Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kan kumatunta cike take da tausayin umma duk da ba itace ta haifetaba amma tanajin sonta har cikin zuciyarta, rumaisa ta marairaice fuska ta dube abba tace "Dan Allah abba kaje kazo da ita, wlh babu hannunta a ciki" sai a lokacin tayi magana, Abba yadube yaga yata hawaye tausayi ta bashi, yace "toh shikenan" da sauri ya mike, yanufi hanyar fita, Hajja luba tace "ina kuma zakaje" Abba yajuyo yace " zanje station din ne nazo da ita tunda rumaisa ta bukaci ganinta" Bai jira hajja luba tasake maganaba yafita yabar gidan, *Bayan minti 30* Falo ya cika umma da Abba Hajja luba da kuma rumaisa, duk suna zazzaune, sunyu jugum2, umma dukta galabaita tayi baki, ta wahala sosai, Abba yana zaune yana kallon hajja luba, Umma tatashi tazo gurin rumaisa kwalla duk sun cika mata edo tace " Dan Allahki rumaisa kiyafemin, Alhakinkine ke fita akaina, nasan dacewa na cuceki, na hanaki jindadi a gidan nan, amma wlh yanzu nayi nadama sosai, dan Allah kiyafemin" Kuka rumaisa takeyi ta d'ago umma ta rungumeta tana fadan " nayafe miki ummata, wlh nayafe mike har cikin zuciyata" Umma tana kuka tace " nagode rumaisa" suka kara kakkame juna, suna kuka, Duk haushi umma take bawa hajja luba, Hajja luba taja tsaki sannan tayi gyaran murya, domin ita har yanzu bata sauka daga dokin zuciyar data hauba, tace " ni ba ruwan da kukanki, kukan munafinci, mtsw, Hajja luba ta juya gurin abban rumaisa tace " kai kuma bara kaji, maganar auren dole dazakayiwa rumaisa na janye wannan maganar, kabawa rumaisa wadda takeso, idan kuwa ba haka wlh nida kaine" Cike da mamaki abban rumaisa yake kallon Hajja luba, wai kodai batasan wadda rumaisa takeso bane, mahaukacine fa, taya zai aurar da diyarsa ga mahaukaci, Cikin sanyin jiki abba yace "hajiya waddafa takeso dinnan mahau..." bai karasa maganarba sukaji an turo kofar falon aka shigo tare dayin sallama, Fahad ne shida da iyayensa... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 65 and 66 Via *OHW* _A love story_💝 Falon gabaki daya kallon kowa su yake kallo, abban rumaisa, da umma, hajja luba da basu san suba su na mamakin suwaye su, Rumaisa kuwa tuni jikinta yadau rawa, muryarta na rawa ta dube fahad cike da masifa tace "mekazo yi a gidanmu, meya kawoka" Abban rumaisa ya cika da mamaki ya dubi rumaisa yace "suwaye wadan nan kuma" Rumaisa ta fashe da kuka tanajin yadda zata gayawa abbanta cewa shine wadda yasaceta, sai tayi shiru kawai tana kallonsu taji dame sukazo, Tun shigowarsu fahad yake kallon Rumaisa sannan suka karaso cikin falon, suka gaisa da juna, Abban fahad yace "ni sunana Alhaji sani babba" abban rumaisa yayi saurin katsesa da cewa "ok nagane, Allah sarki, ban taba ganin ganinkaba amma inajin labarin sosai a garin nan" abban fahad yana murshi yace "eh hakane kasan ni bamai yawan zama kasar nan bane" abban rumaisa yace "eh hakane, lafiya kuwa " yafada yana kallon abban fahad, Abban fahad yanisa sannan yace "nine mahaifin fahad, wato wannan yaron" yajuya yana kokarin nunawa abban rumaisa fahad, sai yaga wayam babu fahad a gurin, Koda suka juya, a lokacin har Fahad yakarasa gurin rumaisa edonsa sunyi ja sosai, ya durkusa a gabanta, Falon gabaki daya saida kowa yayi mamaki, Ya dago kansa ya kalleta a lokacin har hawaye sun fara fita a cikin edonsa, murya a sanyaye yace "kada zuciyarsa tayi zargin cewa nazone domin na cuta miki a a, hakika rumaisa bazan taba mantawa dakeba a tarahin rayuwata saboda irin gudun muwar da kika bani wacca ita narasa tun a baya da