yasamu karbuwa, ina kara gode muku sosai Allah yabar zumunci.. Ameen Jinjina gareku yan uwana marubuta na Group din ONLINE HAUSA WRITER'S dakuma duk sauran marubuta na duniya baki daya, nagode sosai da goyon bayan da kuka bani, Allah yacika mana burinmu na Alkhairi, Kunfi kowa son novel dinna Hausa books group, especially ummun ikram, jitakeyi kamar tabini jega tayiwon typing, dole na muki godiya nagode sosai, KUJIRANI a sabon novel dina mai suna AUREN BAZATA (marriage without love) Sannan kuma akwai wasu novels dazanyi nida wasu kamar su, HAR A ZUCIYA, BAYA DA KURA, sannan kuma da HAWAYEN MASOYA, duk kujira zuwansu, suma suna dauke da darussa kala-kala, a cikinsu, Ina kara gode muku masoyana kuna raina aduk inda kuke, Allah yabarmu tare NAKU ABDUL-MR, SMILES😃 Mr, smiles 07068890036 domin gaisawa dakuma gyara, nagode😘 AYI SALLAH BABBAR SALLAH, LAFIYA 😊 Bissalam saimun sake haduwa, love you oll😊
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37