Chapter 33
Chapter 33
yanzu nake batun zuwa kiranki saikuma gashi kinzu" Umma tayi murnushi tace "gani nayi baki fitoba shine nace bari ninazo, kin fitone?" Rumaisa tace "eh nafito" "Tohm jmuje" Bakin mirrio suka fara zuwa umma ta taimaka mata tayi kwalliya mai kyau, Sannan umma taje tadauko mata wasu sabanbin kaya daga cikin kayan aurenta da kabir, rumaisa ta karba tasaka bakaramin kyau tayiba, sai faman murmushi take, Sai da umma ta tabbatar data shirya rumaisa tsaf sannan tabar dakin, tabarta a tsaye tana tubanin wai suwaye zasuzo haka, dahar za'ace sai umma ta shiryata, saikace wata small girl... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 119 and 120 Via *OHW* _A love story_💝 Da yamma ana batun suka sauka garin abuja, Basu dire ko inaba sai kofar gidan su rumaisa, mai gadi ya wangale musu kofa, suka fara jiro motocinsu a cikin gidan, Abba yafito cike da fa'a yatar besu, yakarasa dasu dakin baki, Rumaisa tana zaune a cikin dakinta sai kukan motaci takeji suna direwa a harabar gidansu, taso tatashi ta leka ta Window domin tagani amma sai kuma kawai tafasa, Tana zaune umma tashigo fuskarta dauke da fara'a, ganin umma tashigo yasa ta mike tana fadan "umma sunzo koh" Umma tayi saurin cewa "eh sunzo, kaje dakin baki, sunacen saiku gaisa" Tohm " kawai tacewa umma kanta soke akasa tafita tabar umma tsaye acikin dakin, tanufi dakin baki, Cike da faduwa gaba tatura kofar dakin baki, wani irin kamshi ya doki hancinta, dasauri ta sauke nunfashi, sannan ta taka kafarta a cikin dakin, tare dayin sallama, Yana zaune kan kujera yayi wani irin zama kasaita, yajuyo sallamarta, a hankali ya dube inda take tare da karba sallamar, a lokacin hartashigo dakin kanta a kasa tayi tsaye guri daya, takasa zuwa ko ina, Yabita da kallo zuciyarsa sai duka takeyi da karfi, a hankali take jiyo sautin Muryar sa yana fadan "shigo mana" tunda tajiyo sautin muryar takejin gabanta na faduwa, Taso ta dago kanta domin ta gazgata sautin da kunnuwanta kejiyo mata, amma kuma saita tsinci kanta da kasa yin hakan, Bata dago kantaba a haka take tafiya kanta a kasa harta karasa bakin kujera tazauna, Yanayin yadda tazauna yabashi dariya, yayi d'an murmushi kadan yana kallonta yace "amm fuskar taki tsadane da ita dahar bakyason d'agota mutane sugani" Gaban rumaisa yakara faduwa itadai jitakeyi kamar tasan mai muryar, kuma akace mata baki sunzo, ita da taji saukar ambaliyan motoci a harabar gidansu, ai yakamata taga mutane a dakin akalla sukai su goma amma saita rika jin muryar mutum daya, kodai sauran bazasuyi magana bane saita dago kanta, duk a zuci take wannan zancen, A hankali take dago kanta sukayi edo hudu da majnoon dinta, saida taja da baya saboda razana, ayya kuwa edanuwanta gaskiya suke nuna mata cewa Majnoon ne a kusa da ita, Suka kafe juna da edo suna kallon juna cike da jindadi da nishadi, Sun jima a haka kafin bakinta yasoma rawa tanason ta furta wani abu, Mubarak yadaga mata hannu "basai kinyi maganaba ninidai mubarak, ba mafarki kikeba, domin nasan zuciyarki zata saka miki hakan" Murmushi rumaisa tayi jitakeyi kamar ta burma ihu, dariyar haure daya tayi tana kallonsa tace "mekazoyi gidanmu" Nunfashi Mubarak yasauke yana kallonta yace "ummm nazone natafi da matata" Rumaisa tadan zare edo cike da mamaki tace "wacece kuma matar taka, kuka ina take" Sai da yayi murmushi Sannan yace "a yanzu haka ina tare da matata, wacca tadawomin da rayuwata daidai kamar a baya, natashi daga Majnoon nakoma Mubarak" Dariya maganar tabata, tare da mamakin ta ina yasan dacewa shi Majnoon ne, Takara kafe edonta akan nashi tana murmushi tace "wacece?" Shima yayi murmushi yace " RUMAISAN MUBARAK" Gabanta yasake