Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
Download Book

mai ruwan orange mai haske, hade yake da wani siket maii ratsin baki, aka barbazo mata gashinta agabanta, gashin shima yasha gyara, sannnan aka yafa mata gyale akai, hakadai tafito 'yar india sak, tayi kyau sosai, A bagaren Mubarak kuwa shima yashirya sosai, sakamakon yau walima aka yasa yanada rawani, shima yayi kyau abinsa, yafito kamar sarki, Misalin karfe 10:30 na dare, aka gama walimar, sannan kuma aka kai amarya Rumaisa dakinta, saida umma tamata nasihohi sosai, haka ita haj luba takara tofa albarkacin bakinta, Saida rumaisa tayi hawaye, saboda sunyi mata nashisa mai ratsa jiki, Dakin yasha kamshi iya kamshi, komai nadaki white ne dakin yayi haske sosai, umma da haj luba sukakai rumaisa dakinta sannan suka fito sukabarta ita kadai, Mubarak kuwa saida yasake sabon shiri, sannan yasa Faisal yarakashi dakin amarya, ba karamar rigima sukayiba akanshi bazai jeba dakyardai Mubarak yasamu faisal yaje, koshi yana zuwa ba wani surutu yatsaya yiba, ya bar dakin, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, Yana komawa daki, yasauke nunfashi yana Hawaye, lokaci daya yaji son aure yashigo masa rai, tambayar kansa yake "toshi wama zai aura bayan shidai rumaisa yakeso" Zarah ta fado masa a rai, tunani yayi irin wulakanci daya rika mata, kaf guda yaji tausayinta yakamashi, (hahha faisal yakamu)... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 125 and 126 Via *OHW* _A love story_💝 Dakarfi tazabura tana kokarin tashi, faisal yasakar mata wani irin lallausan murmushinsa, Harara ta dalla masa tare dajan wani irin wawan tsaki, ta kwashi jakarta tabar gurin, dasauri yabita a baya yana kirar sunanta, amma ko juyowmsa bata yiba, Dayaga bata imanin tsayawa yayi saurin riko mayafinta tare da shiga gabanta, ai kuwa nanta daga hannu ta wankesa da wani irin wawan mari, saida yaga wata wuta, Saukar hannunta akan kuncensa yasa ta kanne edonta, saboda wani irin zafi dataji acikin zuciyarta, kafin ta bud'e edon tuni hawaye sun sauko mata, takasa maida hannu a jikinta, Faisal yana dafe da kumatunsa edonsa sunyi ja sosai kamar zaiyi kuka yace "lokacin kine, kiyimun duk abinda yadace, domin yanzu a shirye nake dana dauke duk wani wulakancin dazaki mun, idan mari daya bai mikiba kiramun daya, ya nuna mata gefen kumatun sa daya, sannan yace " amma kisani sabon sonkine a cikin zuciyata kuma a yanzu zan fara rainonsa" Tana tsaye sai hawaye take, itama marin data masa har cikin zuciyarta taji, duk sai taji ta tsani hannu jitake kamar tasa wuka ta gutsure sa, yau wai ace itace tadaga hannu ta mari faisal dinta farin cikin, muradin ta, tabbas tayi babban kuskure da bazata taba mantawa dashiba, Dakarfi kuka ya kube mata da gudu ta kauce masa ta nufi cikin motarta, tana shiga motar tafashe da wani irin masifaffen kuka, cike da tsanar kanta meyasa tayi hakan, meyasa sai bayan yadawo gareta zata wulakantashi, tana kuka bakinta ke furta " ina sonka faisal, wlh ina sonka..." Da karfi takara bude kofar motar tafito da gudu ( kusa mata slow a gurin gudun nan nata😜) Takarasa gurinsa,bayansa ya juya yana hawaye bai masan da zuwan taba, jiyayi kawai tatabashi ta baya, Yanajuyo sukayi edo hudu, murmushi yasakar mata, itama cikin kuka tayi karfin hali yin murmushi tare da mika masa hankicif, yakarba ya share hawayensa, sannan shima ya mika mata hankacif din yasauke murya yace "kema kishare hawayenki, domin ni banason ganin HAWAYEN MASOYA" Karbar hankacif din tayi tana murmushi tashare Hawaye, tasaukar dakai tace "kayi hakuri da abinda namaka, idanma zaka ramane toka rama" murmushi yayi sannan