Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
Download Book

ita ko motsa edonta batayiba, Tausayinta yakeji har cikin zuciyarsa, durkusawa yayi kusa da ita ya rike keken guragun datake zaune yayi gyaran murya sannan yace "inada labari akan yaronki Mubarak" yana gama fada sai kuma yayi shiru yana kallonta, Duk inda jijiwowin jikinta suke saida suka motsa, bugun zuciyarta yakara karfi, yana rike da keken yaji keken yafara rawa a hankali yadago kasan yana kallonta , a daidai lokacin hawaye suka soma fita acikin edonta, a hankali take dago kanta tana kokarin furta magana sai kuma takasa, Makwogaronta yasoma zafi, tari tasoma yi babu kakkatawa, kamar ranta zai fita, faisal ya mike tsaye cike da tsoro, yana fadan " lafiya kuwa meke faruwane" Itakam tari taci gaba dayi da karfi sosai harsaida ta fado daga kan keken datake zaune, faisal yace " oh shet" nanfa yaji tafiyar mutanen suna kokarin shigowa gurin..... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 99 and 100 Via *OHW* _A love story_💝 Dasauri ya gudu yasami guri ya labe bayan kofar falon suna shigowa shi kuwa yafita da karfi, da gudu yakarsa dakin da aka saukesa, Yana shiga dakin yafada kan gado yana sauke nunfashi, Gabansa sai faduwa yake, Allah2 yake kardai ace shine silar tashin ciwon umman Mubarak, tunani barkatai suka rinka zomasa, Ma'aikatan nashiga gurin sukaga halin datake ciki dasauri suka je suka sanar da mai martaba, Cikin firgita ya iso falon ganin halin datake ciki yasa yayi saurin kiran dr bukar domin shine family doctor nashi, Bada jima wataba kuwa dr bukar yakaraso, yadubata sannan yayi mata allurar bacci, saida ya tabbatar data samu sauki sannan yabar gidan, Bayan fitar dr bukar, Mai martaba ya dube ma'aikatan cikin bacin rai yace "waya shiga sashenta" ma'aikatan sukace su wlh basuga kowa yashiga ba, Ajiyar zuciya kawai mai martaba yayi sannan yace su fice subashi guri, haka kowa ya watse akabar mai martaba shikadai yayi tsaye yana kallon umman Mubarak, yajima yana kallonta kafin shima yafita yabar dakin... *BAYAN KWANA BIYU* ABUJA Majnoon yasamu sauki sosai, sun saka masa suna *kabir* haka suke kiransa, shikuwa yana amsawa, Suna bashi kulawa sosai, A duk lokacin da akayi masa maganar aurensa da rumaisa, toh komai farin cikin dayake nan take farin cikin zai gushe, Hakan yasa aka daina masa maganar auren, saidai kullum rumaisa tana tare dashi , abubawa kawai take koya masa, tasamu farin ciki sosai atare dashi, Yauma kabir yana zaune akan gadonsa na jinya, rumaisa tana zaune kusa dashi, tana masa bayanin yadda ake alwala, har suka kammala, kuma yana fahimta sosai, Rumaisa tayi murmushi tace "Yanzu dai kasan yadda akeyin alwala saura sallah, tayi gyaran murya, a lokacin suka hada edo tayi masa murmushi shima yamata, sannan tace "ita kuwa sallah idan zaka farata, zaka fuskanci alkibla, tadago kanta ta kallesa tace " kasan meye alkibla" kai kawai ya girgiza mata alamar baisaniba yana murmushi, tace "gabas itace alkibla, tanuna gabas da yatsanta,sannan taci gaba cewa "bayan ka fuskanci alkibla sai kuma kayi ikama...." tana batun fara karanto masa ikama Sukaji a turo kofar dakin anshigo, suka tsayar da karatunsu, suna kallon mai shigowa, abba ne yashigo da takarda a hannunsa, ya dubesu yayi murmushi yace "saiku tashi kushirya muwuce gida domin likita ya sallamemu" yakarasa maganar yana dariya, Rumaisa tajidadi sosai, ta dube majnoon tace "kabir zakaje gidanmu" Girgiza mata kai yayi "eh zanje mana, ai gidanku gidan mune" Murmushi tayi sannan tace "toh shikenan, tashi kashirya mutafi" Nan fa suka shiga hada kayansu, umma da haj luba suka tayasu aka hada