Chapter 18
Chapter 18
"naam abba" "Kirage yawan tunaninnan domin baya haifar da alkhairi kinji" rumaisa ta noke kai tace "toh abba zandaina" Abba yayi ajiyar zuciya yasake dubanta yace "daman abinda yakawoni shine, maganace akan faisal munyi magana nida iyayen sa yau zaizo gurinki, domin kufara fuskantar juna kafin ranar aurenku, dan Allah Rumaisa kibashi kulawa, karki sharesa, idan kikayimun haka zanyi matukar farin ciki" Hawaye suka cicciko a edon Rumaisa murya a sanyaye tace "shikenan Abba insha Allah zanyi kokarin yin haka" Abba yajidadi sosai yace "Allah yayi miki albarka" rumaisa tace "ameen" muryarta na rawa kamar zatayi kuka, Abba ya mike tsaye "kifito kici abinci, kafin yazo" yana gama fada yabar dakin rumaisa ta gagara yin magana domin a lokacin har kukan yasoma zomata, Ai kuwa abba na fita ta fashe da kuka, kuka mai sauti take amma a hanakali sautin kefita dan kar wani yaji, Kuka sosai tayi saida taji zuciyarta tafara zafi sannan tadaina, tashare hawayenta, tatashi tashiga toilet, wnka tayi sannna tafito, Bawani mekupp tayiba, porder ce kawai tashafa, sannan ta janyo wata doguwar gown tasaka tayi kyau abinta, amma dai fuskar a daure, Tazo gaban mirror tayi tsaye tana kallon kanta, sai lokacin ta lura da irin ramar datayi, har kansanta na wuya sunfito.... Allah sarki rumaisa😭 ***** ******* ****** Tunda yafito daga wanka yake cikin farin ciki, dasauri sauri yashafa mai, sannan yakarasa bakin akwatinsa ya janyo wani light blue yadi, yasaka yayi kyau abinsa, yazo bakin mirror yayi tsaye yana kallon kansa, yayi murmushi a lokacin yana kokarin daidaita hula akansa, bayan yazaunar da hular daidai, yakarayin murmushi, sannan ya janyo turare yafeshe jikinsa kaf nan take ya kwashi kamshi, Sannan yakarasa wurin ajiye takalminsa, yajanyo wasu takalmi masu ratsin blue a cikinsu, yasaka, sannan yafita falo, Momy naganinsa ta washe baki tana fadan " a a lallai wannan shirin saidai zuwa gurin rumaisa" Faisal yayi murmushi sannan yakaraso gurinta, har zai zauna sai kuma yafasa, momy tace "zauna mana" faisal yayi murmushi yace "a a momy bazan zaunaba domin banason nayi leti zuwa, kidai jirani idan nadawo zaki sha labari" yana karasa maganar ya nufi kofar fita, cikin zumuri da jindadi momy tace a dawo lafiya" nan dai yafita yaje yashiga motarsa, yayiwa mai gadi hoh yabude masa kofar, yana fita daga gidan yasaka wakar Soyayyace tafito dani, ta ko ina ansan dani kizo muje muza gaya, Alkawarin so murike,) wakar umar m sharif, cike da nishadi sautin wakar ke fita ta speakers na motar, wakar tana ratsashi sosai domin harya haddace wakar wani baiti naji yana rairowa kamar haka "tarkon so yakama zuciya, gidan sarauta da sarauniya, natabbata banishan wuya dan adalcinta da gaskiya na tabbata nafad'a a hannnu nagari bata cutar dani, dan lele nazamo a guntane, bazatasoni insa wuya" haka dai yaci gaba da suburbuda wakarsa yana tafiya, Misalin karfe 7:30 na yamma abba yadawo daga masallaci yana zaune a falo, umma kuwa tana kicin tana hada musu girki, hajja luba tana dakin rumaisa saman sallaya tana lazumi, Yaro yashigo gidan, yayi sallama abba ya amsa, yaron yace "wai ana sallama da rumaisa a waje" cike da farin ciki abba yace "kace tana zuwa " Yaron yace "toh" yafita Yana fita abba yatashi dasauri yaje yasanar da rumaisa, Bata tsaya bata lokaciba gurin yin mekup, tadan kimtsa jikinta sannan tafito hajja luba tayi mata magana akan tadan saki fuska mana, hakan yasa tadan waye fuskarta kadan sannna tafita, A jikin motarsa ta samesa a tsaye, tun daga nesa yake kallonta yana mata murmushi, rumaisa takaraso gurinsa ta gaidashi ya amsa cike da farin