Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

lafiya, bayan tasamu lafiya daga baya mayi mata bayani, wlh ni matar tausayi take bani" yakarasa maganar cike da makirci, Faisal yace "toh shikenan nima ina goyon bayanku dari bisa dari, kuma zan baku duk wani taimako, daya dace, Allah yakaima sati mai zuwa" Adnan yace "ameen, nidai na zanshiga wanka saina fito" Yana gama fada yanufi toilet, Faisal yayi yaja nunfashi sannan yajanyo filo yagyara kwanciyarsa, Zuciyarsa cike da tausayin umman Mubarak, Tun kwanan baya daya shiga sashen umma Mubarak yatayar mata da ciwo, tun daga ranar bai kara shiga sashen ba tsoronma zuwa gurin yake domin baya sonma taganshi.... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 101 and 102 Via *OHW* _A love story_💝 *Bayan kwana hudu* Ranar takama ranar juma'a bayan abban rumaisa yadawo daga masallaci, Yazauna falo yana fira shida Momy, suna cikin firarsu abba yace "ina rumaisa takene" Umma tace "tana cikin dakinta, ita da kabir, nashiga dazu nagansu suna karatu" Murmushi abba yayi sannan yace "bari inje insame, zamuyi magana dasu" yana maganar yana kokarin tashi harya mike, sannan ya wuce dakin rumaisa, Suna zaune rumaisa ce ke ja masa karatun shikuwa yana zaune kusa da ita yayi jugum, Yafada duniyar tunani, idan suna tare da rumaisa, sai yarikajin yanason kamar ya iya tuna wani, amma sai kuma yakasa, Abba yaturo kofar dakin yashigo, hakan yayi sanadiyar juyowarsu gabaki daya suna kallon kofar, Murmushi abba yamusu, suma sukai masa, yakaraso kusa dasu yayi tsaye a kansa yace "karatu kawai kukuyi" Rumaisa tace "wlh kuwa ai mumma kusa gamawa" Abba yayi murmushi yace "yawwa hakan yanada kyau" sai kuma yadanyi shiru kafin yace "amm daman maganar auren kune gobene, kuma ni banason yawan taron jama'ar nan, nasa angayyatomin malamai sannan kuma abban faisal shizai wakilci kabir a gurin daurin auren, sannan kuma cikin harabar gidan nan nakeson adaura auren, dan haka idan kinadawa wasu kawaye dazaki gayyato saiki sanar dasu, amma fa bada yawaba" Farin ciki gabaki daya ya lullube rumaisa, tana murmushi race "ni abba banida wasu kawaye da yawa, yan skull dinmune kadai, kuma bazasu wuce mutum biyarba, sannan kuma suduka nasanar dasu" Abba yace "yawwa hakan ma yayi" Kabir ya dube abba yace "abba ni ina nawa abokanai" Murmushi abba yayi sannan yace "gamu! ! ai mune abokananka, kuma danginka, kakwantar da hankalinka, kaji?" Abba yakarasa maganar yana kallonsa yana dariya, Kabir ya girgiza kai, Sannan abba yafita yabar dakin, yabarsu sukaci gaba da karatunsu, Rumaisa sai farin ciki takeji a cikin xuciyarta, Burinta ya kusa cika, Majnoon zai zamo mijinta... *Washe gari* ranar aure, Tunsa sassafe abba ya yasa aka share harabar gidan tasss, sannan yadauko wayarsa yakira daddy faisal yasanar dashi cewa kafin 10:00 yakirawo malaman gabaki daya su hallara a harabar gidansa, zuwa karfe 11:00 a daura aure, "Toh" kawai daddy yace sannan suka kashe wayar, Suna kashe wayar daddy yakira faisal, Yana kwance a cikin blanket yana bacci mai dadi, yaji wayarsa tadau kara, a hankali ya zuro hannunas yadauki wayar yakara a kunnesa, batare daya duba wayake kiraba, Hello son" shine sautin daya daki kunnensa, sai lokacin yasan da cewa daddy ne kekira, cikin muryar bacci yace "daddy antashi lafiya" Daddy yace "lafiya lau, amm daman tun jiya naso nakiraka nasanar dakai cewa yaune daurin auren rumaisa ita da wanna marar lafiyan" Wani irin mummunan faduwar gata ya ziyarci faisal, da karfi yace " what! !!, da sauri yaye blanket dinda ke jikinsa, daddy yace " lafiya kuwa meke faruwane " Cikin gaggawa faisal yace "daddy ina zuwa ..." da