yafaduwa tana cike da mamakin yaushe aka daura mata aure da Mubarak, bayan tasan dacewa ana daf da fara daurin musu aura komai ya yatarwatse, Dakatar mata da tunaninta yayi daceewa "karkiyi mamaki, domin nasan dacewa yanzu haka shikikeyi akan ya akayi aka dauramun aure dashi, nima a bazata abun yazomin, bayan nakoma gida abinda yafaru shine mummunan labari yasamnin akan cewa kanine ya kashemun iyali matata da yarona KISAN GILLA, wannan shine dalili dayasa mai martaba yasa aka daura aurena dake batare da saninaba, acewarsa ta wannan hanyarce kadai zamu saka miki akan taimakon dakikayi akaina, lokacin da mai martaba yasanar dani cewa andaura min aure dake, banjidadiba, amma kafin nazo nan sainaji kamar kece silar dawowa da farin cikina, kuma danazo sainaji kwata-kwata bana kunyarki, jinakeyi a jikina kamar munyi shekara goma atare, lallai wannan ba komai bane illa alakar zukata biyu, ma'ana zuciyata da taki, rumaisa yanzu nadawo gareki.." Hawaye suka sauko kan kumatunta wanda itama batasan dalilin zuwan suba, shin na tausayin labarin Mubarak ne kona farin ciki ne, hawayenta tashare sannan tace "Allah yajikansu da rahama" Murmishi Mubarak yayi sannan yace "ameen,yana murmushi yace "yanzu saurake ki haifomin wani yaron" Kunya rumaisa taji ta rufe fuskarta tana murmushi, tasowa yayi daga inda yazo kusa da ita, ya kura mata edo wani irin sonta nakara shiga zuciyarsa, yarasa dalili dayasa sonta yashiga zuciyarsa lokaci daya, kafin yazo abuja babu sonta ko kadan a cikin zuciyarsa amma yanzu sonta gabaki daya ya mamaye zuciyarsa, nan take ta meye masa gurbin margayiya matarsa, Cike da fargaba yariko hannunta, saida taji jikinta yadau wata irin sock, da karfi tasauke nunfashi tare da lumshe edo, A hankali yake murza hannu, yana murmushi cikin wata sanyanyiyar murya yace "I LOVE YOU RUMAISA" yakarasa maganar yana kallonta, Wani irin farin ciki takeji har cikin zuciyarta, da karfi ta kanne edonta, saboda wata irin kunyarsa dataji, da sauri ta mike ta janye hannunta daga nashi, tana murmushi ta kauda edonta daga kallonsa cikin b'arin murya tasoma furta "mee..t.." takasa karasa maganar saboda wata irin kunya takeji, da gudu tafita tabar dakin, Prince Mubarak yayi dariya yana kara jin sonta a cikin zuciyarsa, Tana fita ta zarce dakin umma, da gudu tashigo dakin, umma tana zaune akan sallaya taga sallar laa'sar, tafado jikinta cike da farinciki, umma tace "lalala rumaisa karyani zakiyi, wannan irin fadowar haka" Rumaisa tadago kai ta harari umma cikin wasa sannan tace "wato umma shine kukayimun AUREN BAZATA koh, yaushene akayi auren daba a sanar daniba" Umma tayi murmushi tace "karkiga laifina, laifin abban kine shiyace kar'a sanar dake, jiya bayan sallar isha aka daura muku aure a masallaci" Farin ciki kam a gurin rumaisa adaina magana, domin bazai iya misaltuwaba, yau dinnan jinta takeyi kamar ba itaba, Umma tadago daga jikinta tace "kitashi kije kishirya masa ruwan wanka, idan yafito kikaisa dinner yaci abinci koh" Rumaisa ta zare edo "umma nikuma, nifa kunyarsa nake, shibazai iya hadawa kansa ruwan bane" Umma tabe baki "au sai yanzu kika fara kunyasa bayan yazama mijinki, adacen ai bakya kunyarsa, nidan Allah tashi kije banason maganar banza" Rumaisa ta mike tana dariya tafice tabar dakin, Dakin baki takoma, tana shiga tasame zaune kan kujera ya tayar da kansa sama yana tunani, sallamar taace ta katse masa tunani, ya juyo yana kallonta, murmushi ya mata, kanta a sunkuye takaraso gurin, cike dajin kunya tace "zakayi wankane nashirya maka ruwan wanka" Murmushi yayi sannan yace "eh zanyi mana, amma tare dake zamuyi koh?" Dasauri tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37