kayan sannan suka fita, bayan sun fita suka saka kayan a mota, sannan kuma kowa yashiga motar, Abba yaja motar suka nufi gida, Bayan sunkarasa gida, abba yabawa kabir daki daya daga cikin dakunan dake gidan, tare da nunnuna masa komai na gidan, Haka dai suka wuni cike da farin ciki da walwala, Bayan sallar isha, suka taru a falo suna fira cikin nishadi da kwanciyar hankali, Abba yakatse musu fira dacewa "munsaka ranar auren rumaisa da kabir nanda sati daya, me kukace?" Haj luba tayi saurin karbe maganar cike dajindadi tace " hakan yayi, domin ni na matsu babbar garin nanba, banaso natafi banga auren 'yar jikan tawaba, Allah yatabbatar mana da alkhairi" Duka falon suka amsa da ameen, Rumaisa tana kwance akan cinyar umma, ta rufe fuskarta saboda kunya, Kabir kuwa yana zaune akan kujera, tunda abba yayi maganar aurensu, yaji kansa na sarawa, kwakwalwarsa nai masa zafi, da sauri ya mike tsaye yabar falon, suduka suka bishi da kallo, sun kasa fahimtar lamarinsa, a duk lokacin da aka dauko zancen aurensu, sai kawai suga ya canza yanayi, wani lokaci kuwa saiya tashi yabasu guri, Babu wanda ya furta ko uffan, domin inda sabo sunsaba da wannan halin nasan, Sundan taba fira kadan sai kuma suka watse kowa ya nufi dakinsa... Washe gari Abba yasa akafara gyaran daya daga cikin gida jensa, inda rumaisa da kabir zasusha amarcinsu, Komai na auren abba yayi, Suna bawa kabir kulawa sosai, duk ya sake jiki dasu, kamar daman cen sunsan juna.... □□□□■□□□□□●□□□●□ KOGI Umman mubarak tasamu sauki sosai amma dai haryanzu ba abinda ya chanza akan rashin lafiyarta , mai martaba yasa aka maidata falon da take ciki, Taci gaba dazamanta domin tafison zama cen fiye da ko ina, acikin gidan Faisal da adnan sun shaku sosai, kullum sai adnan ya fita yawo tare da faisal, domin yasamu ya gusar masa da tunanin fadawa wani labari akan Majnoon, Kullum suna waje, idan kaga sundawo gida to sai dare idan sunzo bacci, Kwanan faisal biyu a dakin da mai martaba yabashi, A rana ta ukku, prince adnan ya umurcesa akan cewa yadawo dakinsa da kwana, Duk dai sunyi hakanne dandai kawai su gusarwa faisal da tunaninsa daga fadawa wani labarin Majnoon, Dominsu sunaji a jikinsu cewa shine Mubarak, ba wani mai kamadashi, Yau dadare bayan sundawo daga yawonsu, dakin adnan suka dire, Faisal yazaune kan gado yana nishi "waii wlh yau dukna gaji, kasala nakeji" yafada yana kokarin kwantawa, Adnan yayi murmushi yace " hmm nima wlh nagaji, amma dai bazan kwantaba sainayi wanka" Tabe baki kawai faisal yayi "uhim kaika sani nikam wanka saida safe, Allah bazan iya tashi ba yanzu" Adnan yayi shiru yana murmushi, sai da yagama cire kayan dake jikinsa, dagashi sai singlet da boxer, ya juyi ya kalli faisal yace "yawwa daman mantawa nayi ban fadamaba " Faisal yadago kansa "eh menene " Adnan yace " daman umma ce tace, sati mai zuwa muje abuja muzo da wancen mutumen maikama da yaya Mubarak, " Faisal ya koma kwance yana cewa "tohm shikenan Allah yakaima, sai kuma yadago kansa ya dube faisal yace "saidai kuma akwai matsala" Dasauri adnan yace "matsalarme fa" Faisal yace " daman naso nasanar dakai cewa shifa waccen mutumen, yanada matsala domin ya manta da komai daya taba faruwa dashi a baya, ma'ana yakamu da cutar amnesia" Gaban Adnan yayi mummunan faduwa, awani bangare kuwa dadi yaji, domin ayanzu yanada damar dazai tunkare majnoon babu fargana tunda yamanta komai, Ajiyar zuciya yayi, zuciyarsa cike da farin ciki sannan yace " ba cutarsa bane damuwarmu, damuwarmu shine munemawa umman Mubarak lafiya, domin na tabbatar dacewa tana ganinsa zata samu

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37