rayuwata bata kasance a yadda kika tsinceniba, banada alkhairin dazan iya saka miki dashi sai dai ina rokonki Alfarmar abu guda daya agurinki" fahad yadanyi shiru yana kokarin share hawayensa, folon gabaki daya shi ake sauraro, sannan yace "Dan Allah rumaisa ki yarda ki aureni, ta wannan hanyarce kadai zan iya saka miki akan alkhairin da kikaimun" Gaban rumaisa yayi mummunar faduwa tabbas fahad yabata tausayi amma saidai idan tayi na am da kudurinsa to tabbas ta cuci kanta, domin bashine a cikin zuciyarta ba, hawaye ke fita a edonta tasa hannu ta share, cikin sanyin murya take Takira sunansa, yadago kansa ya kalleta, sannan taja nunfashi taci gaba dacewa "tarayyata dakai banayita tabe danna aureka saboda ni ban taba kaunar kaba, na kusancekanee kawai dan na fidda kai halin dakake ciki amma ni bantaba jin sonka a zuciyataba, kayi hakuri" Tunda tafara maganar zuciyar fahad tasoma duka tara2 , hankalinsa yayi mutukar tashi dajin kalaman rumaisa, hawaye suka kara sauko masa, yakara marairaice fuska yana cewa "amma rumaisa idan kikamun haka bakimun adalciba, dakinsan haka zakimun dakin barni naci gaba abubawan danake daya fimin, amma danme zaki dandanmun zuma a baki kihanani lasa, dan Allah rumaisa ki amincedani" Rumaisa tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace "fahad nifa bazan aure kaba, domin ni inada wadda nakeso" tana karasa maganar sai kuma tayi shiru, ganin hankalin kowa a falon yadawo kansu, duk taji ta tsargu, a hankalin sautin kuka fahad yasoma fita, jiki a sanyaye ya mike tsaye yana kallon rumaisa sannan yace "amma meyasa zakimun haka, kinkuwa san yadda zuciyata take bugawa ayanzu, wlh jinake kamar zata fasa jirkina tafito, karki illatamun rayuwa rumaisa, kece kadai wacca nakeso dan Allah rumaisa kiyarda ki ...." rumaisa ta daga mishi hannu tasauya yanayin fuskarta zuwa bacin rai cike da hargo tace "me kakeson nayi maka ne, nidakai munyi alkawarin aurene, ko kuma nace zan aurekane, nagaya maka bana sonka, kafita rayuwata mana aaaa" Abban fahad duk jikinsa yayi sanyi a hankali yakarsa gurin ya janyo hannun fahad, kuka fahad yake sosai, umman fahad ma haka kuka take tasa gyale ta toshe bakinta kar sautin kukanta yafita, tana mamakin rashin tausayi irin na rumaisa, Abban fahad yace "muje koh " ya riko hannun fahad, fahad ya firgi hannunsa daga rikon abbansa yamasa, ya juyo ya kalli rumaisa yace "baki taba yimun ba amma kin nunamin alama, bantaba tunanin imaninki da tausayinki a iya baki kadai suka tsayaba idan aka bukata bazaki iya yiwa mutumba, to Amma wlh inason kisani" fahad yanuna mata dan yatsaya kafin yaci gaba cewa "duk ranar da muka sake gamo dakee..." sai kuma yayi shiru yakasa karasa maganar ya yarfar da hannunsa yana kuka, cike da tausayi, Abban fahad ya kara janyo hannunsa suka nufi kofar fita fahad sai kuka yake yana fadan "karku rabani da rumaisa wlh itace muradin raina, dan Allah abba kubata hkuri ta amince ta aureni, dan Allah umma kubata hkr" haka yarika jiro kalaman magiya duk ya fita hayyacinsa, Hakadai suka jasa suka fita dashi, a mota suka sakashi umma ta zauna gidan baya a tare dashi tana lallashinsa, ran abba a bace ya firgi motar da karfi tsiya suka fice sukabar gidan... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 67 and 68 Via *OHW* _A love story_💝 Suna fita abban rumaisa yace "waye kuma wannan a ina kika sansa" Rumaisa tadan bata fuska kamar batason fada ganin falon kowa ya sakar mata edo, yasa tace " Sunansa fahad, shine

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37