sauri ya tsinke wayar, yace "ohh shet" Juyawa yayi gefen adnan, dake bacci sai kwasar minshari yake yasamesa yana bacci, da karfi faisal yake bubuga kafarshi yana kirana sunansa, "kai tashi akwai matsala" A hankali yake bude edonsa ya dube faisal yace " lafiya kuwa ?" Faisal yace " ina kuwa lafiya, yanzun nan daddy ya kirani wai yaune za'a daura auren, mutumen abuja mai kama da yayanka Mubarak," Da karfi adnan yamike cike da tashin hankali yace "ehhh, nashiga ukku" cikin gaggawa faisal yace " yadace ace mun isa garin abuja kafin a daura auren nan, domin kasan idan aka daura auren nan baza a barmu muzo dashiba" Adnan yace "hakan za'ayi maza jeka dakinka kayi wanka nima yanzu zanshiga nayi wanka anan " dasauri adnan, yafada toilet, Shima Faisal yakoma dakinsa yashiga wnka, bawani wankan kirki adnan yayiba domin duk ya tsorata, yana fitowa cikin gaggawa yasaka kayansa, yana gamawa yanfi dakin ummansa, Yana shiga dakin yatarar da ita zaune akan sallaya, nan yashiga fada komai dake faruwa, bakaramar firgita tayiba, cike da tashin hankali tace " bazakuje a mota ba, jirgi zaku hau yanzu yasaukeku abuja, kushirya maza kuje airport kafin mai martaba yatashi daga bacci" Haka kuwa akayi bayan sun gama shirya duk yadda abin zai kasance, Atare suka fito shida umma, Koda suka fita suka tarar da faisal tsaye a bakin kofar dakin adnan, shima haryazo bai gansa cikin dakinba shine yatsyawa waje yana jiransa, Nan suka wuce zuwa harabar gidan, driver yadaukesu a moto ya lula dasu zuwa airport.... Aha muje zuwa....😃 https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 103 and 104 Via *OHW* _A love story_💝 Suna karasawa airport sukayi sa'a kuwa jirgir safe bai tashiba, nan suka shiga.... suka lula zuwa abuja.. □□□□ □□□□ □□□□ Rumaisa tana zaune a daki, tare dawasu kawayenta su biyu, leemart da kuma maryam, suna fira, amma ita sam zuciyarta bata gurin, tunani takeyi ashe daman burinta zai cika akan MAJNOON, yau za'a daura mata aure tare da kabir (Majnoon) tazamo mallakinsa shima yazamo nata, daman hausawa sunce komai yayi farko zaiyi karshe Maryam ta dafata, ta baya, saida ta zabura "waike tunanin me kike ne, tun dazu muke miki magana amma kinyi shiru" Rumaisa ta sosa kanta, cike da jin kunya tace "amm bakomai, me kikace ?" Maryam tace " cewa mukayi kitashi kije kiyi wanka kingafa lokaci yana tafiya" Murmushi rumaisa tayi sannan tace "Tohm shikenan kujirani yanzu zanfito" tana gama fada tamike tafada toilet, □□□□ □□□□ □□□□ Abba kuwa tuni yayi wankansa cikin farara shadda, sai fara,a yake, anata shirye-shirye fara daura aure, umma ma tasha ado, ita da haj luba sunyi kyau abinsu, yau farin ciki ya yawaita a gidan abba, □□□□ □□□□ □□□□ Kabir kuwa tunda yatashi a safiyar yau yakejin gabansa nafaduwa, Duk yakasa sakin jikinsa, musan mamma dayaji labarin cewa yaune aurensa, Tun jiya abba yakai masa nasa kayan dazai saka, yayi wanka yafito yazo yayi tsaye a tsakiyar daki, shifa yanzu komai yadaure masa kai, a duk lokacin dayaji anyi maganar auren nan sai gabansa yafadi, yarasa dalilin yin hakan, Yayi tsaye a bakin mirror yana kallon kasan, bansan meya tunaba sai kuma naga yayi murmushi, sannan yafara shafa mai, bayana yagama, Sannan ya shirya shima cikin farar shadda tasha aiki, tana kalli, yasaka hula baka, takalmi bakake, abinka da farin mutum saifa yafito tas dashi, yayi kyau sosai... □□□□ □□□□ □□□□ 9:30 Motoci sai parking sukeyi a kofar gidan abba, yafito waje yana tabar baki cike da fara'a, duk da auren na boyene amma saida mutane suka taru sosai, domin abba mutumen mutanene, harabar gidan abba tacika

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37