Chapter 34
Chapter 34
"nikuma" tare da nuna kanta, Kai ya kida mata " eh mana kedin, keba matata bace" Cikin rawar murya Tace "to..to..to.." yana murmushi ya katseta dacewa "kwantar da hankali, kije kawai nizanyi wanka dakaina, kije ki huta saina fito" Kai kawai ta girgiza masa sannan tafice tabar dakin, Yana kallonta harta fita sannan yayi murmushi, ya mike yafada toilet, wanka yayi sosai sannan yafito, yasake saka wasu sabanbin kaya, sannan yafita, A falo sukasha fira sosai shida su umma da haj luba, har aka kira sallar magriba, sannan ya mike yaje yayi alwala yatafi masallaci, bai dawoba saida aka gama isha, Koda yashigo gidan, anjera masa abinci kala2 akan diner table, rumaisa ce tamasa jagora har suka karasa bakin diner, suka zaune , bayan sunzauna tayi serve dinsa, Yana cin abincin suna fira duk da ba wata mata sosai take masaba, tarasa dalilin dayasa yanzu yake mata kwarjini, Hakadai yaci abinci yayi nak, Sannan sukayi saida safe, yatashi ya wuce sashen baki, ita kuwa ta wuce dakin umma.. Tana shiga tazauna gefen gadon da umma take kwance, ta sauke nunfashi tana kallon umma, Umma tace "a ina kikabar mijinnaki" Rumaisa tayi murmushi tace "umm yatafi dakinsa wai bacci yakeji" Umma ta harareta cikin wasa "to shine bazaki tayashi bacci ba, kefa nalura dake Allah yanzu kinaso kizamo wata huhulahu, idan kikayi wasa da mijiki wata zata kwace mikishi kina zaune kinyi sakaci, shifa namiji kulawa yakeso da tarairaiya tamkar kwai, kikula da mijinki fiye da yadda zaki kula da kanki, kibashi farin ciki fiye da yadda zaki bawa kanki, ki rike abinki hannu bibbiyu, karkiyi wasa dashi" Jikin rumaisa yayi sanyi, tare dajin wani irin kishi, akan umma tace wata zata iya kwace mata shi, murya a sanyaye tace "yanzu umma yazanyi" Murmushi umma tayi sannan ta dafata tace "kije kitayashi bacci, karkisa komai a ranki, kinji Rumaisa" Girgiza kai tayi jiki a sanyaye "toh umma" sannan ta mike tafita, Kafin taje dakin saida ta wuce dakinta ta sanya katon hijab, sannan takarasa dakinsa, Yana kwance akan gado yana wasa da wayarsa, taturo kofar dakin tashigo, suna hada edo yasaka mata murmushi, dukar da kanta tayi harta karaso kusa da gadon tazauna a bakin gadon, Uffan baice da itaba, yaci gaba da dannar wayarsa, shima miskilin karshene, Ta jima a zaune batayimai maganaba shima baimataba, Dadai taga bayada imanin yimata magana, sannan ta sauke nunfashi cike da kunya tace "zowa nayi natayaka bacci" Murmushi yayi sannan yace "uhim ga gurinan ki kwanta nibanajin bacci yanzu" Bata kara furta uffanba, ta juya tagefe daya ta kwanta, batare data cire hijab dintaba, a hakan ta kudunne cen karshen gado ta juya masa baya, Yanayin kwanciyarta yabashi dariya, yayi murmushi tare da girgiza kai, Yajima yana game din kafin ya ajiye wayarsa sannan yatashi yacire rigarsa, yakoma dagashi sai singlet da dogon wando rigar daya cire, Sannan yadawo kan gadon yakwanta, tanajin kwanciwarsa ta kanne edonta, duk jikinta yayi sanyi, Bayan ya kwanta yakurawa bayanta edo, sannan ya ja jikinsa yakarasa kusa da ita, hannunsa yasa ya sarkafota ta baya, Yajuyo da fuskarta daidai gurinsa, yasa hannu yana shafa fuskar, Nan take jikinta yadau kyarma, ya lura da irin yadda jikinta yake rawa, hakan ya tabbatar masa dacewa batayi bacci ba, murmushi yasaka sannan yasauke muryarsa yace "kunyata kikeji ne, dabazaki bude edonba" Ta girgiza masa kai, Yayi murmushi yace "toh shikenan, kisha kwanciyarki lafiya saida safe" yana gama fada ya manna mata kiss a goshi, sannan ya juya ya janyo blanket ya rufe jikinsa, Tajima a yadda yabarta, bata motsaba domin takasa yin komai duk jikinta yayi sanyi, Saida ta dainajin motsinsa sannan ta bude edonta, koda tajuya taganshi har yayi bacci, A sannu tatashi ta kura masa edo tana kallonsa, sai kara shige masa rai yake, taja jikinta takarasa kusa dashi, jikinta narawa ta kwanta akan kirjinsa, saida tayi wani sauke nunfashi, Ashe shima ba bacci yakeba, a hankali yake sauke hannayensa akan bayanta, yakara manneta kam a jikinsa, A hakadai har sukayi bacci, ko wannensu zuciyarsa cike da kaunar juna.... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 121 and 122 Via *OHW* _A love story_💝 _Washe gari_ Tu da sassafe aka shiga hada musu kayansu, komai anshirya musu na zuwa kogi, Karyawa kawai sukayi, sannan suka shiga motaci, rumaisa da Mubarak, a mota daya, abban rumaisa da umma a mota daya, haj luba kuwa motarta ita kadai, sai sauran bodyguard din suka shiga sauran motocin Haka dai suka kwashe gidan gabaki daya suka wuce kogi, Daga baya daddy yakira abba yasanar dashi cewa shima zaizo amma sai zuwa gobe a motarsa zaizo, yau dinma yanada aiki daya tsayar dashine, abba yamasa fatan Allah yakawosa lafiya, ■■■■ ■■■■ ■■■■ *KOGI* Kusan azahar suka karasa kogi, sunga karamci iya karamci, Umma Mubarak kuwa tunda akazo take neman surukarta, tana ganinta kuwa ta rungumeta cike da farin ciki, Faisal yana dakinsa cikin bakin ciki, tun jiya dadare yaci kukansa mai isarsa, tare da bawa zuciayrsa hakuri, domin a yanzu yasan dacewa rumaisa tasha gabansa, saboda a yanzu ita matar wanice, kumako wani D'in yarima dan sarki, ya karbi gaddara kuma yayarda dacewa daman dai tunchan Allah yayi rumaisa ba matar sa bace, zaiyi kokarin cire sonta a zuciyarsa, Hakadai yazaune cikin daki sai saka-sake yake, daya gaji da zaman yatashi yashiga toilet, bayan yayi wanka yafito, Yayi kokarin boye damuwarsa sannan yafito yatayasu farin ciki, Umma da abba aka kaisu masaukinsu, Haka kuma haj luba itama aka kaita nata masauki, Umman Mubarak kuwa cewa tayi itakam bata tashi kai 'yarta daki mijintaba, sai bayan angama shagalin baki, sannan za'a kai rumaisa dakinta, Haka kuwa akayi, saida aka kara gyara sashen Mubarak aka cire masa duk wani abu dazai sashi yatuna da margayiya matar aka saka sama sabo, Da dadare suka taru a falo sukasha firarasu harda mai martaba, ko wannensu cike da farinciki, anan suka tsara yadda bikin zai kasance, kwana ukku za'ayi anashan biki kafin akai amarya dakinta, Mai martaba yasa angayyato manya2 mawaka, harda 'yan fim, and, ( nima saida nayi tawa gayyatar, na gayyato, rankatakaf OHW, da kuma my members yan hausa book) kowa yazo, Gida yacika da mutane, hatta yan aikin dake gidan suna farin cikin da wannan auren, *Day 1* Aka shirya wani katon hell awani babban hotel dake cikin garin kogi, acen akaje akasha biki, manyan mutane, da manyan sarakuna duk sun hallara, an watsa naira iya naira, Amarya da ango sunyi kyau abinsu, daka gansu zaka tabbatar da cewa suna cikin farin ciki, Tuni su daddy suka karaso shida momy, komai a gaban edonsa akayi, faisal yayi farin ciki sosai da zuwansu, ansha biki iya biki, har zuwa yamma sannan kowa ya watse, *Day2* Wani gurin hutawa babba, aka kama, amma wannan ba wata gayyata akayiba, wannan bakin family, shimadai anci kuma ansha, an baje an chase, *Day3* A rana ta uku kam malamai aka kira aka gabatar da walima, mai martaba ya gayyaci manyan malamai, dakuma alaranmominsu, ansha wa'azi sosai, abinsa sai wanda yagani, A daren ranar umman Mubarak tasa aka tsarawa rumaisa wata irin kwalliya tagani da fada, ga hannayenta sunsha lalle, dawasu irin turararuka masu kamshi, Aka shirya rumaisa cikin wani sari (Indian dress)
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37