yace "aiko a mafarki bana fatan Allah yanunamin namareki, kefa wani sashece ta jikina" Dariya tayi tace "nagode" Hannusa yasa cikin aljihu sannan yace "muje muci abinci koh" Ba musu tace "toh shikenan" tana Murmushi Tana gaba yana bayanta har suka karasa bakin kujerun suka zazzauna, cike da farin ciki suke fira har suka gama cin abinci, Kafin surabu saida zarah tabawa faisal adress dinta, shikuma yayi mata alkawarin cewa yana komawa gida, insha Allah zai sanar da mahaifinsa domin suzo akan maganar aurensu, Hakai suka rabu cike da kewar juna, sannan kowa ya wuce gida, Bayan faisal ya isa gida, yana karasawa cikin falon yatarar da momy da daddy zaune suna kallo, yayi sallama yashigo cike da farin ciki, yakarasa bakin kujera yazauna, momy ta dubesa, taga sai washe baki yake, tace "son yau wannan washe bakin haka, ayya kuwa lafiya" noke kai yayi yana murmushi yace "amm lafiy lau momy, abinda kuke jirane nasamo muku" Daddy yayi saurin cewa " menene?" Faisal yayi murmushi yace " suruka nasamo muku sunanta zarah gama address dinta" ya mikawa daddy card dinda data bashi, Farinciki sosai sukaji, momy tace " lallai wannan itace zarah, domin ta zare mana zuciyar yaronmu" duka falon suka kwashi dariya, daddy harda su dafe ciki saboda farin ciki, babu abinda yafiso a duniya irin yaga faisal cikin farin ciki, da kyar yasamu ya tsayar da dariyarsa yace "insha Allah gobe zanje nasamu iyayenta" Faisal yayi farin ciki da maganar daddy, nan dai suka yi 'yar fira zuwa ana fara kiran magriba, sannan suka tashi shida daddy sukayi alwala sukayi masallaci.... □□□□ □□□□ □□□□ Zarah ma haka tana komawa gida tasanar da ummanta cewa gobe za'ayi baki, Umma tayi murna sosai, abbanta nadawo aka sanar dashi shima yayi murna sosai, Da dare Tana zaune a dakinta tana waya da faisal firar soyayya suke, feena tashigo tazo tazauna kusa da ita, zarah ta sarkafata sannan taci gaba da wayarta, Feena tabita da kallo taganta sai washe baki take, takasa hakura saida tace "anty zarah meya sakaki farin ciki" zarah tadan kauda wayar daga kunnenta tace "faisal ne" Feena ta zare edo "faisal kuma anty zarah, halam yadaina sakaki kuka ne" Zarah tayi murmushi takara kauda wayar daga kunnenta tace "eh barima nabakishi kugaisa" tana gama maganar ta mayar da wayar a kunneta sannan tace "ga wata kanwata mai masifar surutu, sunanta feena, zaku gaisa" Faisal yace "toh shikenan" cike da farin ciki, Ta mikawa feena wayar, feena ta karbi wayar suka gaisa cikeda girmamawa, daga karshe dai take tambayarsa meyasa yake saka antynta kuka a kwanan baya, Zarah tayi saurin karbe wayar tana dariya tace " manta da ita kawai" Haka dai sukci ga da wayarsu cike da farin ciki, kusan kare daren sukayi suna waya, sai kusan 3 snnan suka katse wayar suka samu suka kwanta... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 127 and 128 Via *OHW* _A love story_💝 _Washe gari_ Daddy yaje yasami abban zarah suka daidaita komai, damacen ashe sunsan juna abokanan junane, nan dai suka tsayar da maganar auren nanda wata daya, haka dai suka rabu kowa yana cike da farin ciki, □□□□ □□□□ □□□□ _Bayan wata daya_ *KOGI* Yaune su Rumaisa zasu dawo daga honeymoon dinsu, tunda safe mai martaba ya turo motoci airport, Suna sauka aka daukosu suka dawo gidan, Rumaisa takara kyau da haske tayi bul2, Suna shigowa falon suka tarar da umma da mai martaba, rumaisa ta rungume umma, suna hada jiki da umma, kamshin turaren umma yadaki hancinta, nan take zuciyarta tatashi, yankuri tayi zatayi amai, dasauri tabar falon tafada toilet, ai kuwa NAN tafara kwararo amai, Hankali

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37