ciki, suna gama gaisuwar tayi shiru, shima yayi shiru ganan fuskarta a murtuke yasa yayi murmushi yace "rumaisa kibani dama nanumiki irin sonda nake miki, a koda yaushe muradina shine naga kin kasance tawa" Murmushi kadan rumaisa tayi kafin tace "ai banice zan baka damaba, zuciyatace, domin ni ai nagama baka dama tunda har nazo gurinka" murmushi faisal yayi yace "toh shikenan nikuwa zan nunawa zuciyarki cewa duk duniya babu wadda yake sonta kamar yadda nakesonta" Hmm kawai rumaisa tace masa, haka dai sukaci gaba da firarsu, duk yayi magana saita bashi amsa, amma dai ta gagara sakin fuskar, Shikam dai ko a haka suka tsaya yaji dadi sosai, koda ace duk yazo zaginsa take to shikam babu abinda zai damesa, Sun kusan awa daya suna magana, rumaisa dukta tsargu, wani irin zafi takejin zuciyarta nayi, nan take kanta yadau ciwo, jiri tasoma gani, Ta mike tsaye kamar zata fadi, tace "banajindadi jiri nake gani,kaje saida safe" bata jira yayi maganaba, tabar gurin dasauri, Faisal ya mike cike da farin ciki, yadan tabe baki, yace "any way! Gobema zan dawo" Abba yana zaune a falo umma ta kawo masa abinci yana shirin fara ci, Rumaisa ta shigo falon, ta dafe kanta da kuma zuciyarta, abba yace "lafiya kuwa " Kala bata ce masaba takarasa dakinta, da sauri yabiyo bayanta, tana shiga dakin jiri ya kwasheta ta sulala a kasa tana tari da karfi ta dafe gefen kirjinta daidai gurin zuciyarta, tana kuka, hajja luba dake zaune akan sallaya tayi saurin karasawa gurinta tana fadan rumaisa lfy kuwa, koda taduba taganta tana aman jini tsorata sosai hajja luba tayi dasauri ta kwalawa abba kira, a daidai lokacin ya turo kofar dakin yashigo... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:46 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 73 and 74 Via *OHW* _A love story_💝 yana shigowa dakin yaga halin da rumaisa take ciki dasauri yasa aka daukota suka nufi asibita, Sa isarsu asibitin Aka kaita emergency room, aka bata taimakon gaggawa, Umma, abba , hajja luba duk sun tsorota da ciwon rumaisa, ace yarinya harda aman jini, Bayan wasu yan mituna likita yafito daga cikin da rumaisa take ciki a hargitse, dasauri su hajja luba suka karasa gurinsa, tun basuyi maganaba likitan yace "tana bukatar karin jini da gaggawa domin jini yafita a jikinta sosai" Abba duk ya firgice da sauri yace "toh yanzu likita yaza ayi kennan" Cikin gaggawa likatan yace "kuzo muje a gwada jininku mugani ko za a samu wadda yadace danata" haka kuwa akayi suka bi bayan likitan akaje aka gwada jininsu, na umma ne yayi daidai danata, aka kuwa d'ibi roba daya akaje aka sakawa rumaisa *BAYAN MINTI 50* likitan yakara fitowa daga cikin da rumaisa take ciki a karo nabiyu, sun abba sukayi saurin karasawa gurinsa, Hajja luba hawaye take tana cewa "likita meya faru da itane" Likita ya dube abba sannan yaja nunfashi yace "'yarku tana daf dakamuwa da cutar hawan jini, domin tunani da damuwa sun mata yawa, meyake damunta?"yakarasa maganar da tambaya Abba ya dubi umma, umma ta dube hajja luba, sukansu basusan meye damuwarba, abbane yayi saurin cewa "muma bamu saniba likiti, saidai idan zata iya magana mezai hana a atambayeta" Likita yace "ba yanzu, domin yanxu munsamu munyi mata karin jini kuma yanzu haka bacci take bazata samu farkawaba sai nan dazuwa awa daya" Abba yace " to shikenan zamu jirata, yadanyi shiru har likitan zaibar gurin sai kuma yayi saurin cewa "likita yanzu ya jikin nata" Likitan yajuyo yayi ajiyar zuciya sannan yace "tasamu sauki, sosai" yana gama fada yabar gurin, abba yadube umma duk jikinta ya mutu yace "mungode
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37